INEC Ta Goyi bayan ADC da Sauran Jam'iyyun da Kotu Ta Bukaci a Soke Su
- Hukumar INEC ta garzaya Kotun Daukaka Kara a Abuja game da bukatar wata kotu da a soke rijistar wasu jam'iyyu
- INEC ta ce ta yi mamakin yadda kotun farko ta yanke hukunci duk da umarnin Kotun Daukaka Kara na dakatar da hakan
- Lauyoyin jam'iyyun sun gargadi cewa hukuncin na iya haddasa rudani ga zabukan cike gurbi da za a gudanar a jihohi shida
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta garzaya Kotun Daukaka Kara kan bukatar wata kotu kan jam'iyyun adawa.
Hukumar ta je kotun ne domin neman a dakatar da aiwatar da hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ya umarci soke rijistar jam'iyyar ADC da wasu jam'iyyu guda hudu.

Source: Twitter
Punch ta ruwaito cewa Kotun da ke Abuja karkashin Mai Shari'a Peter Lifu ta umarci INEC ta soke rijistar jam'iyyun ADC, APP, AA, Accord Party da ZLP.
Dalilin Hukumar INEC na daukaka kara
Har ila yau, hukumar zaben ta goyi bayan takardar daukaka kara da jam'iyyun da abin ya shafa suka shigar domin kalubalantar hukuncin da kotun ta yanke.
Kotun ta yanke cewa jam'iyyun sun gaza cika sharuddan kundin tsarin mulki da ake bukata domin ci gaba da kasancewa a matsayin jam'iyyun siyasa masu rijista.
A ci gaba da sauraron karar a gaban alkalai uku na Kotun Daukaka Kara, lauyan INEC, Haliru Mohammed, ya ce hukumar ta yi mamakin yadda kotun kasa ta ci gaba da fitar da hukuncin.
Mohammed ya kara da cewa ba su samu wata sanarwa daga kotun kan ranar fitar da hukuncin ba, sai dai suka gani ne a matsayin labarin gaggawa a kafafen yada labarai.
Saboda haka, ya ce hukumar INEC ba ta adawa da bukatar masu daukaka kara na neman a dakatar da aiwatar da hukuncin da aka yanke.

Source: Twitter
Abin da lauyan jam'iyyar ADC ya ce

Kara karanta wannan
"Muna kira ga fannin shari'a"; Atiku ya dauki zafi kan umarnin kotu na soke rajistar ADC
Lauyan ADC, Mista Shuaibu Aruwa SAN, ya kuma shaida wa kotun cewa jam'iyyar ta samu labarin hukuncin ne ta hanyar sakon WhatsApp daga kotun da ta fara sauraron karar.
Aruwa ya bukaci Kotun Daukaka Kara ta shiga lamarin, yana mai cewa an fitar da hukuncin ne duk da cewa akwai umarnin kotun da ke dakatar da hakan.
Ya ce:
"Abin da alkalin kotun tarayya ya yi tamkar kalubalantar ikon Kotun Daukaka Kara ne bayan an jawo hankalinsa kan umarnin dakatarwa."
Ya kara da cewa lokaci ya yi da kotun za ta dauki matakin gaggawa domin kare mutuncinta tare da sake daidaita al'amuran shari'a, cewar Daily Post.
Lauyoyin sauran jam'iyyun da abin ya shafa sun kuma ja hankalin kotun kan zabukan cike gurbi da INEC ta tsara gudanarwa a ranar 20 ga Yuni a jihohi shida.
Sun ce idan aka bar hukuncin ya ci gaba da aiki, zai iya haifar da rudani da rashin tabbas a tsarin gudanar da wadannan zabuka.
An maka INEC, yaron Wike a kotu
A wani labarin, an ji cewa dan wasan Nollywood, Emeka Ike, ya kai karar hukumar INEC da mai taimaka wa Nyesom Wike a babbar kotun Abuja.
Ike wanda ya shiga siyasa ya ce wallafa bayanansa a kafofin sadarwa ya saba hakkinsa na sirri kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
Ya bukaci kotu ta umarci a goge sakon, a nemi afuwarsa a fili, tare da bugawa a jaridu uku na kasa saboda lahanin da aka yi masa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

