Jerin Kasashe 64 da ba Sa Bukatar Biza domin Shiga Jamus a 2026

Jerin Kasashe 64 da ba Sa Bukatar Biza domin Shiga Jamus a 2026

  • Kasar Jamus za ta ci gaba da bai wa 'yan kasashe 62 damar shiga ba tare da biza ba domin zama na kankanin lokaci a cikin kasar
  • Matafiya za su iya zama har zuwa kwanaki 90 cikin kwanaki 180 domin yawon bude ido, ziyarar iyali ko harkokin kasuwanci ba biza
  • Jamus ta fadi makomar Najeriya da karin wasu kasashen kan ko wasu daga cikin 'yan kasar za su ci gajiyar zama a cikinta ba tare da biza ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Gwamnatin Jamus ta tabbatar da cewa 'yan kasashe da yankuna 62 da ba sa cikin Tarayyar Turai (EU) ko yankin Schengen za su ci gaba da shiga kasar.

Ta ce ta yi wannan sassauci ne ga wadanda ke sha'awar shiga kasar na dan wani lokaci ba tare da biza ba domin zama na kankanin lokaci a shekarar 2026.

Kara karanta wannan

Wike ya tsage gaskiya kan yiwuwar PDP ta iya lashe zaben shugaban ƙasa a 2027

Jamus ta sassauta tsarin biza ga masu shiga kasarta
Shugaban gwamnatin kasar Jamus, Friedrich Merz Hoto: Muhammed Abdullah Kurtar/FADEL SENNA
Source: Getty Images

Jaridar Punch ta wallafa cewa bisa ga bayanan da ke shafin Ma'aikatar Harkokin Wajen Jamus, matafiya daga wadannan kasashe za su iya zama a Jamus na tsawon kwanaki 90 cikin kowane kwanaki 180, idan tafiyarsu ta shafi yawon bude ido, halartar tarurrukan kasuwanci ko ziyarar iyali.

Kasashen da za su shiga Jamus ba biza

A ruwayar jaridar Vanguard, wannan rangwamen ba ya bai wa mutum damar yin aikin da ake biya albashi yayin da yake Jamus.

'Yan kasashen da aka lissafo za su iya shiga Jamus ba tare da an bukaci biza ba idan gajeren zama ne sun hada da:

  1. Albania
  2. Andorra
  3. Antigua da Barbuda
  4. Argentina
  5. Australia
  6. Bahamas
  7. Barbados
  8. Bosnia da Herzegovina
  9. Brazil
  10. Brunei
  11. Canada
  12. Chile
  13. Colombia
  14. Costa Rica
  15. Dominica
  16. El Salvador
  17. Georgia
  18. Grenada
  19. Guatemala
  20. Honduras
  21. Hong Kong (masu fasfo na SAR)
  22. Isra'ila
  23. Japan
  24. Kiribati
  25. Kosovo
  26. Macao (masu fasfo na SAR)
  27. Malaysia
  28. Marshall Islands
  29. Mauritius
  30. Mexico
  31. Micronesia
  32. Moldova
  33. Monaco
  34. Montenegro
  35. New Zealand
  36. North Macedonia
  37. Nicaragua
  38. Palau
  39. Panama
  40. Paraguay
  41. Peru
  42. Saint Kitts da Nevis
  43. Saint Lucia
  44. Saint Vincent da Grenadines
  45. Samoa
  46. San Marino
  47. Serbia
  48. Seychelles
  49. Singapore
  50. Solomon Islands
  51. Koriya ta Kudu
  52. Taiwan (masu fasfo masu lambar katin shaida)
  53. Timor Leste
  54. Tonga
  55. Trinidad da Tobago
  56. Tuvalu
  57. Ukraine
  58. Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE)
  59. Birtaniya
  60. Amurka
  61. Uruguay
  62. Vanuatu
  63. Vatican City
  64. Venezuela

Kara karanta wannan

2027: Fadar shugaban kasa ta yi magana kan barazanar kashe Peter Obi

Kasashen da ke bukatar biza zuwa Jamus

A gefe guda kuma, Jamus ta ce 'yan kasashe da yankuna 102 na fadin duniya na bukatar biza kafin su shiga kasarta.

Najeriya ba za ta mori saukin biza ga masu shiga Jamus ba
Shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Twitter

Najeriya na cikin jerin kasashen nan tare da Afghanistan, Algeria, Angola, Bangladesh, China, Ghana, India, Pakistan, Saudi Arabia, Afirka ta Kudu, Sudan, Turkiyya, Vietnam, Yemen, Zambia, Zimbabwe da sauran kasashe.

Saboda haka, 'yan Najeriya da ke son zuwa Jamus, ko don yawon bude ido, ziyarar iyali ko wata tafiya ta gajeren lokaci, har yanzu dole ne su fara neman biza kafin su tashi zuwa kasar.

Iran ta ba Trump kunya - Jamus

A baya, mun kawo labarin cewa shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz ya yi maganganu game da yakin da aa shafe tsawon lokaci ana fafata shi a tsakanin Iran da Amurka da sra'ila da suka hade kai.

A bayanin da ya yi, Friedrich Merz ya bayyana cewa shugabannin Iran da sojojinta sun ba Amurka kunya, yana cewa Donald Trump ya rasa mafita duk da kalaman da ya rika yi ana tsaka da musayar wuta.

Shugaban gwamnatin Jamus ya ce alamu sun nuna cewa Amurka ba ta da ingantaccen tsari game da yakin, tare da tambayar irin hanyar fita daga rikicin da take da shi bayan ta yi zurfi a cikin lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng