Dalung Ya Yi Kira ga Uba Sani bayan zuwa Gidan Malamar Islamiyyar da aka Kashe

Dalung Ya Yi Kira ga Uba Sani bayan zuwa Gidan Malamar Islamiyyar da aka Kashe

  • Solomon Dalung ya ziyarci iyalan malama Ummulkhairi Usman Aliyu da jama'a suka suka taru suka kashe a Mararaban Jos
  • Tsohon ministan ya ya ce ya ji zafin yadda miji da 'ya'ya suka rasa abokiyar rayuwa bayan al'umma sun kashe ta bisa zargi na karya
  • Dalung ya matsa wa gwamnatin Kaduna lamba cewa a gurfanar da masu laifi a gaban kotu kuma a yi la'akari da biyan diyya ga iyalanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Kaduna — Tsohon ministan wasanni a Najeriya, Solomon Dalung ya kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan malama Ummulkhairi Usman Aliyu, malamar Islamiyya da aka kashe a Mararaban Jos da ke jihar Kaduna.

A ranar Litinin, 13 ga watan Yuli 2026 ya bayyana cewa ya zauna da mijin malamar, Malam Aliyu Muhammed, wanda ya gaya masa yadda wannan bala'i ya ruguje rayuwarsa.

Solomon Dalung da iyalan malamar Islamiyya
Solomon Dalung da iyalan malamar Islamiyyar da aka kashe a Kaduna. Hoto: Solomon Dalung
Source: Facebook

A sakon da ya wallafa a Facebook, Dalung ya nuna damuwa kan yadda malamar ta fita zuwa karatun addinin Musulunci amma ba ta dawo da rai ba.

Kara karanta wannan

An cafke mata da yaran 'yan bindiga, an saki bidiyo bayan sace daliban Oyo

Dalung a gidan malamar Islamiyya

Yayin ziyara zuwa gidan Malama Ummulkhairi, tsohon ministan ya ce ya yi maraba da matakan da gwamnatin jihar Kaduna ta dauka, ciki har da alkawarin tallafa wa ilimi da walwalar 'ya'yan malamar.

"Jiya na kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan marigayiya Malama Ummulkhairi Usman Aliyu, malamar addinin Musulunci da aka kashe ta a Mararaban Jos, Jihar Kaduna.
"Na zauna tare da mijinta, Malam Aliyu Muhammed, inda na saurare shi yana ba da labarin irin azabar da suka fuskanta, wadda ta sauya rayuwarsa gaba ɗaya.
"Na kuma gana da 'ya'yansu, waɗanda fuskokinsu yanzu ke ɗauke da nauyin wannan mummunan al'amari.
"Akwai bambanci kan mutum ya karanta irin waɗannan labarai a kafafen yaɗa labarai da ya zauna a gidan iyalan da rayuwarsu ta rushe gaba ɗaya saboda shi."
Malamar Islamiyya da iyalanta
Iyalan malamar Islamiyya a hagu, Ita da aka kashe a dama. Hoto: Abdulkarim Hamisu Assuyudi
Source: Facebook

Matakin da gwamnati ta dauka

Sai dai Dalung ya kara da cewa tausaya masu kadai ba zai isar ba, ya yi kira da a gurfanar da duk wanda ke da hannu a mutuwar malamar a gaban kotu.

Kara karanta wannan

'Idan Tinubu ya ba ni kuɗi na shiga APC, zan karba': Ministan Buhari

"Duk da cewa na yaba da matakan da Gwamnatin Jihar Kaduna ta ɗauka, ciki har da alƙawarinta na tallafa wa jin daɗi da ilimin 'ya'yan marigayiyar, adalci bai kamata ya tsaya ga nuna tausayawa kawai ba.
"Dole ne a gurfanar da waɗanda suka aikata wannan laifi tare da tabbatar da an hukunta su yadda doka ta tanada.
"Duk wani abu da ya gaza hakan zai rage darajar rayuwar ɗan Adam tare da ƙarfafa masu tunanin cewa za su iya aikata laifi ba tare da hukunci ba.
"Ina kuma roƙon Gwamnatin Jihar Kaduna cikin girmamawa da ta yi la'akari da duk hanyoyin shari'a da doka ta amince da su domin tabbatar da adalci gare su."

An tallafawa malamar Islamiyya

A wani labarin, mun kawo muku cewa malaman Islamiyya a Najeriya sun yi karo-karo sun hada tallafi ga iyalan malamar da aka kashe a Kaduna.

Legit Hausa ta rahoto cewa iyalan malamar sun karbi tallafin ne ta hannun wani wakilin da aka tura da ke zaune a Maraba Jos a Kaduna.

Wanda ya jagoranci hada kudin a kafafen sada zumunta ya bayyana cewa Legit cewa sun tara kudin ne domin rage wa iyalanta radadin rayuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng