Tinubu Ya Girgiza da Babban Malami a Najeriya, Sheikh Tijani Shehu Ya Rasu
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nuna alhininsa game da rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Imam Tijani Olubodun Shehu Gbajabiamila
- Tinubu ya yaba da irin gudunmawar da marigayin ya bayar a matsayin jagoran al'umma da kuma kokarinsa na karfafa zaman lafiya tsakanin al'umma
- Shugaban kasar ya mika sakon ta'aziya ga iyalan marigayin, gwamnatin jihar Legas, da daukacin dalibansa da masoyansa a fadin duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna alhininsa kan rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci kuma jagoran al'umma, Sheikh Imam Tijani Olubodun Shehu Gbajabiamila, wanda ya rasu kwanan nan.
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa yana ya yaba da muhimmiyar gudunmawar da marigayin ya bayar ga al'umma a matsayinsa na shugaban addini da aka girmama.

Source: Facebook
A cewar fadar shugaban kasa, shugaba Bola Tinubu ya samu damar sanin malamin da amfana daga jagorancinsa lokacin da yake gwamnan jihar Legas da kuma kafin wannan lokacin.
Gudunmawar Imam Gbajabiamila
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa marigayi Imam Gbajabiamila ya kasance jagora mai cike da hikima, inda ya gudanar da aiyukan addini da wa'azi gami da ba da shawarwari na rayuwa ga al'umma.
Tinubu ya sanar da cewa iliminsa na Al-Kur'ani da koyarwar Musulunci ya kasance mai zurfi, sannan ya kasance mai karfafa gwiwar matasa wajen neman ilimi da ciyar da kai gaba.
Hakanan, shugaban kasar ya ce malamin ya taka rawa wajen shiga tsakanin mutane da karfafa zaman lafiya tsakanin mabiya addinai daban-daban.
Sakon ta'aziyyar Tinubu
Rahoton da Punch ta walllafa ya nuna cewa shugaban kasar ya bayyana a cikin sanarwar ta'aziyyar cewa malamin ya kasance jagora wajen hada kan al'umma.
Bola Tinubu ya ce:
"Ayyukan Imam Gbajabiamila sun wuce kawai matsayinsa na jagoran addini; ya kasance mai hada kan mutane ta hanyar amfani da iliminsa da hikimarsa."
Shugaba Bola Tinubu ya kara da cewa:
"Rasuwarsa babbar rashin ce ga jiharmu da ma kasa baki daya, amma aikin da ya yi zai ci gaba da kasancewa jagora da karfafa mu."

Source: Original
A tsawon rayuwarsa, marigayin ya rike mukamai daban-daban ciki har da darakta na al'amuran Musulunci a kungiyar matasan Zumuratul Islamiyyah da kuma Mataimakin Shugaban Majalisar Limamai da Alfe-alfe na shiyyar Legas.
Tuni dai aka yi jana'izar malamin bisa yadda addinin Musulunci ya koyar tare da 'yan uwansa malamai da dalibai daga yankuna daban-daban na Legas.
Tinubu ya nada mukamai
A wani labarin kuma, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya amince da nada mutane 26 a kwamitocin gudanarwa na hukumomin gwamnatin tarayya 10.
Nadin, wanda aka sanar ta hanyar sanarwa daga mai taimaka wa shugaban kasa kan tsare-tsare da yada labarai, Bayo Onanuga, ya fara aiki ne nan take.
Daga cikin wadanda aka nada har da tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, wanda aka nada shugaban hukumar samar da wutar lantarki a karkara (REA), da kuma Junaid Bindawa a matsayin shugaban hukumar albashi.
Asali: Legit.ng

