Sowore: Kotu Ta Bada Belin Dan Takarar Shugaban Kasa, Ta Gindaya Sharudda

Sowore: Kotu Ta Bada Belin Dan Takarar Shugaban Kasa, Ta Gindaya Sharudda

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya samu beli a wajen kotu a shari'arsa da hukumar DSS
  • Alkakin babbar kotun ta tarayya da ke Abuja ya bada belin Sowore kan kudi Naira miliyan 200 tare da gindaya masa sharuddan da zai cika
  • Hukumar DSS ce ta gurfanar da Sowore a gaban kotun kan zargin cewa ya ci mutuncin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Mai shari'a Mohammed Umar na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya amince da bayar da belin Naira miliyan 200 ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore.

Omoyele Sowore dai yana fuskantar shari'a ne a gaban kotun kan cin mutuncin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Sowore ya samu beli a kotu
Dan takarar shugaban kasa na AAC, Omoyele Sowore Hoto: Omoyele Sowore
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta kawo rahoton cewa alkalin kotun ya bada belin Sowore ne a ranar Talata, 30 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

NDC ta ɗauki mataki bayan hukuncin kotu, ta fara tura sunayen 'yan takara ga INEC

An gindaya sharudda ga Sowore

A cikin sharuddan da aka gindaya, mai shari'a Mohammed Umar ya umarci Sowore ya kawo mutane biyu da za su tsaya masa.

Ɗaya daga cikin waɗanda za su tsaya masa ya kasance basaraken gargajiya ne daga garin su Sowore, yayin da ɗayan kuma dole ne ya kasance yana da fili ko gida a Abuja.

Kotun ta kuma umarci wakilan masu shigar da ƙara da su tantance waɗanda za su tsaya ma sa.

Bugu da ƙari, alkalin ya umarci Sowore da ya miƙa fasfo ɗinsa na fita ƙasashen waje ga mataimakin babban rajistara na kotun har sai an kammala yanke hukunci a kan shari'ar.

Bayan haka, alƙalin ya saki wanda ake ƙarar ga lauyoyinsa kuma ya ɗage sauraron shari'ar zuwa ranar Litinin, 6 ga watan Yulin 2027, domin Sowore ya fara kare kansa a shari'ar.

A baya an tura Sowore gidan gyaran hali

Tun da farko dai alƙalin ya ba da umarnin tsare Sowore a gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja, rahoton Channels tv ya nuna hakan.

Kara karanta wannan

Kungiyar Obidient ta bada tabbaci kan takarar Obi da Kwankwaso a 2027 duk da hukuncin kotu

A cikin wani takaitaccen hukunci, Alƙali Umar ya umarci da a ci gaba da tsare Sowore a gidan gyaran hali har sai an saurara tare da yanke hukunci a kan buƙatarsa ta neman dakatar da umarnin soke belinsa da kuma sammacin kama shi.

Kotu ta bada belin Sowore
Dan gwagwarmaya, Omoyele Sowore Hoto: Omoyele Sowore
Source: Facebook

Alƙalin ya kuma watsar da buƙatar Sowore ta baya wadda ke neman alƙalin ya janye jikinsa daga shari'ar saboda zargin nuna son kai.

Hukumar tsaro ta DSS ta gurfanar da Sowore ne gaban kotun saboda zargin cin mutuncin Shugaba Bola Tinubu ta hanyar kiran sa da “babban mai laifi” a cikin wani sako da ya wallafa a shafukansa na “X” da Facebook.

Sowore ya nuna yatsa ga Ministan Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Omoyele Sowore wanda ya yi takarar shugaban kasa a zaben 2023, ya tunkari Ministan ayyuka, David Umahi a caji ofis.

Omoyele Sowore ya tunkari David Umahi ne kan zargin yana amfani da karfin iko wajen zaluntar wata mata mai suna TracyNither Nicolas Ohiri.

Kalaman Sowore ya rika yi sun fusata ma’aikatan Ministan, inda suka shiga fada da shi, wasu kuma na kokarin ture shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng