An Samu Bidiyon Babban Mai Ɗaukar Bidiyon Boko Haram da Sojoji Suka Kashe a Borno
- Boko Haram ta tabbatar da mutuwar babban mai ɗaukar bidiyonta, Abu Salim al-Barnawi, bayan sojojin Najeriya sun hallaka shi a wani hari da ya ci tura
- Rundunar Operation Hadin Kai ta ce an kashe wasu manyan mayaƙa tare da Abu Salim, yayin da aka kwato kyamara da sauran kayan aiki
- Sojoji sun ce mutuwar Abu Salim ta raunana ƙarfin yaɗa farfagandar Boko Haram da kuma ƙoƙarin ƙungiyar na jan hankalin sababbin mayaƙa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.
Borno - Ƙungiyar Boko Haram ta fitar da sanarwar rasuwar ɗaya daga cikin manyan masu ɗaukar bidiyo da kyamara na ƙungiyar, Abu Salim al-Barnawi, wanda sojojin Najeriya suka hallaka yayin wani yunƙurin kai hari kan sansanin soji.
Wani faifan bidiyo mai tsawon mintuna uku da daƙiƙa uku da aka samu ranar Laraba ya nuna marigayin yana ɗaukar bidiyo tare da shiga wasu hare-haren da ƙungiyar ta gudanar.

Source: Twitter
Rundunar soji ta yi karin bayani
Jami'in yaɗa bayanai na Operation Hadin Kai a yankin Arewa maso Gabas, Kyaftin Muhammed Goni, ya ce Abu Salim ya taba jagorantar hare-hare zuwa ƙasar Kamaru kafin daga bisani ya koma sashen yaɗa labarai na ƙungiyar, in ji rahoton Punch.
A cewar Goni, ƙungiyar Boko Haram ta fitar da sanarwar mutuwarsa ne bayan sojojin Najeriya sun kashe shi a wani hari da 'yan ta'addan suka kai kan sansanin soji.
Ayyukan da yake yi wa Boko Haram
Rundunar ta bayyana cewa Abu Salim al-Barnawi ne ke ɗaukar hotuna da bidiyon hare-haren ƙungiyar, tare da samar da kayan farfaganda da ake amfani da su wajen yaudarar jama'a da kuma jan hankalin sababbin mayaƙa.
Goni ya ce:
"Kashe Abu Salim da tawagar yaɗa labarai ta ISWAP a lokacin harin da ya ci tura a Cross Kauwa ranar 12 ga Yulin 2026 ya nuna irin nasarorin da Operation Hadin Kai ke samu."
Wasu manyan mayaƙa sun mutu
Jaridar Daily Trust ta rahoto rundunar ta ce a harin, sojoji sun kashe wasu fitattun mayaƙa ciki har da wani ɗan ƙasar Siriya da kuma wani kwamandan ƙungiyar mai suna Aliyu Zabarmari.
Ta kuma bayyana cewa wani ɗan ƙasar Larabawa da ke yaƙi tare da ƙungiyar har yanzu ba a san inda yake ba, yayin da wasu manyan mayaƙa suka tsere da raunuka masu tsanani.

Source: Twitter
Sojoji: Mun raunana ƙarfin Boko Haram
A cewar Operation Hadin Kai, mutuwar Abu Salim wani babban koma baya ne ga Boko Haram da ISWAP, musamman a bangaren yaɗa farfaganda.
Rundunar ta jaddada cewa hare-haren da take ci gaba da kai wa 'yan ta'addan na ci gaba da haifar da sakamako mai kyau wajen rage ƙarfin ƙungiyoyin.
Kalli bidiyon da Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X a kasa:
Sojoji sun gano bayanai kan 'yan ta'adda
Tun da fari, mun ruwaito cewa, sojoji sun ce sun kashe mai ɗaukar bidiyon ISWAP tare da ƙwato kyamara da ke dauke da wasu muhimman bayanai game da 'yan ta'addan.
Binciken farko ya ba sojoji damar gano bayanan wasu ƙwararrun ƴan ta'adda daga ƙasashen waje da le taimaka wa kungiyar ISWAP.
Rundunar ta ce an kashe mai daukar bidiyon da tarwatsa lagon ISWAP ne a harin da suka kai dpn sace magungunan cutar kwalara.
Asali: Legit.ng


