Wasu Ƴan Siyasa na Daf da Rasa Tikitinsu, INEC Ta Yi Watsi da Wasu Zaben Fitar da Gwani

Wasu Ƴan Siyasa na Daf da Rasa Tikitinsu, INEC Ta Yi Watsi da Wasu Zaben Fitar da Gwani

  • Hukumar zaɓe mai zaman kanta, INEC za ta sa kafar wando daya da wasu jam’iyyun siyasa game da gudanar da zaɓen fitar da gwani
  • INEC ta bayyana cewa duk wani zaɓen fitar da gwani da aka gudanar ƙarshen watan Mayun 2026 ba za ta amince da shi ba
  • Kwamishinan INEC, Mohammed Kudu Haruna ya ce jam’iyyu su ci gaba da bin dokokin Zaɓe na 2026 yayin da ake jiran hukuncin daukaka ƙara a kotu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta gargadi jam’iyyun siyasa game da zaɓen fitar da gwani a Najeriya.

Hukumar ta bayyana cewa duk wani zaɓen fitar da gwani da aka gudanar bayan wa’adin ranar 30 ga Mayu 2026 da ta gindaya ba za ta amince da shi ba.

Kara karanta wannan

Hashim: Dan takarar shugaban ƙasa ya faɗi yadda zai raguzo da farashin Dala idan ya ci zabe

INEC ta yi gargadi game da zaɓen fitar da gwani
Shugaban hukumar INEC a Najeriya, Joash Amupitan. Hoto: INEC Nigeria.
Source: Twitter

Shugaban kwamitin yaɗa bayanai da ilimantar da masu zaɓe, Mohammed Kudu Haruna, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da jaridar Punch.

INEC ta ja kunnen jam'iyyu kan bin doka

Mohammed Haruna ya shawarci jam’iyyun siyasa da su ci gaba da bin tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2026 har sai an kammala sauraron ƙarar da INEC ta ɗaukaka a Kotun Ɗaukaka Ƙara.

Haruna ya bayyana cewa duk wani zaɓen fitar da gwani da aka gudanar bayan ranar 30 ga Mayu zai kasance marar inganci muddin kotun ɗaukaka ƙara ba ta soke hukuncin da aka yanke ba.

Ya ce a halin yanzu ya dace jam’iyyun siyasa su ci gaba da yin aiki bisa ga dokokin da ke aiki domin kaucewa matsalolin shari’a.

Duk da hukuncin kotu, INEC ta bokare, ta gargadi ƴan siyasa kan zaben fitar da gwani
Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, Joash Amupitan. Hoto: INEC Nigeria.
Source: Facebook

Umarnin INEC ga jam'iyyun siyasa a Najeriya

Hakazalika hukumar ta umarci jam’iyyun siyasa su bi sauran jadawalin ayyukan zaɓe da ta fitar domin shirye-shiryen zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Matashin da ya kirkiri muryar Tinubu ta bogi ya shiga komar ƴan sanda

A wani hukunci daban, Mai Shari’a James Omotosho ya tabbatar da cewa INEC tana da ikon tsara da sauya jadawalin ayyukan zaɓe.

Sai dai ya jaddada cewa dole ne hukumar ta yi amfani da wannan iko ne cikin iyakokin wa’adin da Dokar Zaɓe ta 2026 ta tanada.

A halin da ake ciki, kwamitin sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen fitar da gwani na ADC a Kaduna ya umarci sake gudanar da zaɓe a wasu mazaɓu.

Shugaban kwamitin, Dakta Muhammed Fagge, ya ce sun binciki ƙorafe-ƙorafe da hujjoji kafin yanke hukuncin sake gudanar da wasu zaɓukan.

Ya bayyana cewa an gano kura-kurai, take dokoki da kuma wasu zarge-zargen magudi a wasu daga cikin zaɓen fitar da gwanin.

Jadawalin zabe: INEC ta daukaka kara

Mun ba ku labarin cewa hukumar INEC mai zaman kanta ta daukaka kara kan hukuncin da ya soke duka wa'adin da ta sanya wa jam'iyyun siyasa a jadawalin zabe.

Lauyan INEC, Alex Izinyon (SAN), wanda ya shigar da kara a gaban kotun daukaka kara ta Abuja, ya nemi a jingine hukuncin da babbar kotun tarayya ta yi.

A makon jiya ne, kotun tarayya ta soke wasu daga cikin tsare-tsaren INEC, ciki har da wa'adin zaben fitar da gwani da na mika sunayen 'yan takara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.