An Shiga Fargaba da Mace Ta Yi Yunkurin Kai Harin Bam a Ginin Majalisar Amurka

An Shiga Fargaba da Mace Ta Yi Yunkurin Kai Harin Bam a Ginin Majalisar Amurka

  • FBI ta kama wata mata bisa zargin shirya kai hari kan Majalisar Dokokin New York, tana da alaka da kungiyar ISIS
  • Ana zargin Bowie da yawan ziyartar Capitol, daukar hotunansa da kuma neman kayan hada bam domin kai hari tare da kashe sanatoci
  • Hukumar FBI ta ce Bowie ta kuma shirya tserewa bayan harin, sannan ta koma Amurka domin wasu hare-hare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka (FBI) ta dakile wani zargin shirin kai harin ta’addanci da ya shafi ISIS a Capitol na New York.

An tuhumi Jessica Bowie, mai shekaru 35 daga Albany, da kokarin bai wa wata kungiyar ta’addanci da aka ayyana tallafi, bayan zargin shirya kai hari kan majalisar a New York na kasar Amurka.

Kara karanta wannan

Yadda sojoji suka ceto bayin Allah a Kebbi da wasu jihohi 2 daga yan bindiga

An yi yunkurin kai hari kan ginin majalisar dokokin Amurka
Shugaba Donald Trump a hagu da majalisar dokokin Amurka a gefen dama. Hoto: Reuters.
Source: Getty Images

An kama mata kan yunkurin harin bam

A cewar karar da aka shigar a wata kotun tarayya da ke Arewacin New York, ana zargin Bowie da gaya wa wani mutum da FBI ta boye sunansa cewa tana goyon bayan kungiyar ISIS, tare da neman taimako wajen koyon yadda ake hada abubuwan fashewa, cewar NBC News.

Hukumar FBI ta kama Bowie ranar Laraba a Albany, ta hannun Joint Terrorism Task Force, kamar yadda Mataimakin Babban Lauyan Amurka John A. Sarcone ya bayyana wa manema labarai ranar Alhamis.

Ana sa ran Bowie za ta gurfana a gaban kotu ranar Alhamis da rana, kan tuhuma guda ta yunkurin bai wa wata kungiyar ta’addanci ta kasashen waje tallafin kayan aiki.

A cewar karar, Bowie ta musulunta shekaru biyar da suka gabata, sannan ta fara tsattsauran ra’ayi ta intanet. Ta kuma kirkiri wasu asusun kafafen sada zumunta da sunayen Musulunci.

Rahoton ya ce wasu daga cikin wadannan asusun ana zargin na Bowie ne, saboda masu samar da su sun dakatar da su akai-akai kan karya ka’idojin amfani da kafafen sada zumunta.

Kara karanta wannan

Mahaifi ya kona 'yar cikinsa saboda malalar fitsarin kwance kullum a gadonsu

Ana zargin ta gaya wa wannan mutumin cewa tana son taimako domin kai hari kan Capitol na New York. Ginin yana kasa da mil biyu daga gidanta.

Wata mata ta shirya kai hari a majalisar Amurka
Shugaban Amurka, Donald Trump jim kadan bayan jawabi ga 'yan majalisar Republican a Doral, Florida. Hoto: Roberto Schmidt.
Source: Getty Images

Yadda aka gano lamuran Bowie

Rahoton ya ce Bowie ta ziyarci Capitol sau biyar tsakanin 21 ga Yuli zuwa 9 ga Agusta, inda jami’an leken asiri suka lura tana daukar hotunan yankin.

Ana zargin Bowie ta ce tana son kai harin a ranar da mafi yawan sanatoci za su kasance a Capitol.

Ana kuma zargin ta da cewa ta ce za ta iya kai hari kan Fadar White House da shugaban Amurka.

Lokacin da aka tambaye ta dalilin da ya sa take son kai hari kan Capitol na jihar, an ce ta amsa cewa a zahiri za ta fi son kai hari kan Fadar White House da shugaban kasa, amma hakan ya fi wahala.

An kuma tambaye ta ko mutuwar wasu mutane, ciki har da Musulmai, za ta dame ta idan harin ya faru, cewar CNN.

A cewar karar, Bowie ta ce hakan zai dame ta, musamman idan akwai Musulmi, yara ko mata masu ciki da suka mutu, sai dai ta ce tana fatan Allah zai gafarta mata.

Kara karanta wannan

Yadda aka cafke jami'in DSS na bogi yana barazana da bindigar karya

Dan majalisar Amurka ya fusata kan harin Plateau

An ji cewa dan majalisa a kasar Amurka, Riley Moore, ya yi martani mai zafi kan kisan da wasu 'yan bindiga suka yi a jihar Plateau.

Riley Moore ya soki gwamnatin Najeriya wajen gaza kare 'yan kasarta amma tana zuwa aikin dakile juyin mulki a wata kasar daban.

Dan majalisar ya bukaci gwamnatin Shugaba Donald Trump da ta dauki mataki kan Najeriya saboda zubar da jinin ake yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.