Jarumin Fim Ya Maka INEC, Hadimin Wike a Kotu, Ya Buƙaci Diyyar N10bn

Jarumin Fim Ya Maka INEC, Hadimin Wike a Kotu, Ya Buƙaci Diyyar N10bn

  • Jarumin Nollywood, Emeka Ike, ya kai karar hukumar INEC da mai taimaka wa Nyesom Wike a babbar kotun Abuja
  • Ike ya ce wallafa bayanansa a kafofin sadarwa ya saba hakkinsa na sirri kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada
  • Ya bukaci kotu ta umarci a goge sakon, a nemi afuwarsa a fili, tare da bugawa a jaridu uku na kasa saboda barnar da aka yi masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Jarumin Nollywood, Emeka Ike, ya shigar da kara a babbar kotun tarayya da ke Abuja kan zargin karya dokokin kare bayanan sirri.

Ike ya maka Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, da Lere Olayinka, mai taimaka wa ministan Abuja, Nyesom Wike.

An maka yaron Wike da INEC a kotu
Hadimin Nyesom Wike, Lere Olayinka a wajen wani taro. Hoto: Lere Olayinka.
Source: Facebook

An maka yaron Wike, INEC a kotu

Kara karanta wannan

Zaɓen 2027: Peter Obi ya bayyana abin da zai fara yi game da Nnamdi Kanu

An shigar da karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1272/2026, 15 ga watan Yuni, ta hannun lauyansa, Leonard Adeh, Ike ya ce an saba ka'ida bayan an yada bayanansa na rajistar zabe ba tare da yardarsa ba, cewar TheCable.

Lamarin ya samo asali ne bayan Olayinka ya wallafa hotunan bayanan canjin wurin rajistar zaben Ike daga Imo zuwa Abuja a shafukan sadarwa a watan Mayun 2026.

Ya yi hakan ne yayin da yake tambayar cancantar jarumin wajen neman kujerar majalisar wakilai a Abuja.

Wannan wallafa bayanai ya jawo cece-kuce a tsakanin 'yan Najeriya, inda mutane da dama suka zargi Olayinka da samun damar shiga wata kafar bayanai ta sirri da aka tanada domin ma'aikatan INEC kadai.

Daga baya, INEC ta musanta rade-radin cewa an yi kutse cikin babbar ma'adanar bayanan rajistar masu zabe.

Hukumar INEC ta ce wasu masu izinin shiga tsarin ne suka yi amfani da bayanan da aka ba su ta hanyar da ba ta dace ba.

Jarumin fim ya maka INEC da hadimim Wike a kotu
Shugaban hukumar INEC, Joash Amupitan. Hoto: INEC Nigeria.
Source: Twitter

Bukatar jarumin fim ga hukumar INEC

Ike ya bukaci kotu ta ayyana cewa wallafa bayanansa ba tare da amincewarsa ba ya saba wa hakkinsa na sirri da kariyar bayanan jama'a, kamar yadda sashe na 37 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.

Kara karanta wannan

Kotu ta yi umarni a kama tsohon ministan Tinubu da ya samu takarar gwamna

Jarumin ya ce INEC na da alhakin kare bayanan masu kada kuri'a daga shiga hannun wadanda ba su da izini, saboda ita ce ke kula da adanawa da tsaron irin wadannan bayanai.

Ya kuma bukaci kotu ta ayyana cewa sanarwar da INEC ta fitar ranar 2 ga Yunin 2026 ta nuna amincewa da gazawar da aka samu wajen kare bayanansa daga amfani da su ba bisa ka'ida ba.

Ike ya roki kotu ta umurci Olayinka ya goge sakon da ya wallafa a kafofin sadarwa, sannan ya rubuta cikakken neman afuwa gare shi saboda karya hakkinsa na sirri, cewar Punch.

Bugu da kari, Ike yana neman a biya shi diyyar Naira biliyan 10 a matsayin diyya daga INEC da Olayinka saboda take masa hakkinsa na sirri da kare bayanansa.

Yan sanda sun yi wa hadimin Wike tambayoyi

A wani labarin, an ji cewa an yi wa hadimin Nyesom Wike, Lere Olayinka tambayoyi a hannun ‘yan sanda kan fitar da bayanan masu kada kuri’a daga shafin hukumar zabe ta kasa (INEC).

Masu bincike daga sashen leken asiri na rundunar ‘yan sanda sun yi wa Lere Olayinka tambayoyi a ranar Talata a hedikwatar ‘yan sanda da ke birnin Abuja.

Wannan tambayoyin wani bangare ne na bincike kan laifin yanar gizo, amfani da ma’ajiyar bayanai ba tare da izini ba, da kuma fitar da takardun sirri na kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.