Ran Shugaban Gwamnonin Arewa Ya Baci kan Surutu Babu Aiki, Ya Kawo Mafita

Ran Shugaban Gwamnonin Arewa Ya Baci kan Surutu Babu Aiki, Ya Kawo Mafita

  • Shugaban kungiyar gwamnonin jihohin Arewa (NSGF) kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi kira kan matsalolin tsaro
  • Gwamna Inuwa Yahaya ya yi kiran ne a ranar Litinin yayin da yake gabatar da saƙon fatan alheri a taron Majalisar sarakunan gargajiya ta Arewa
  • Taron ya samu halartar gwamnoni, sarakunan gargajiya, shugabannin hukumomin tsaro da wakilan gwamnatin tarayya domin tattauna batun tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Jigawa — Shugaban kungiyar gwamnonin Arewa, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi kira da a ɗauki matakan gaggawa kuma masu ƙarfi domin magance matsalolin tsaro, talauci da rashin ci gaba da ke ƙara ta’azzara a Arewacin Najeriya.

Ya yi magana yana mai bayyana cewa lokacin yawan taruka da fitar da shawarwari ba tare da aiwatar da su ba ya kamata ya zo ƙarshe.

Kara karanta wannan

Tsaro: An kafa zafafan dokoki a Katsina, an hana POS, cajin waya da sauransu

Sultan, Inuwa Yahaya da Umar Namadi a Jigawa
Sarkin Musulmi, Gwamnan Jigawa da Gwamna Inuwa Yahaya a Dutse wajen taron sarakuna a Arewa. Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

Mai magana da yawun Inuwa Yahaya, Isma'ila Uba Misilli ya wallafa a Facebook cewa gwamnan ya yi maganar ne da yake jawabi a taron majalisar sarakunan gargajiya ta Arewa a Dutse, jihar Jigawa.

Kira ga shugabannin Arewa

Inuwa Yahaya ya buƙaci 'yan siyasa, sarakuna, hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki da su wuce matakin magana kawai su rungumi mafita ta zahiri da za ta iya dawo da zaman lafiya, kwanciyar hankali da bunƙasar yankin.

Ya bayyana halin tsaro a yankin a matsayin abin damuwa ƙwarai, yana mai cewa ’yan bindiga, rikicin makiyaya da manoma sun cigaba da lalata al’ummomi, kawo cikas ga tattalin arziki da raunana haɗin kan jama’a.

“Idan ba tsaro, babu haɗin kai. Idan ba tsaro da haɗin kai ba, ba za a samu cigaba ba,”

In ji shi.

Alakar talauci da matsalar tsaro

Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana cewa matsalar tsaro a Arewa ba ta samo asali daga aikata laifffuuka kaɗai ba, tana da alaƙa da shekaru masu yawa na rashin kula da harkokin zamantakewa da tattalin arziki.

Kara karanta wannan

"Sabuwar kungiyar ta'addanci za ta fara aiki a Najeriya," An gargadi Bola Tinubu

A cewarsa, kimanin mutane miliyan 86 a Arewacin Najeriya na fama da talauci mai fuskoki da dama, yayin da yankin ke ɗauke da mafi yawan yara marasa zuwa makaranta a ƙasar.

Ya yi gargaɗin cewa yaɗuwar talauci, rashin aikin yi da ƙarancin damar samun ilimi sun samar wa ƙungiyoyin masu laifi da masu tsattsauran ra’ayi damar ɗaukar matasa masu rauni zuwa cikinsu.

Wasu sarakuna a wajen taro a Dutse
Sarkin Gombe tare da wasu sarakunan Arewa wajen taro a Dutse, jihar Jigawa. Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

Kiran yin gyare-gyare a Arewa

Domin sauya wannan hali, Inuwa Yahaya ya ba da shawarar aiwatar da manyan gyare-gyare da suka haɗa da kafa ’yan sandan jihohi, ƙara zuba jari a ilimi da koyar da sana’o’i, ƙarfafa matasa, farfaɗo da harkar noma.

Ya kuma buƙaci shugabannin Arewa su nuna ƙwazo wajen aiwatar da shawarwarin da ake cimmawa zuwa aiki a zahiri:

“Mun gaji da tarukan da ba sa haifar da sakamako. Mun gaji da sanarwar bayan taro da ba a aiwatarwa. Mun gaji da alkawuran da ba a cikawa,”

In ji shi.

Gwamnan Gombe ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga gwamnatin da al’ummar Jihar Katsina kan rasuwar Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya.

Vanguard ta wallafa cewa Inuwa Yahaya ya jaddada muhimmiyar rawar da sarakunan gargajiya ke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

Kara karanta wannan

Abin ba dadi: Manjo Janar Rabe Abubakar ya mutu a hannun 'yan bindiga

Jihar Katsina ta dauki matakan tsaro

A wani labarin, mun kawo muku cewa Gwamnatin jihar Katsina ta dauki sababbin matakan tsaro domin yaki da 'yan ta'adda masu garkuwa da mutane.

Gwamna Dikko Radda ya sanar da cewa an hana sana'ar cajin waya, acaba, POS da sayar da fetur a cikin jarakuna a wasu kananan hukumomi.

Yayin da ya ke gargadi ga jama'a, Dikko Radda ya bayyana cewa ba za a sassauta wa duk wanda ya karya dokokin da aka sanya a jihar ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng