Trump Ya Amince da Yarjejeniyar Makamashin Nukiliya da Saudiyya

Trump Ya Amince da Yarjejeniyar Makamashin Nukiliya da Saudiyya

  • Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya amince da wata babbar yarjejeniya ta makamashin nukiliya da kasar Saudiyya ana tsaka da yakin Iran
  • Yarjejeniyar za ta ba Saudiyya damar kafa shirin nukiliya na farar hula na tsawon shekaru 30 duk da cewa Amurka na adawa da amincewa Iran ta mallaki makamashin
  • Ana sa ran kamfanonin Amurka za su jagoranci aikin, yayin da za a takaita damar sauran kasashen waje na yin aikin samar da makamashin nukiliya a yankunansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar Saudia – Shugaban Amurka, Donald Trump, ya amince da wata muhimmiyar yarjejeniya da Masarautar Saudiyya da za ta ba kasar damar kafa shirin makamashin nukiliya na farar hula.

Rahotanni sun bayyana cewa yarjejeniyar, wadda gwamnatin Trump ta amince da ita a hukumance, za ta kasance na tsawon shekaru 30.

Kara karanta wannan

'Da sauran rina a kaba': Trump ya fadi abin da ya rage tsakaninsa da Iran

Amurka ta kulla yarjejeniya da Trump
Shugaban Amurka Donald Trump tare da Mohammed Bin Salman Hoto: Chip Somodevilla/Getty Images
Source: Getty Images

Kafar Wall Streat Journal ta kawo labarin cewa haka kuma yarjejeniyar ta bai wa kamfanonin Amurka muhimmiyar dama wajen gina cibiyoyin makamashin nukiliya na Saudiyya.

Amurka da Saudiyya sun kulla yarjejeniya

AP ta kawo labarin cewa yarjejeniyar na iya bude kofar bai wa Saudiyya damar tace sinadarin uranium a cikin kasarta, matakin da ake ganin zai taimaka wajen bunkasa shirin makamashin nukiliyar kasar.

A cewar jami'an gwamnatin Amurka, ana hasashen yarjejeniyar za ta kai darajar biliyoyin Daloli, lamarin da zai samar da gagarumar dama ga kamfanonin Amurka da ke harkar makamashi da gine-ginen nukiliya.

Sai dai kuma, ana sa ran matakin zai jawo damuwa daga wasu kasashe da masana harkokin tsaro, musamman kan yiwuwar yaduwar fasahar nukiliya a yankin Gabas ta Tsakiya

Manufar yarjejeniyar Amurka da Saudiyya

Rahoton ya nuna cewa daya daga cikin manufofin yarjejeniyar ita ce tabbatar da cewa kamfanonin Amurka ne suka mamaye manyan ayyukan gina cibiyoyin nukiliyar Saudiyya.

Kara karanta wannan

Kasafin kudin 2026: Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu da boye Naira tiriliyan 12.8

Sai dai duk da wannan kaka-gida da Amurka ke shirin yi wajen aiwatar da aiki, an bayar dama ga sauran kasashen waje su shiga wannan aiki.

Amurka ta saka jami'anta a gaba wajen taimakon Saudiyya da makamashin
Shugaban kasar Amurka Donald Trump Hoto: Donald J Trump
Source: Getty Images

Idan aka aiwatar da yarjejeniyar gaba daya, za ta kasance daya daga cikin manyan yarjejeniyoyin hadin gwiwa tsakanin Amurka da Saudiyya a fannin makamashi.

Kuma wannan na iya kara karfafa alakar kasashen biyu a bangaren tattalin arziki da fasaha, duk da yakin d ake ci gaba da gwabzawa tsakanin Amurka da Iran a Gabas ta Tsakiya.

Amurka ta yi awon gaba da sinadarin nukiliya

A baya, kun ji cewa sojoji sun yi wa motar jigilar uranium mai hatsari rakiya zuwa tashar jirgin ruwa domin kai wa kasar Amurka cikin tsauraran matakan tsaro na musamman domin bayar da kariya.

Hukumar IAEA da ke sanya idanu a kan harkokin makamashin nukiliya a duniya ta ce aikin kwashe uranium ɗin haɗin gwiwa ne tsakanin Venezuela, Amurka da wasu hukumomin duniya masu kula tsaro.

Masana sun bayyana cewa uranium ɗin na iya zama barazana idan ya shiga hannun ƙasashe ko ƙungiyoyin da ke neman makaman nukiliya yayin da Amurka ke kokarin yin uwa da makarbiya kan wadanda za su mallaka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng