Kano: Wasu na Raɗe Raɗin Haɗin Kai da Kwankwaso da Takarar Ganduje a NDC

Kano: Wasu na Raɗe Raɗin Haɗin Kai da Kwankwaso da Takarar Ganduje a NDC

  • Wasu jita-jita marasa tushe zuwa yanzu suna nuna akwai yiwuwar Abdullahi Umar Ganduje ya fice daga APC
  • Abin da ya fi ban mamakin shi ne rade-radin cewa tsohon gwamnan zai hadu da Rabiu Musa Kwankwaso a NDC
  • Idan wannan ta tabata, wani tsohon kwamishina a jihar Kano ya hango karshen siyasar Dr. Abdullahi Ganduje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Wasu sun fara rade-radin cewa ana daf da ganin wani sauyi da watakila ba a taba gani ba tunda ake siyasar Kano a shekarun nan.

Akwai rahotanni marasa tabbas da ke cewa Abdullahi Umar Ganduje da tsohon mai gidansa, Rabiu Musa Kwankwaso za su koma gida daya.

Ganduje da Kwankwaso
Abdullahi Umar Ganduje lokacin kamfen 2023 da Rabiu Musa Kwankwaso da ya kai wata ziyara kwanan nan Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR/Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Rade-radin haduwar Kwankwaso da Ganduje

Muaz Magaji wanda babban ‘dan siyasa ne a Kano, yana cikin wadanda suke kara yada wannan jita-jita musamman a kafar nan ta Facebook.

Kara karanta wannan

Jami’an ‘yan sanda sun damke kakakin PDP bisa zargin taba sanata a Facebook

Tsohon kwamishinan ya yi nuni da cewa Abdullahi Umar Ganduje zai koma jam’iyyar NDC.

Injiniya Muaz Magaji yake cewa wai ana so a tsaida Abdullahi Ganduje a matsayin ‘dan takaran Sanatan Kano ta Arewa a karkashin NDC.

Magaji wanda aka fi sani da Dan Sarauniya ya fito ne daga yanki daya da tsohon gwamnan kuma wanda ya nada shi kwamishinan ayyuka.

Dansarauniya ya hango karshen siyasar Ganduje

‘Dan siyasar ya yi ikirarin karshen Ganduje ne ya zo a siyasa, yana nuna cewa barin APC mai mulki tana nufin za a birne tasirinsa kaf a jihar Kano.

A ranar Laraba ya rubuta kamar yadda ita ma tashar rediyon Freedom Radio ta rahoto shi:

"Na ji kishin-kishin Allah zai haɗa mana Ganduje da Kwankwaso a gida daya! Wai Ganduje zai yi takarar Sanata a Kano ta Arewa a NDC.
Nace Alhamdulillah lokaci ya yi kenan, ritaya ta zo a siyasar Kano"

- Engr. Mu'azu Magaji.

A shafin nasa, tsohon kwamishinan ya dage cewa an zo babin karshe na siyasar Ganduje muddin ya rabu da APC, jam’iyyar da ya rike shugabanta na kasa.

Kara karanta wannan

Magana ta canza da aka nemi sunayen wasu ‘yan takaran jam'iyyar APC aka rasa

‘Bai da wata daraja’; ‘Dan Sarauniya ya jefa magana

Da aka fito da hoton wata fostar Ganduje da tambarin NDC, injiniyan ya caccaki lamarin, yake nuna cewa babu wata daraja wajen tsohon gwamnan.

Ya ce:

“Wannan mutanen fa sun raina mana hankali”

Dansarauniya sun gargaji Kwankwaso kan Ganduje

An kuma ga Magaji ya dauko da wata magana da Kwankwaso ya yi a kan Ganduje, yake cewa sun gargadi tsohon sanatan a kan ba magajinsa takara.

Wata tashar rediyo ta rahoto Kwankwaso yana cewa Ganduje har abinci yake kawo masa saboda kawai ya saki jiki ya ba shi takara, a karshe sai ya bijire.

Dr. Ganduje bai dade da shiga ofis a 2015 ba, sabani ya bayyana tsakaninsa da Madugun Kwankwasiyya kuma tun lokacin aka ja daga har yau.

Da gaske Ganduje zai koma jam'iyyar NDC?

Zuwa yanzu Ganduje ko wani na kusa da shi bai ce komai game da jita-jitar ba, amma an ga ‘Yan Kwankwasiyya suna ta maganganu a kan shi.

Kara karanta wannan

NDC: An samu bayanin abin da aka tattauna a sabuwar haduwar Kwankwaso da Dickson

Bashir Sanata Zwk da yake tare da Kwankwasiyya ya daura har da wani bidiyo na Khadimul Islam a shafin Facebook, ya yi masa take da ‘ashe za mu hade.’

A shafi nasa a dandalin sada zumuntan, ya yi ta rubutu sunan Ganduje yana kwarara yabo, a gefe guda kuma ya yi ikirarin Nasiru Gawuna ya rabu da su.

Duk da wannan abu da 'Yan Kwankwasiyya ke yi, babu wata majiya mai karfi da ta gaskata jita-jitar.

Sanusi II: Abdullahi Ganduje ya jawo magana

Ana da labarin lokacin da wani mai fashin baki kan harkokin jama'a, Ibrahim Ado Kurawa ya soki Abdullahi Ganduje kan wasu maganganun da ya yi.

Kalamansa masu cin karo da juna game da masarautar Kano ta jawo masanin tarihin ya dura kan tsohon gwamnan na Kano kuma babban 'dan siyasa.

Abin da ya faru kuwa shi ne Ganduje ya kira Muhammadu Sanusi II da Sarkin Kano, sai kuma ya dawo yana nuna shi bai yi masa mubaya'a ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng