Rikadawa ya fadi dalilin taba matar aure a shirin Nollywood, yace ba yadda ake tunani ba ne

Rikadawa ya fadi dalilin taba matar aure a shirin Nollywood, yace ba yadda ake tunani ba ne

  • Rabiu Rikadawa ya yi karin haske a kan hotunan da aka gani na wata ‘yar wasa tana taba jikinsa
  • ‘Dan wasan kwaikwayon ya bayyana cewa Sameera Fasheena ta taba shi ne ba tare da son ransa ba
  • Rikadawa yake cewa hakan ya faru ne saboda ‘yar wasar ta fito a matsayin amaryarsa a shirin fim

Kano - Babban ‘dan wasan kwaikwayon Hausa, Rabiu Rikadawa ya maida martani ga masu sukarsa a kan taba jikin wata wanda ba muharramarsa ba.

Ganin yadda Sameera Fasheena ta rika taba Rabiu Rikadawa a wasan ‘Mustapha’ da suke yi, mutane suka fito suna yin tir da danyen aikin magidancin.

Gensunus ta wallafa hirar da aka yi da Malam Rabiu Rikadawa a shafin Youtube, inda ya kare kansa, yace ba da son ransa ya kusanci wannan tauraruwa ba.

Read also

Innalillahi: An tsinta gawar limamin Abuja kusa da gona

Rikadawa yake cewa abin ya faru ne a shirin Mustapha mai dogon zango wanda za a haska a tashar Rock, inda Sameera Fasheena ta fito a matsayin amaryarsa.

Tauraron yace ya nemi ‘yar wasan mai aure da ‘ya ‘ya hudu ta daina taba shi, amma hakan ya faskara har sai da mai bada umarnin sirin ya shiga tsakaninsu.

Rikadawa
Rabiu Rikadawa Hoto: www.dateline.ng
Source: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rikadawa ya yi raddi ga masu surutu

“Ita wannan mata ta fito ne a matsayin matata. Ina da mata biyu a shirin, da Sameera Fasheena da kuma 'yar wasa Franca Blanc. - Rabiu Rikadawa.
“Wannan mata sunanta Smaeera Fasheena, kuma ita ta fara gabatar da kanta a lokacin da na sauka a Abuja da za ayi shirin. Ta ce mani ita ce wance-wance.”
“Motsi kadan ta jawo ni, ta taba ni, idan ta matso in matsa. Ina nuna mata ba sai ta taba ni ba. Sai ta ke tunanin ko kyamar ta nake yi ne, na nuna mata ba haka ba.”

Read also

Ronaldinho da shahararrun ‘Yan wasan kwallon kafa 6 da suka tsiyace bayan sun yi ritaya

A game da kokarin rungumarsa da Fasheena ta yi, yace da aka zo za ayi wani shiri ne sai ta zaburo ta na neman rungumarsa, amma ya yi ta rike hannuwansa.

Duk da haka, Rikadawa yace sai da matar ta damko shi duk da ya na cewa 'a'a'. Tauraron yace ya fito da hotunan ne domin nuna abin da yake faruwa a bayan-fage.

Sadiq Daba ya cika

A shekarar nan ne aka ji cewa tsohon jarumin Nollywood kuma kwararren dan jaridar nan, Sadiq Daba ya rasu bayan ya yi tsawon lokaci yana fama da rashin lafiya.

Sadiq ya rasu ne bayan ya dade yana fama da cututtukan leukemia da kansa wanda aka fi sani da daji.

Source: Legit

Online view pixel