Kebbi: Yadda Zaben Cike Gurbi Ya Jawo wa Wasu Shugabannin APC Rasa Kujerunsu

Kebbi: Yadda Zaben Cike Gurbi Ya Jawo wa Wasu Shugabannin APC Rasa Kujerunsu

  • An dakatar da shugaban jam'iyyar APC na jihar Kebbi, Alhaji Abubakar Kana-Zuru bisa takaddamar da ta tashi bayan zabukan cike gurbi
  • APC ta sanar da cewa ta gudanar da bincike kan korafe-korafen da aka shigar, kuma ta tabbatar da wasu daga cikin matsalolin da aka gabatar
  • A hannu daya, Gwamna Nasir Idris ya dakatar da kwamishinan raya kiwon dabbobi da kamun kifi, Kabir Zuru ba tare da ranar dawowa aiki ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kebbi - APC reshen Kebbi ta dakatar da shugaban jam’iyyar na jiha, Abubakar Kana-Zuru, da shugabanta na karamar hukumar Zuru, Aliyu Abiola.

Jam’iyyar ta ce matakin ya biyo bayan damuwa da aka samu kan yadda ta gudanar da ayyukanta a zaben cike gurbin mazabar Zuru da aka kammala kwanan nan.

Kara karanta wannan

Rigima ta kunno kai, an dakatar da shugaban jam'iyyar APC da kwamishina a jihar Kebbi

APC ta dakatar da shugabanta na jihar Kebbi saboda abin da ya faru a zaben fitar da gwani.
Tutar jam'iyyar APC a wani gangamin siyasa da aka gudanar. Hoto: @OfficialAPCNg
Source: Twitter

An dakatar da shugabannin APC a Kebbi

Sanarwar dakatarwar ta fito ne daga hannun sakataren APC na jihar, Sa’idu Muhammad Kimba, inda aka bayyana cewa an dauki matakin ne bayan korafe-korafen wasu masu ruwa da tsaki a Zuru, in ji rahoton Channels TV.

A cewar jam’iyyar, an zargi shugabannin da aka dakatar da nuna rashin himma wajen gudanar da ayyukan jam’iyya, rashin kyakkyawar hulda da muhimman masu ruwa da tsaki, da kuma gazawar hada kan magoya bayan APC.

Haka kuma, jam’iyyar ta ce akwai zargin rashin bin wasu ka’idojin cikin gida na jam’iyyar.

APC ta bayyana cewa ta gudanar da bincike kan korafe-korafen, inda ta ce an tabbatar da wasu daga cikin matsalolin da aka gabatar.

Wanda zai jagoranci APC a Kebbi

Bayan dakatar da Kana-Zuru, jam’iyyar ta umurci mataimakin shugaban APC na jihar da ya rike shugabancin jam’iyyar a matsayin mukaddashin shugaban har sai an sake ba da wani umarni.

Kara karanta wannan

APC ta yi shiri, ta fadi yadda za ta lashe zabe a dukkan kananan hukumomin Gombe

Shi ma Aliyu Abiola an dakatar da shi daga matsayin shugaban APC na karamar hukumar Zuru, kuma jam’iyyar ba ta bayyana tsawon lokacin da dakatarwar za ta dauka ba.

Gwamna Nasir Idris ya dakatar da kwamishina daga aiki
Gwamnan jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris yana jawabi a wani taro. Hoto: @NasiridrisKG
Source: Facebook

Gwamna ya dakatar da kwamishina

A wani mataki makamancin haka, Gwamnan Kebbi, Nasir Idris, ya amince da dakatar da kwamishinan Raya Dabbobi da Kamun Kifi na jihar, Kabir Zuru, cewar rahoton Punch.

Sakataren gwamnatin jihar (SSG), Yakubu Bala-Tafida, ne ya sanar da dakatarwar, inda ya ce matakin ya fara aiki nan take kuma zai ci gaba har sai an sake fitar da wani umarni.

An umurci kwamishinan da ya mika dukkan kadarorin gwamnati da nauyin da ke karkashinsa ga babban sakataren ma’aikatar.

An yi kokarin samun martanin wadanda aka dakatar, amma har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a samu amsa daga gare su ba.

Tsohon shugaban APC a Kebbi ya rasu

A wani labari, mun ruwaito cewa, tsohon shugaban APC na karamar hukumar Koko/Besse a Kebbi, Alhaji Muhammadu Besse, ya rasu a hannun ‘yan bindiga.

Majiyoyi sun ce an yi garkuwa da Besse ne a farkon watan Yunin shekarar 2026, kuma tun daga lokacin iyalansa da magoya bayansa suka kasance cikin damuwa da fargaba.

Mutuwar Alhaji Besse ta kara jawo tambayoyi masu yawa kan matsalar tsaro da ke addabar al’ummomi a sassan Arewacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com