Ahmad Babba Kaita ya samu kuri’a 224, 607 a zaben Sanatan Katsina

Ahmad Babba Kaita ya samu kuri’a 224, 607 a zaben Sanatan Katsina

‘Dan takarar Jam’iyyar APC mai mulki a zaben Sanatan Yankin Arewacin Katsina watau Honarabul Ahmad Babba-Kaita ya lashe zaben ‘Dan Majalisar da aka yi jiya Ranar Asabar. Babba Kaita ‘Dan Majalisar Jihar ne yanzu haka.

Ahmad Babba Kaita ya samu kuri’a 224, 607 a zaben Sanatan Katsina
Lokacin da Mukaddashin Shugaban kasa ya zo Daura kamfe

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa ‘Dan takarar APC ne zai lashe zaben da aka gudanar jiya a Yankin Daura. APC ce za tayi nasara ko da kawo yanzu dai Hukuma rzabe na kasa watau INEC ba ta sanar da sakamakon zaben ba.

Mun samu labari cewa ‘Dan takarar na Jam’iyyar APC mai mulki watau Ahmad Babba Kaita ya samu kuri’u 224, 607 wanda ya nuna ya sha gaban kowa a zaben. Babbar Jam’iyyar adawa ta PDP ce ta zo ta biyu da kuri’u sama da 59, 700.

KU KARANTA: Shugaban Jam'iyyar APC ya bayyana yadda su ka kwashe da Tambuwal

‘Yan takarar da su ka sha kashi sun hada da Kabir Babba-Kaita wanda ‘Dan uwan ‘Dan takarar APC da yayi nasara ne. Jam’iyyar GPN ta samu kuri’u 1056 yayin da DA ke da 796 a zaben. Jam’iyyar MPN da MMN sun samu kuri’u 633 da 343.

An yi zaben ne bayan rasuwar Sanatan Yankin watau Mustapha Bukar wanda ya bar Duniya kusan watanni 4 da su ka wuce. A akwatin Unguwar Sarkin Yara ‘A’ wanda nan ne inda Shugaban kasa Buhari yake zabe APC ta samu kuri’a 1984.

Dazu kun ji labari cewa Jam’iyyar APC mai mulki ta kama hanyar lashe zaben wasu ‘Yan Majalisu da aka yi a Arewa Jihohin Bauchi da kuma Katsina da ma Jihar Kogi a karshen wannan mako.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng