Soke Rajistar NDC: Uba Sani Ya Aika Sako ga Obi, Kwankwaso da Sauran 'Yan Siyasa
- Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya aika da sako ga 'yan siyasar da ke kushe bangaren shari'a na Najeriya
- Uba Sani ya tunatar da cewa bai kamata ana siyasantar da hukunce-hukuncen da kotuna ke yankewa ba saboda kawai ba a samu yadda ake so ba
- Gwamnan ya tunatar da dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi, yadda ya baya ya taba cin gajiyar hukuncin kotu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bukaci ‘yan siyasa da su guji sanya siyasa a cikin hukuncin da kotuna ke yankewa.
Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, na daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar hukuncin kotu a baya.

Source: Facebook
Gwamna Uba Sani ya bayyana yayin da yake jawabi a wata tattaunawa ta musamman da tashar Arise News a ranar Talata, 30 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan
DSS da yan sanda sun yi bincike, an ji gaskiya kan ɓullar sabuwar ƙungiyar ta'addanci a Najeriya
Wane sako Uba Sani ya ba 'yan siyasa?
Uba Sani ya mayar da martani kan fargabar da ke tattare da hukuncin babbar kotun tarayya da ya shafi rajistar jam'iyyar NDC, inda ya jaddada cewa amincewa da sashen shari'a yana da muhimmanci ga dorewar dimokuradiyyar Najeriya.
Gwamnan ya ce bai kamata ‘yan siyasa su rika yaba wa kotuna lokacin da hukunci ya yi musu dadi ba, sannan su rika kushe sashen shari’ar duk lokacin da aka yanke hukuncin da bai yi daidai da ra’ayoyinsu ba.
“Ga wasunmu da suka yi amanna da dimokuradiyya, tsarin doka, da sashen shari'a, mun yi amana cewa dole ne mu kasance masu taka-tsantsan. Mayar da kowane al'amari na shari'a ya zama na siyasa ba zai amfane mu ba."
- Gwamna Uba Sani
Uba Sani ya yi maganar Peter Obi
Yayin da yake tunawa da tarihin siyasar Obi, Uba Sani ya bayyana cewa tsohon gwamnan na jihar Anambra ya taba kwato wa'adin mulkinsa bayan ya garzaya kotu.
“Domin da yawa daga cikin wadannan 'yan siyasan, su ma sun kasance wadanda suka ci gajiyar wasu shari’o’i a kasar nan. Ko shi kansa jagoran NDC, ina nufin dan takarar shugaban kasa, Peter Obi, ka tuna shi ma wani ne da ya ci gajiyar wani gagarumin hukuncin shari’a mai karfi lokacin da yake gwamna."
“Lokacin da abin ya yi wa ‘yan siyasa dadi, sai su ji cewa sashen shari’a shi ne wuri mafi kyau da za a je. Lokacin da abin ya juyo kansu, sai su ji cewa sashen shari’a shi ne wuri mafi muni."
- Gwamna Uba Sani

Source: Facebook
Ya kare bangaren shari'a
Yayin da yake amincewa da cewa babu tsarin shari'a da yake cikakke 100 bisa 100, gwamnan ya jaddada cewa dole ne masu kishin dimokuradiyya su ci gaba da yin amanna da kotuna da sauran hukumomin dimokuradiyya.
“Dole ne ka fahimta, idan kai dan dimokuradiyya ne, ka yi amana da tsarin. Ka yi amanna da sashen shari'armu. Ba ni da wata shakka a zuciyata. Sashen shari’armu ba cikakke ba ne. Kuma babu inda yake cikakke a fadin duniya. Amma a kowane hali, shin za mu iya kasancewa masu amanna da tsarin?."
- Gwamna Uba Sani
Abin da Kwankwaso ya ce kan shari'ar NDC

Kara karanta wannan
NDC ta ɗauki mataki bayan hukuncin kotu, ta fara tura sunayen 'yan takara ga INEC
A wani labarin kuma, kun ji cewa madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi magana kan shari'ar da ake yi da jam'iyyar NDC.
Dan takarar mataimakin shugaban kasar na jam'iyyar NDC, ya tabbatar wa magoya bayansu cewa za a shawo kan matsalolin shari'a da suke fuskanta.
Kwankwaso ya bukaci dukkannin 'yan jam'iyya da magoya bayan NDC da su ci gaba da kasancewa cikin natsuwa duk da kalubalen da ake fuskanta.
Asali: Legit.ng
