Gwamna Sule Ya Fatattaki Kwamishinoni 6, Ya Yi Sauye Sauyen Gwamnati Gabanin 2027
- Gwamna Abdullahi Sule ya sallami kwamishinoni shida a wani karamin sauyi da ya ce zai kara inganta aikin gwamnati kafin zaben 2027
- Gwamnan ya musanta jita-jitar rusa majalisar zartarwa gaba daya, yana mai cewa sauye-sauyen da aka yi na dabarun gudanar da mulki ne
- Sakataren gwamnatin Nasarawa ya ce za a sanar da sabbin kwamishinoni bayan kammala dukkan matakan da suka dace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.
Nasarawa - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya amince da yin wani karamin sauyi a majalisar zartarwar jihar, inda ya sauke kwamishinoni shida daga mukamansu.
Gwamnatin Nasarawa ta bayyana cewa wannan matakin zai taimaka wajen kara inganta aikin gwamnati gabanin babban zaben shekarar 2027.

Source: Twitter
Gwamna ya musanta jita-jitar rusa SEC
An sanar da matakin ne ranar Talata bayan kammala taro na biyar na majalisar zartarwar jihar a shekarar 2026, wanda aka gudanar a gidan gwamnati da ke Lafiya karkashin jagorancin gwamnan, in ji rahoton Channels TV.
Da yake jawabi ga mambobin majalisar, Gwamna Sule ya musanta rahotannin da ke yawo cewa gwamnatinsa na shirin rusa majalisar zartarwa baki daya.
Ya bayyana cewa gwamnati za ta yi ne kawai wasu sauye-sauye na dabaru domin kara karfafa shugabanci da kuma shirya matakin gaba na aiwatar da manufofinta.
Gwamnan ya kuma yabawa mambobin majalisar bisa gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban jihar tun lokacin da suka fara aiki.
Gwamna ya taya Nasarawa Amazons murna
Har ila yau, Gwamna Sule ya taya kungiyar kwallon kafa ta mata ta Nasarawa Amazons murnar lashe kofin President Federation Cup (PFC) na shekarar 2026.
Ya ce nasarar wata babbar alfahari ce ga jihar Nasarawa.
Ma'aikatun da sauye-sauye ya shafa
Da yake yi wa manema labarai karin bayani bayan taron, Sakataren Gwamnatin Jihar Nasarawa, Shuaibu Magaji (SAN), ya ce an sauke kwamishinoni shida domin samar da gurbin nada sababbin mutane.
Ma'aikatun da abin ya shafa sun hada da:
- Ma'aikatar Tsaro da Harkokin Musamman
- Ma'aikatar Harkokin Mata da Ci gaban Al'umma
- Ma'aikatar Ayyuka, Sufuri da Gidaje
- Ma'aikatar Kimiyya da Fasaha
- Ma'aikatar Yaɗa Labarai, Al'adu da Yawon Bude Ido
- Ma'aikatar Filaye da Binciken Kasa

Kara karanta wannan
'Na shirya a yi tonon silili': Pantami ya bugi kirji kan abubuwan alheri da ya yi

Source: Facebook
Bayani kan nadin sababbin kwamishinoni
Magaji ya gode wa kwamishinonin da aka sauke bisa irin hidimar da suka yi wa jihar, yana mai cewa gwamnan ya yaba da gudunmawar da suka bayar a lokacin da suke kan mukamansu.
Ya kara da cewa za a bayyana sunayen sabbin kwamishinoni bayan kammala dukkan matakan da suka dace, kamar yadda Punch ta ruwaito.
A cewarsa, ana sa ran wannan sauyin zai taimaka wajen kara karfafa aiwatar da ayyukan gwamnati da inganta isar da ayyuka ga al'umma a shekarun da suka rage na wa'adin Gwamna Sule.
Gwamna Sule ya yabi Shugaba Tinubu
A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamna Abdullahi Sule na Nasarawa ya ce Shugaba Bola Tinubu ya fi sauran masu neman takarar shugaban ƙasa.
Gwamna Abdullahi Sule ya ce banbancin da ke tsakanin Tinubu da abokan hamayyarsa ya yi kama da dare da rana.
Gwamnann jihar ta Nasarawa ya bayyana ayyukan raya ƙasa, ilimi da ci gaban kasuwar hannayen jari a matsayin nasarorin gwamnatin Tinubu.
Asali: Legit.ng
