'Da Man Fetur Ya Kai N10,000': Sarki Ya Fadi yadda Dangote Ya Ceci Najeriya

'Da Man Fetur Ya Kai N10,000': Sarki Ya Fadi yadda Dangote Ya Ceci Najeriya

  • Aluwo na Iwo, Oba Abdulrosheed Adewale Akanbi, ya yi magana game da tsadar man fetur a kasar Najeriya
  • Basaraken ya ce matatar mai ta Aliko Dangote ta ceci tattalin arzikin Najeriya daga durkushewa gaba daya
  • Sarkin ya bayyana cewa da ba a samu matatar Dangote ba, farashin litar fetur zai iya kaiwa N10,000 sakamakon tsadar danyen mai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Iwo, Osun - Aluwo na Iwo, Oba Abdulrosheed Adewale Akanbi, ya bayyana yadda matatar Aiko Dangote ta ceci Najeriya.

Sarkin ya ce matatar mai ta Dangote ta hana tattalin arzikin Najeriya fadawa cikin matsanancin hali tare da kare talakawa daga tsananin wahala.

Sarki ya yabawa Dangote kan kokarin ceto Najeriya
Sarkin Iwo da ke jihar Osun, Abdulrosheed Adewale Akanbi. Hoto: @MandieBrowne.
Source: Twitter

Hakan na cikin wata sanarwa da sakataren yada labaransa, Alli Ibraheem, ya fitar, wanda Tribune ta samu.

Sarki ya fadi yadda Dangote ya ceci Najeriya

Kara karanta wannan

Davido: Malamin Musulunci ya yi wa Rarara wankin babban bargo kan tsaro

Basaraken ya ce da ba a samu wannan matata ba, da ‘yan Najeriya suna iya sayen litar fetur har N10,000.

Ya bayyana cewa hauhawar farashin danyen mai a kasuwannin duniya da kuma rikice-rikicen siyasa tsakanin kasashe sun sa farashin makamashi ke kara tashin gwauron zabo.

Oba Akanbi ya bayyana Alhaji Aliko Dangote a matsayin bakar fata da ya dauki nauyin gina katafariyar matatar mai da kudinsa, wadda yanzu ke fitar da kayayyaki.

Ya ce matatar ta bai wa Najeriya da baki gaba daya karfin tattaunawa a tattalin arzikin duniya, musamman lokacin da ake fuskantar matsalolin samar da mai.

Sarki ya karrama Dangote saboda kokarinsa a tattalin arziki
Attajiri a Najeriya, Alhaji Aliko Dangote. Hoto: Dangote Group.
Source: UGC

Yadda yakin Amurka, Iran ya shafi makamashi

Sarkin ya ce rikicin Amurka da Iran ya janyo tangarda a harkokin makamashi a duniya, amma matatar Dangote ta taimaka wajen rage tasirin matsalar.

Ya kuma yi nuni da cewa matatar ta kara karfin tace mai daga ganga 650,000 zuwa ganga 700,000 a kullum, abin da ya nuna ci gabanta.

Wannan karin karfi ya samu tabbaci daga mataimakin shugaban bangaren mai da iskar gas na Kamfanin Dangote, Devakumar Edwin.

Kara karanta wannan

Za a kashe N83bn kan ambaliya a Najeriya, Shettima ya yi muhimmin kira ga jihohi

A cewarsa, kamfanin na da burin kaiwa ganga miliyan 1.4 a kullum nan da shekarar 2028 domin zama cibiyar tace mai mafi girma.

Oba Akanbi ya ce idan aka cimma wannan buri, zai taimaka wajen dawo da martabar Najeriya a matsayin babbar kasa a nahiyar Afrika, cewar The Nation.

Sarkin ya ce kayayyakin Dangote yanzu suna isa kasuwanni daban-daban a Afrika, Turai, Amurka da kuma Saudiyya, musamman man jiragen sama.

Oba Akanbi ya ce an karrama Dangote a kasashen waje, don haka ya cancanci samun karin yabo da girmamawa a cikin gida.

A matsayin karramawa, Aluwo na Iwo ya ba Aliko Dangote sarautar “Atayero na Najeriya,” ma’ana wanda ya tace Najeriya.

Babban Sarki ya tallata Tinubu

Mun ba ku labarin cewa yan Najeriya da dama sun taya shugaba Bola Ahmed Tinubu murnar cika shekara 74 a duniya, inda aka yi masa fatan alheri game da mulkin da ya ke.

Sarkin Iwo, Oba Abdulrosheed Akanbi ya hararo wasu abubuwa da za su iya faruwa da ya ce za su iya jawo a nemawa Tinubu wa'adin mulki na uku.

Oba Abdulrosheed Akanbi ya bayyana dalilan da suka sanya shi maganar a wani sako da ya fitar yana taya shugaban kasar murnar cika shekara 74.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.