'Idan Tinubu Ya Bani Kuɗi na Shiga APC, Zan Karba': Ministan Buhari
- Tsohon ministan matasa da wasanni a zamanin Muhammadu Buhari Solomon Dalung ya ce yana addu'ar APC ta ba shi kudi domin ya koma cikinta
- Barista Solomon Dalung ya yi zargin cewa a yanzu haka, APC mai mulki na bin wasu daga cikin 'yan adawa ana ba su kudi domn su fice daga jam'iyyunsu
- Tsohon Ministan ya bayyana yadda ya shirya kashe kudin idan har APC ta yanke shawarar ta zo masa da kudi domin ya amince da ita a zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Plateau – Jigo a jam'iyyar ADC, Barista Solomon Dalung, ya bayyana cewa yana addu'ar jam'iyyar APC ta ba shi kudi domin ta jawo hankalinsa ya koma cikinta.
Ya bayyana haka ne bayan ya yi zargin cewa yanzu APC na bibiyar yan adawa, da zarar an ba su kudi sai a ji sun bar jam'iyya suna cewa ba a yi masu adalci ba.

Source: Facebook
A wata hira da ya yi da DCL Hausa, tsohon ministan wasanni a gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi zargin cewa ana shiga jam'iyyar ADC ana sayen 'yan siyasa da kudi domin su sauya sheka.
Dalung na fatan APC ta 'saye' shi
A hirar, Solomon Dalung ya kara da cewa shi ma yana fatan APC za ta kawo masa kudi, yana mai cewa zai karba, amma hakan ba zai sa ya goyi bayan jam'iyyar ba a lokacin zabe.
A cewarsa:
"Kamar mu yanzu, muna sauraransu, muna ta rokon Allah su kawo mana kudi."
Ya ci gaba da cewa:
"Amma kuma idan sun yi haka za mu yi Alhamdulillahi Rabbil Alamin domin mun samu duniya."
Dalung ya ce idan APC ta ba shi kudin, zai yi amfani da su a matsayin kayan yakin neman zabe domin ya fafata da jam'iyyar a lokacin babban zabe.
Zargin Dalung kan Tinubu
A ci gaba da hirar, Solomon Dalung ya yi zargin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na son ya kasance shi kadai ne zai tsaya takara a babban zaben da ke tafe.

Source: Getty Images
Haka kuma ya ce idan 'yan Najeriya ba su daina karbar atamfa, kayan abinci, taliya da sauran abubuwan da ake rabawa domin neman kuri'a, to ana cikin matsala.
Ya kara da cewa dole ne talakawa su rashi tsaye wajen yaki da karban irin wadannan kyaututtuka suna sauya ra'ayinsu da kuma zaben 'azzalumai.'
Dalung ya magantu kan yan majalisa
A baya, kun samu labarin cewa tsohon ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung ya zargi ‘yan majalisa da neman ya biya cin hanci wajensa a shekarun da yake minista a gwamnatin Muhammadu Buhari.
‘Dan siyasar ya yi shekaru kusan hudu a matsayin ministan matasa da wasanni a mulkin Muhammadu Buhari ya yi zargin cewa wasu daga cikin yan majalisa kan nemi a ba su cin hanci a kan batun kasafi/
Barista Solomon Dalung ya kara da cewa domin majalisa ta amince da kasafin kudinsu, wasu daga cikin abokan aikinsa sun rika biyan cin hancin kudin da aka nema daga hannun ministocin.
Asali: Legit.ng

