Malamin Addini Ya Yi Hasashe kan Makomar Tinubu a Zaben 2027, "Zai Sha Mamaki"

Malamin Addini Ya Yi Hasashe kan Makomar Tinubu a Zaben 2027, "Zai Sha Mamaki"

  • Proohet David Kingleo Elijah ya yi hasashen murabus ɗin wasu daga cikin Ministocim Shugaba Bola Tinubu, gabannin zaɓubbukan shekarar 2027
  • Malamin addinin Kiristan ya tabbatar da cewa abin da zai faru zai kasance kamar abin mamaki ga Shugaba Tinubu
  • Manyan 'yan siyasar da ake zaton za su fafata a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 sun haɗa da Tinubu na jam'iyyar APC, Atiku Abubakar na ADC da kuma Peter Obi na NDC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Ojo, jihar Legas - Prophet David Kingleo Elijah ya fitar da wani sabon sako, inda ya yi hasashe kan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.

Malamin addinin ya ce Shugaba Bola Tinubu ba zai samu hanyar samun nasara a zaɓubbukan shekarar 2027 cikin sauki ba.

Malamin addini ya yi hasashe kan Tinubu
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a ofis Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

An yi hasashe kan Tinubu

Prophet Elijah, babban fasto na cocin Glorious Mount of Possibility Church da ke Legas, ya yi wannan hasashen ne a cikin wani bidiyo da aka sanya a YouTube.

Kara karanta wannan

Atiku ya sake dura kan Tinubu saboda matsalar rashin tsaro a Najeriya

Bidiyon yana ta samun karɓuwa a dandalin sada zumunta na intanet, inda aka kalle shi fiye da sau 6,400 tun lokacin da aka wallafa shi ranar Laraba, 20 ga watan Mayu, 2026.

Malamin addinin ya hango nakasu ga APC

A cikin bidiyon, Prophet Elijah, wanda ya bayyana kansa a matsayin “Babban bawan Allah,” ya ce wasu na-kusa da Tinubu za su “ba shi kunya” a zaɓubbukan shekarar 2027.

Ya kuma bayyana cewa wasu ministoci za su yi murabus daga majalisar ministocin Tinubu, abin da ya ce zai iya girgiza shugaban ƙasar.

“A shekarar 2027, mutanen da shugaban ƙasar zai dogara da su za su ba shi kunya. Kuma mutanen da zai dogara da su ɗin za su ba shi kunya a daidai mintunan ƙarshe kuma su juya masa baya."
"Za mu ga ƙarin ministoci suna yin murabus. Ministoci za su yi murabus. Wasu mutane daga gwamnati za su sauya sheka daga jam'iyyar da suke ciki. Ina magana ne a kan jam'iyyar APC mai mulki."
'Wasu gwamnoni za su sauya sheka kuma su koma wata daban. Abin da zai faru zai kasance kamar abin mamaki ga Shugaba Tinubu.”

Kara karanta wannan

Bayan sukar APC, ADC da NDC, Babachir ya fadi wanda zai zaba a 2027

- Prophet David Kingleo Elijah

Fasto ya yi hasashe kan Tinubu
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Yayin da 'yan Najeriya ke jiran zaɓukan shekarar 2027, an rawaito cewa rajistattun jam'iyyun siyasa 22 sun shiga takarar, inda aka tsayar da aƙalla 'yan takarar shugaban ƙasa 11, kamar yadda jaridar The Guardian ta bayyana.

Shugaba Tinubu ya nada mamba a NDDC

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya zabi Dr. Zainab marwa domin zama mamba a majalisar gudanarwa ta hukumar kula da ci gaban Niger Delta (NDDC).

Shugaba Tinubu ya miƙa sunan Dr. Zainab Marwa ga Majalisar dattawa domin tabbatar da ita a matsayin mamba mai wakiltar shiyyar Arewa maso Gabas.

Naɗin da Shugaba Tinubu ya yi mata, an yi shi ne da nufin cike gurbin da aka samu sakamakon murabus ɗin tsohon mamban hukumar da ya gabata, Hon. Abdulrazak Namdas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng