Shugaban Majalisar Dokoki Ya Zama Gwamna a Kaduna, Zai Yi Kwana 9 a Mulki

Shugaban Majalisar Dokoki Ya Zama Gwamna a Kaduna, Zai Yi Kwana 9 a Mulki

  • Rt. Yusuf Ibrahim Zailani ya zama gwamnan rikon kwarya bayan Gwamna Nasir El-Rufai ya yi tafiya
  • Malam Nasir El-Rufai ya aikawa ‘yan majalisa takarda cewa zai yi tafiyar mako daya zuwa kasar waje
  • Tun da Mataimakiyar gwamnan Kaduna ba ta nan, Yusuf Ibrahim Zailani zai zama Gwamnan riko

Kaduna - Shugaban majalisar dokoki na jihar Kaduna, Yusuf Ibrahim Zailani ya zama gwamnan Kaduna na rikon kwarya a halin yanzu.

Daily Trust tace Rt. Hon. Yusuf Ibrahim Zailani ya karbi ragamar mulki ne a sanadiyyar rashin Mai girma gwamna da mataimakiyarsa.

Malam Nasir El-Rufai ya kamar hanyar zuwa Turai a ranar Alhamis, 22 ga watan Satumba 2022, ana sa rai zai shafe kimanin mako guda.

A daidai wannan lokaci kuma mataimakiyar gwamnan Kaduna watau Dr. Hadiza Balarabe da ya kamata ta karbi rikon jihar, tayi tafiya.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamna Tambuwal ya karbe mukamin shugaban gwamnonin Najeriya

Hadiza Balarabe ta tafi makarantar Harvard Kennedy School da ke kasar Amurka domin yin wani kwas na samun kwarewa a shugabanci.

A kundin tsarin mulkin Najeriya, idan gwamna da mataimakin gwamna ba su nan, na uku a jiha shi ne shugaban majalisar dokokin jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan Kaduna
Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai Hoto: @GovKaduna
Asali: Twitter

El-Rufai ya sanar da majalisa

Hakan ta sa Malam El-Rufai ya aikawa majalisa wasika, yana cewa ya damka jagoranci a hannun Yusuf Ibrahim Zailani kafin ya dawo.

Legit.ng Hausa ta samu ganin wannan gajerar wasikar, a ciki gwamnan yace ba zai dawo Najeriya ba sai Asabar, 1 ga watan Oktoban 2022.

El-Rufai bai fadi abin da zai kai shi Turai ba, amma sanannan abu ne cewa yana karatun digirinsa na PhD a wata jami’a a kasar Holland.

“Kamar yadda kundin tsarin mulki (sashe na 190) ya yi tanadi, shugaban majalisa, zai rike ragamar jihar yayin da gwamna da mataimakiya ba su nan."

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Yadda Wani Gwamna da Ayu suka Kitsawa Wike Kullaliya inji Jang

- Nasir El-Rufai

Zailani mai wakiltar Igabi ya zama shugaban majalisa ne a farkon 2020, bayan Rt. Hon. Aminu Shagali ya yi murabus daga kan kujerar.

Timipre Sylva ya samu sarauta

Saboda yadda ya taimakawa yankin Arewa a mulkin Muhammadu Buhari watau Bayajidan Daura, kun ji Ministan fetur ya samu sarauta.

Sarkin Daura, Dr. Faruk Umar Faruk ya ba Ministan fetur, Timipre Sylva, sarautar Sarkin Kudun Hausa, ana sa ran nan gaba za ayi nadin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng