Rana Zafi, Inuwa Ƙuna: Gwamna Fubara Ya Saukar da Kansa, Ya bi Wike da Tinubu

Rana Zafi, Inuwa Ƙuna: Gwamna Fubara Ya Saukar da Kansa, Ya bi Wike da Tinubu

  • Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara, ya bayyana goyon bayansa ga Rainbow Coalition da ke tare da Nyesom Wike.
  • Fubara ya amince da sake marawa Bola Tinubu domin lashe a karo na biyu, tare da marawa Kingsley Chinda baya a takarar gwamna
  • Gwamnan ya ce ya sulhunta da sansanin Nyesom Wike, yana roƙon magoya bayansa su shiga haɗakar Rainbow Coalition domin ci gaban siyasar Ribas cikin lumana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Port Harcourt, Rivers - Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara, ya bayyana a hukumance cewa yana goyon bayan Rainbow Coalition.

Har ila yau, Fubara ya kuma amince da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake yin wa'adi na biyu.

Fubara ya yi mubaya'a ga Tinubu, Wike
Shugaba Bola Tinubu, Nyesom Wike da Siminalayi Fubara. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Sir Siminalayi Fubara.
Source: Facebook

Fubara ya bayyana hakan ne yayin bikin aza harsashin ginin aikin kamfanin Rivien da aka gudanar a Rumuosi, ƙaramar hukumar Obio/Akpor, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Atiku ya sake huro wuta sai Tinubu ya yi murabus

Fubara ya dawo tafiyar Wike, Chinda

Haka kuma ya bayyana Kingsley Chinda a matsayin ɗan takarar gwamna da yake mara wa baya.

Gwamnan ya ce an samu sulhu a Rivers, kuma yanzu yana goyon bayan Rainbow Coalition, wata haɗakar siyasa da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ke jagoranta.

Ya ce ya koma cikin tsohuwar tafiyar siyasa bayan sasanci da aka samu a jihar Rivers tsakaninsu.

Da yake bayyana goyon bayansa ga Tinubu, Fubara ya ce Bola Ahmed Tinubu shi ne shugaban ƙasar Najeriya, kuma shi ne ɗan takarar da suke mara wa baya domin ci gaba da jagorancin ƙasar.

Ya kuma bayyana cewa Kingsley Chinda ne ɗan takarar gwamna da yake goyon baya.

Ya ƙara da cewa duk wanda yake biyayya gare shi ya kamata ya mara wa dukkan 'yan takarar da ke ƙarƙashin Rainbow Coalition baya.

Fubara ya roƙi magoya bayansa su daina jiran samun mukamai ko wasu fa'idodi kafin su shiga haɗakar siyasar. Ya ce babu abin da za su jira domin shi kansa ya riga ya koma cikin iyalinsa na siyasa.

Kara karanta wannan

An tafka babban rashi: Daya daga cikin manyan limaman masallaci ya rasu a Kwara

A cewarsa, lokacin rikici ya wuce, yanzu lokaci ne na zaman lafiya da ci gaba, ya bayyana cewa zaman lafiyar da aka samu zai buɗe ƙofofin sabbin damammaki ga kowa, duk da cewa ana iya rasa wani abu a wani wuri.

Gwamnan ya kuma gargadi magoya bayansa kada su riƙa amfani da sunansa wajen tallafa wa wata ƙungiya ko tafiyar siyasa da ba ta Rainbow Coalition ba.

Ya ce ya bayyana matsayinsa a fili kuma ba ya goyon bayan duk wani abu da zai haifar da rarrabuwar kai.

Ya ce ya riga ya yi abin da ya kamata domin tabbatar da zaman lafiya a Ribas, kuma yanzu burinsa shi ne ci gaba da haɗin kai.

Ya kuma tunatar da jama'a cewa ya janye daga zaɓen fidda gwani na APC a watan Mayun 2026 bayan tuntuba da nazari, bayan sulhun da ya yi da Wike bayan doguwar takaddamar siyasa.

Wike ya magantu kan zaben Tinubu

Mun ba ku labarin cewa Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya yi magana game da sake zaben Bola Tinubu a zaben 2027 da ake tunkara.

Wike ya ce Rivers ba ta da wani zaɓi illa ci gaba da goyon bayan sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a 2027 domin samar da ci gaba.

Ministan ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta bai wa Rivers muƙamai da ayyukan ci gaba fiye da gwamnatocin baya, yana mai kira ga jama'a su yaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.