Obasanjo @ 80: Wanene Olusegun Obasanjo?

Obasanjo @ 80: Wanene Olusegun Obasanjo?

A yau ne tsohon shugaban kasar nan Cif Olusegun Mathew Aremu O. Obasanjo ya cika shekaru 80 da haihuwa. Ko da yake dai tsohon shugaban kasar yace bai ma san ranar da aka haife sa ba.

Obasanjo @ 80: Wanene Olusegun Obasanjo?
Obasanjo @ 80: Wanene Olusegun Obasanjo?

An haifi Olusegun Obasanjo shekaru 80 da suka wuce a Jihar Ogun, ta kai dai babu wanda ya mulki Najeriya na tsawon lokacin kamar tsohon shugaba Obansajo. Cif Obasanjo da shugaba Buhari ne kadai suka mulki Najeriya a zamanin Soji da kuma farar hula a tarihin kasar.

Obasanjo wanda Injiniya ne na Sojoji ya mulki kasar nan daga shekarar 1976 bayan an kashe Janar Murtala Muhammad zuwa shekarar 1979. A watan Oktoban 1979 ne Obasanjo ya mikawa Alhaji Shehu Shagari mulki bayan an yi zaben farar hula. Kusan dai ba a taba yin wannan abu a tarihin Afrika ta yamma ba a wancan lokaci. Hakan ta sa har ya kusa samun kujerar Majalisar dinkin Duniya.

KU KARANTA: Obasanjo tagwaye ne dama?

Obasanjo @ 80: Wanene Olusegun Obasanjo?
Obasanjo @ 80: Wanene Olusegun Obasanjo?

An so Obasanjo ya karbi mulkin rikon kwarya a karshen mulkin Babangida wanda hakan bai yiwu ba; ta kai aka mikawa Cif Ernest Shonekna. Sai dai kuma a lokacin mulkin Janar Sani Abacha, an kama Janar Obasanjo an rufe da laifin kokarin kifar da Gwamnatin Sojin Janar Sani Abacha.

Bayan rasuwar Abacha ne dai Obasanjo ya fito daga gidan yari inda ya tsaya takara a karkashin Jam’iyyar PDP ya kuma yi nasara. Obasanjo yayi shekaru takwas a jere yana mulki har ma yayi kokarin ya kara zarcewa na gaba wanda dokar kasa ta taka masa burki.

Obasanjo @ 80: Wanene Olusegun Obasanjo?
Obasanjo @ 80: Wanene Olusegun Obasanjo?

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel