Mace Ta Samu Shiga Tikitin Takarar Shugaban Kasar Najeriya a Zaben 2027

Mace Ta Samu Shiga Tikitin Takarar Shugaban Kasar Najeriya a Zaben 2027

  • LP ta bayyana Bintu Konto a matsayin 'yar takarar mataimakin shugaban kasa don zaben shekara ta 2027
  • Macen ‘yar siyasar za ta kasance a tikiti tare da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar, Dr. Chibuzo Okereke
  • Hajiya Bintu Konto kwararriya ce a fannin lafiyar jama'a da ayyukan jin kai mai gogewar sama da shekaru 30

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja - Jam’iyyar hamayya ta LP ta gabatar da Hajia Bintu Konto a matsayin ‘yar takara a babban zabe mai zuwa na 2023.

Hajia Bintu Konto za ta yi wa jam’iyyar LP takarar mataimakiyar shugabanr kasa kuma a halin yanzu an tallata wa duniya ita.

Bintu Konto
Bintu Konto da abokin gaminta na takara a LP Hoto: Abia State Labor Party/Amb Sunday Chibuzo Okereke
Source: Facebook

Shugaban ERGAF-AFRICA ya samu takara a LP

A ranar Laraba, Daily Trust ta rahoto cewa an gabatar da Bintu Koko a matsayin abokiyar gamin Chibuzo Sunday Okereke.

Dr. Chibuzo Sunday Okereke wanda malamin jami’a ne a Abuja ya zama ‘dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar LP a watan jiya.

Kara karanta wannan

An gano abin da manyan NDC na Arewa maso Yamma su ka tattauna a Abuja

Jam’iyyar LP mai adawa tana sa ran Bintu Koko za ta taimaka mata a zaben 2027, ta ba ta kwarin guiwar ganin bayan mulkin APC.

An yi wani zama da shugabannin jam’iyyar LP na kasa a lokacin da aka gabatar da ‘yar takarar mataimakiyar shugaban na Najeriya.

Jam'iyyar LP ta tabbatar da takarar Bintu Konto

Nenadi Usman wanda ita ce shugabar LP ta kasa, ta ce an zabi Bintu Konto ne saboda adalcin jam’iyyar da ganin ana tafiya da kowa.

Zaben mace ta nemi kujerar mataimakin shugaban kasa ya yi daidai da tambarin LP mai dauke da hoton uba, uwa da kuma ‘dansu.

Tsohuwar sanatar ta Kaduna ta ce jam'iyyar LP ta yi imani da ba mata dama irin na maza a siyasa.

A game da ‘yar takarar tasu kuwa, Nenedi ta ce shugaba ce mai nagarta da ta yi fice wajen ayyuka na taimaka ‘dan adam a Najeriya.

Idan ta kai labari, shugabar jam’iyyar LP tana ganin Konto za ta kawo cigaba mai ma’ana wajen shugabanci tar da Chibuzo Okereke.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya hango abin da zai hana Tinubu cin zaɓe, ya ba shi mafita

Bintu Konto
Bintu Konto da ta samu takarar mataimakin shugaban kasa a LP Hoto: @AbiaStateLaborParty
Source: Twitter

Jaridar Daily Post ta ce Gwamnan jihar Abia sai da ya samu yabo wajen shugabar jam’iyyar yayin gabatar da ‘yar takarar a birnin Abuja.

Nenedi ta yi misali da aikin gwamnatin Alex Otti a Abia, take cewa abin da za a gani kenan idan jam'iyyar LP ta karbi mulkin kasa a 2027.

Shi ma Okereke ya ji dadin yadda aka dauko masa Hajiya Konto, ya yi farin cikin aiki da ita.

‘Dan takarar na shugaban kasa yake cewa dole akwai rawar da mata za su taka, ya ce yin mulki babu su tamkar tafi ne da hannu guda.

Peter Obi ya hadu da Patrick Egloff

Ana da labarin maganar da aka yi game da Arewa maso yammacin Najeriya a zaman Peter Obi da Jakadan kasar Switzerland

Peter Obi ya gana da Jakadan Switzerland a Najeriya, Patrick Egloff, an yi zancen yadda za a taimaki mutanen kasar nan.

'Dan takarar shugaban kasar na NDC ya gode wa yadda kasar Turan ta taimaka wa Najeriya da gudumuwar da za a iya badawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng