An Gano Yadda Aka Bindige Jigon APC a Kofar Gidansu bayan Sauya Jam'iyya

An Gano Yadda Aka Bindige Jigon APC a Kofar Gidansu bayan Sauya Jam'iyya

  • Wani jigon APC ya ce wasu da ake zargin 'yan daba na siyasa sun harbe shi a Osun bayan ya sauya sheka
  • Mutumin ya ce maharan sun biyo shi ne saboda goyon bayan ɗan takarar APC, Asiwaju Bola Oyebamiji, kuma ya roƙi gwamnati da 'yan sanda su kare shi da iyalansa
  • Wani ɗan ƙungiyar makaɗa, Ayoola Idowu, shi ma ya ce wasu ɓata-gari sun kai masa hari a yankin Gbonmi yayin da yake tattara kayan kiɗansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Osogbo, Osun - An yi zargin cewa wasu 'yan daba na siyasa sun harbe wani jigon jam'iyyar APC, Taoreed Mustapha a jihar Osun.

Lamarin ya faru ne da safiyar Asabar 27 ga watan Yunin 2026 a gaban gidan mahaifinsa da ke yankin Oluode Aranyin a Osogbo.

Kara karanta wannan

Zaben gwamna: 'Yan daba sun buɗe wa mutane wuta, sun harbi wani jigon APC a Osun

N harbe jigon APC a Osun
Taswirar jihar Osun da ke Kudu maso Yammacin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Da yake magana da manema labarai lokacin da ɗan takarar APC, Oyebamiji, ya kai masa ziyara a asibitin da ake kula da shi, Mustapha ya ce maharan sun zo kan babura uku, cewar Tribune.

Musabbabin harbin jigon APC a Osun

Mustapha ya bayyana cewa a baya yana jam'iyyar Accord, amma ya sauya sheka zuwa APC domin mara wa takarar Asiwaju Bola Oyebamiji, wanda aka fi sani da AMBO.

Ya ce tsakanin ƙarfe 6:30 zuwa 7:00 na safe ya hango mutane tara a kan babura uku, suka sauka, suka nuna shi da hannu, sannan nan take suka fara harbe shi.

Mustapha ya ce tun bayan da ya sauya sheka daga Accord zuwa APC, ana ci gaba da neman kashe shi, yana mai roƙon jama'a da hukumomi su taimaka wajen ceton rayuwarsa.

Ya ƙara da cewa mutanen da suka kai masa harin tsofaffin abokan siyasarsa ne a jam'iyyar Accord, kuma ya ce ya san ɗaya daga cikinsu mai suna Ayo sosai.

Kara karanta wannan

Jigon PDP ya karaya, ya fadi yawan jihohi da Tinubu zai lashe a zaben 2027

Yan daba sun harbi jigon APC a Osun
Shugaban jam'iyyar APC a Najeriya, Nentawe Yilwatda. Hoto: Professor Nentawe Yilwatda.
Source: Facebook

Mahara sun yi wa jigon APC fashi

A cewarsa, maharan sun kuma kwace duk abin da yake ɗauke da shi lokacin harin, sannan ya yi kira ga gwamnati da 'yan sanda su kare shi da 'ya'yansa.

A wani asibitin kuma, wani ɗan ƙungiyar makaɗa mai suna Ayoola Idowu ya ce wasu ɓata-gari sun kai masa hari a yankin Gbonmi da ke Osogbo, cewar Vanguard.

Idowu ya bayyana cewa an kai masa harin ne yayin da yake tattara kayan kiɗansa, lamarin da ya ƙara nuna yadda ake samun hare-hare a yankin.

Babbar mota ta hau kan ƴan APC

Mun ba ku labarin cewa rahoto ya nuna cewa an tabbatar da mutuwar wani dan APC bayan wata babbar mota ta burma cikin jerin masu kamfen na jam'iyyar a Osun.

Bayanan da aka fitar sun nuna cewa mutane bakwai ne sun jikkata a hadarin, yayin da ɗaya daga cikinsu kuma ke cikin mawuyacin hali a asibiti.

Jam'iyyar APC ta buƙaci a yi cikakken bincike game da hadarin, tana zargin cewa direban motar na iya burmawa kan mutanen ta da gangan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.