Bayan Takun Saka, Gwamna Ya Hana Davido Shiga Jiharsa Sai bayan Mulkinsa
- Mataimakin gwamnan Edo kan kafafen sada zumunta ya ce an hana Davido yin wasa a Edo har zuwa ƙarshen wa’adinsu
- Dan siyasar ya ce Davido ya yi kalaman rashin mutunci kan gwamnan Edo da iyalansa, bayan rikicin da ya taso tsakaninsu
- Ya kuma yi gargadin cewa wasu matasan Edo sun fusata da kalaman Davido, yana cewa hakan na iya jawo masa matsala
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Edo - Babban mataimaki na musamman ga gwamnan Edo ya yi wa mawaki David Adelek da aka fi sani d Davido barazana.
Apostle Kassy Chukwu, ya ce Davido bai kamata ya yi tsammanin yin wasa a jihar ba har sai bayan sun kammala mulinsu.

Source: UGC
Chukwu ya bayyana hakan ne a wani bidiyo da kafar Peniel TV International Benin City ta wallafa a YouTube ranar Alhamis 20 ga watan Agustan 2027.
Musabbabin rikicin a tsakanin gwamna da Davido
Kalaman mataimakin gwamnan sun biyo bayan ƙin Davido ya ba da haƙuri kan kalaman da ya yi game da Gwamna Monday Okpebholo.
Rikicin ya samo asali ne bayan Okpebholo ya soki Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, wanda shi ne kawun Davido, yayin da ake shirye-shiryen zaɓen gwamnan Osun na ranar 15 ga Agusta.
A baya Davido ya wallafa wani sakamakon WAEC da ya yi ikirarin cewa na Okpebholo ne a shafinsa na Instagram, sannan ya kare matakin a wata hira.
Mawakin ya ce babu wani dalili da zai sa ya ba da haƙuri kan wallafar da ya yi game da sakamakon karatun gwamnan.
Martanin gwamnatin Edo ga Davido
Da yake martani, Chukwu ya ce an haramta wa Davido yin wasa a Edo har zuwa ƙarshen wa’adin gwamnatin Okpebholo.
Ya ce:
“An hana ka zuwa Edo domin yin wasa. Ba ma son ganinka a Edo kuma.”
Chukwu ya zargi Davido da yin kalaman rashin mutunci kan gwamnan da iyalansa, yana mai cewa ba za a marabce shi a jihar ba.
Ya kuma ce wasu matasan Edo sun fusata da kalaman Davido, yana gargadin cewa mawakin na iya fuskantar rashin kyakkyawar tarba idan ya sake dawowa jihar.
Chukwu ya ce matasan Edo sun bayyana cewa ba sa son a sake kawo Davido domin yin wasa a wani wuri a jihar saboda cin mutuncin gwamnasu.
Hadimin gwamnan ya kuma soki wallafar Davido kan tarihin karatun Okpebholo, yana zargin cewa an yi wa takardar sauyi tare da gargadin mawakin.
Gwamnatin Edo ta dura kan Davido
An ji cewa gwamnatin Edo ta ba Davido shawara kan yunkurinsa na kai korafi ga Shugaba Donald Trump kan zaben gwamnan Osun wanda aka gudanar.
Kwamishinan yada labaran jihar Edo ya soki matakin Davido na neman Trump ya sa ido kan zaben gwamnan Osun wanda daga bayan Gwamna Ademola Adeleke ya yi nasara.
Kassim Afegbua ya ce sakamakon karatun Gwamna Okpebholo da ake yadawa a intanet na bogi ne kuma ba za su aminta da cin mutuncin mai gidansu ba.
Asali: Legit.ng

