An Sake Zaben Fidda Gwani a Jigawa, an Maye Gurbin Dan Takarar Sanatan da Ya Rasu

An Sake Zaben Fidda Gwani a Jigawa, an Maye Gurbin Dan Takarar Sanatan da Ya Rasu

  • A sake gudanar da zaben fidda gwanin sanata a jihar Jigawa na jam'iyyar APC, an sanar da sakamako
  • A yau ne aka sanar da Alhaji Mohammad Sabo Nakudu a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin APC
  • Allah ya yiwa dan takarar sanatan jam'iyyar APC a jihar Jigawa rasuwa watanni uku bayan lashe zaben fidda gwani

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Jigawa - A yau Laraba 24 ga watan Agusta ne jam'iyyar APC ta sanar da Alhaji Mohammad Sabo Nakudu a matsayin wanda ya lashe sabon zaben fidda gwain sanata, wanda ya maye gurbin Tijjani Ibrahim.

Watanni uku bayan da INEC ta ayyana shi a matsayin dan takarar sanatan APC, Allah ya yiwa Tijjani rasuwa a ranar 13 ga watan Agusta, lamarin da ya kai ga sake zaben fidda gwanin.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kwamitin Gudanarwar Uwar Jam'iyyar PDP Ta Shiga Ganawar Sirri da Yan Takara

A wata sanarwa da Legit.ng Hausa ta samu daga ofishin yada labarai ta gwamnatin jihar Jigawa, an bayyana yadda zaben ya gudana.

An sake zaben fidda gwani, an baye gurbin Tijjani Ibrahim
An Sake Zaben Fidda Gwani a Jigawa, an Maye Gurbin Dan Takarar Sanatan da Ya Rasu | Hoto: Jigawa State New Media Office
Asali: Facebook

A cewar wani yanki na sanarwar:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Sanata mai wakiltar Jigawa ta Kudu maso Yamma, Alhaji Mohammad Sabo Nakudu ya kuma cin tikitin takarar Sanata jam'iyyar APC Kudu a maso Yamma.
"Shugaban kwamitin zabe, Alhaji Umar Shehu ya ayyana Sabo a matsayin wanda ya ci zaben fidda gwani da aka gudanar a dakin taron Aminu Kano da ke Dutse a babban birnin jihar Jigawa."

Hakazalika, sanarwar ta ce Sabo ya lashe zaben da aka gudanar ne da kuri'u 375.

Kadan daga tarihinsa

Sabo dai tsohon dan majalisar wakilai ya fara mulki a 2011, an kuma sake zabensa a 2015.

A 2015, Sabo ya samu nasarar lashe zaben sanatan Jigawa ta Kudu maso Yamma a karkashin inuwa jam'iyyar APC, an kuma sake zabensa a 2019.

Kara karanta wannan

Hantar Atiku da PDP Ta Kada Bayan Samun Bayanin Zaman Tinubu da Wike a Landan

Allah Yayi wa Jigon APC kuma 'Dan Takarar Kujerar Sanata, Rasuwa

A wani labarin, jigon jam'iyyar APC a jihar Jigawa kuma 'dan takarar kujerar sanatan Jigawa ta tsakiya, Alhaji Tijjani Ibrahim Gaya, ya kwanta dama.

Fitaccen 'dan siyasan ya rasu ne sakamakon gajeriyar rashin lafiya da yayi fama da ita kamar yadda takardar da gwamnan Jigawa ya fitar ta hannun kwamishinan ayyuka na musamman ta bayyana.

Zabbaben gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya aike da sakon ta'ziyyarsa ga iyalansa da jama'ar Jigawa kan rasuwar 'dan takarar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.