Jam'iyyar NDC Ta Jawo Kabiru Marafa, Ta ba Shi Tikitin Takarar Gwamnan Zamfara a 2027
- Jam'iyyar NDC ta ayyana Sanata Kabiru Marafa a matsayin dan takarar gwamnan jihar Zamfara a babban zaben 2027 mai zuwa
- Tsohon sanatan Zamfara ta Tsakiya ya samu tikitin NDC ne ta hanyar tsarin masalaha, inda shugabanni da magoya baya suka amince da shi
- Sanata Marafa ya gode wa shugabanni da ‘ya’yan jam’iyyar NDC bisa amincewa da suka nuna masa har ya samu wannan dama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara, Nigeria - Tsohon sanatan Zamfara ta Tsakiya, Sanata Kabiru Garba Marafa, ya zama ɗan takarar gwamna na jam’iyyar NDC a jihar Zamfara gabanin zaɓen shekarar 2027.
Sanata Marafa ya samu tikitin jam’iyyar ne ta hanyar maslaha bayan kasancewarsa shi kaɗai ya nemi takarar gwamna a ƙarƙashin inwuar NDC a jihar.

Source: Twitter
NDC ta ba Kabiru Marafa takarar gwamna
Channels tv ta ruwaito cewa an tabbatar masa da takara ne a wani taro da aka gudanar a Gusau, babban birnin jihar Zamfara.
Shugabannin jam’iyyar NDC da magoya baya sun hallara domin shaida yadda aka amince da shi a matsayin ɗan takarar gwamna a zaben 2027.
Shugaban kwamitin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar NDC, Aminu Jelani, shi ne ya sanar da Marafa a matsayin dan takarar gwamna a hukumance.
Jelani ya bayyana cewa tsarin da aka bi ya kasance cikin lumana da fahimtar juna, yana mai cewa jam’iyyar ta amince da Marafa ne saboda gogewarsa a siyasa da kuma irin gudunmawar da ya bayar a harkokin shugabanci.
Ya ƙara da cewa NDC na da yakinin cewa Sanata Marafa zai iya jagorantar jihar Zamfara zuwa sabon mataki na ci gaba idan aka zaɓe shi gwamna.
Marafa ya gode wa magoya baya
Da yake jawabi jim kaɗan bayan ayyana shi a matsayin ɗan takarar gwamna, Sanata Kabiru Marafa ya gode wa shugabanni da ‘ya’yan jam’iyyar bisa amincewa da suka nuna masa.
Ya bayyana cewa wannan dama da aka ba shi babban nauyi ne wanda zai yi iya ƙoƙarinsa wajen ganin ya sauke shi yadda ya kamata.

Kara karanta wannan
'Dan marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya samu tikitin takarar gwamna a zaben 2027
Marafa ya gano tushen matsalolin Zamfara
Marafa ya ce babban abin da ya jawo matsalolin da jihar Zamfara ke fama da su shi ne cin hanci da rashawa, yana mai cewa idan aka zaɓe shi gwamna zai tabbatar da gaskiya da riƙon amana wajen tafiyar da dukiyar jama’a.

Source: Original
A cewarsa, rashin gaskiya wajen tafiyar da mulki ne ya haddasa matsaloli da dama a jihar Zamfara musamman a bangaren tsaro, ci gaba da walwalar jama’a, kamar yadda Leadership ta kawo.
Tsohon sanatan ya yi alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta fifita gaskiya wajen kashe kuɗaɗen gwamnati tare da tabbatar da cewa albarkatun jihar sun amfani al’umma baki ɗaya.
Aisha Yesufu ta hakura da takara a NDC
A wani rahoton, kun ji cewa yar gwagwarmayar kare hakkin bil'adama, Aisha Yesufu ta janye daga neman takarar sanata mai wakiltar Abuja a Majalisar dattawa.
Ta ce jam’iyyar NDC ta yanke shawarar ba za ta gudanar da zaben fitar da gwani na kujerar Sanata a Abuja ba, wanda hakan ya sa ta janye daga shiga tseren neman tikiti.
Mai fafutukar ta bukaci magoya bayanta da su ci gaba da nuna hakuri tare da mayar da hankali kan abin da ta bayyana a matsayin babban burin ceto Najeriya a zaben shugaban kasa na 2027.
Asali: Legit.ng
