'Idan na Zama Shugaban Ƙasa,' Makinde Ya Fadi Ayyukan da Zai Yi wa Najeriya
- Tsohon gwamnan Oyo, Seyi Makinde ya amince da takarar shugaban ƙasa ta jam’iyyar APM a zaɓen shekarar 2027
- Ya ce tattalin arziki zai bunƙasa ta hanyar gaskiya da tsari, tare da sauya fasalin NNPC domin tabbatar da albarkatun mai sun amfani talakawan ƙasa
- Gwamnan Bauchi Bala Mohammed ya mara masa baya ta hannun mataimakinsa, yana bayyana Makinde a matsayin jagoran da Najeriya ke buƙata a wannan lokaci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Ibadan, Oyo - Dan takarar shugaban kasa a APM, Seyi Makinde ya yi magana kan irin mulkin da zai yi a Najeriya.
Makinde ya shiga takarar shugaban ƙasa ta 2027 a hukumance bayan ya amince da tsayawa takara a ƙarƙashin jam’iyyar APM.

Source: Twitter
Taron ya gudana a Ibadan tare da halartar shugabannin siyasa da wakilai daga sassa daban-daban, cewar The Guardian.

Kara karanta wannan
Gwamna Makinde ya samu tikitin takara, zai gwabza da Atiku da Tinubu a zaben 2027
Manufar Makinde kan jagoranci a Najeriya
A jawabinsa na karɓar takara, Makinde ya ce manufarsa ba ta samo asali daga son rai ba, sai dai daga buƙatar dawo da fata da sake gina amincewar jama'a.
Ya bayyana cewa tattalin arzikin ƙasar zai iya farfaɗowa ta hanyar gaskiya, da'a da gyare-gyare masu amfani.
A cewarsa, gyare-gyaren da yake magana a kai za su shafi rayuwar talakawa kai tsaye, ya yi alƙawarin yin cikakken gyara a ɓangaren mai da iskar gas.
Ya ce ya kamata 'yan Najeriya su amfana da albarkatun ƙasar kamar yadda ake samu a sauran ƙasashen da ke da irin waɗannan albarkatu.
Ya kuma ce dole ne a sake fasalin NNPC ta zama hukuma mai sauƙin gudanarwa, inganci da cin gashin kai ta fuskar kasuwanci.

Source: Twitter
Makinde ya yi alkawari game da abinci
Dangane da wadatar abinci, Seyi Makinde ya ce bai dace ƙasa mai yalwar albarkatu ta kasance tana fama da yunwa ba.

Kara karanta wannan
Peter Obi ko Kwankwaso: NDC ta shirya tsaida 'dan takarar shugaban kasa a zaben 2027
Ya ce miliyoyin mutane da ke kwanciya da yunwa a ƙasa abu ne da bai kamata ya ci gaba ba.
Dan takarar ya jaddada cewa kamfen ɗinsa zai mayar da hankali kan ƙwarewa da mafita maimakon alkawuran banza.
Ya ce ba zai yi alƙawarin mu'ujizai ba, amma zai samar da shugabanci mai sauraro da aiki, cewar rahoton Punch.
Tun da farko, gwamnan Bauchi Bala Mohammed, ta hannun mataimakinsa Mohammed Auwal Jatau, ya jagoranci tawaga daga Arewa maso Gabas wajen bayyana goyon baya ga takarar Makinde.
Tawagar ta bayyana Makinde a matsayin jagoran da Najeriya ke buƙata a wannan muhimmin lokaci na tarihinta.
An roki gwamna ya ba Musulmi mulki
An ji cewa kungiyar Musulmi a jihar Oyo ta kosa da kalar mulkin da ake yi musamman duba da mabambantan addinai da ake da su a jihar Musulmin sun bukaci.
Gwamna Seyi Makinde ya nuna adalci da daidaito ta hanyar mara wa dan takarar Musulmi baya a zaben gwamnan PDP.
Kungiyar ta tuna yadda gwamnan ya nuna kusanci da Musulmi a baya, ciki har da gina masallaci da taimaka wa masu a zuwa Hajji da Umrah.
Asali: Legit.ng