NNPP Ta Hakura da Tsayar da Dan Takarar Shugaban Kasa a 2027, Ta Bayyana Dalili

NNPP Ta Hakura da Tsayar da Dan Takarar Shugaban Kasa a 2027, Ta Bayyana Dalili

  • Jam’iyyar NNPP ta bayyana cewa ba za ta tsayar da dan takarar shugaban kasa a zaben 2027 ba, tana mai fifita hadaka da wasu jam’iyyu
  • Shugaban jam’iyyar na kasa, Bala Mohammed, ya ce Najeriya na bukatar hadin kai domin samun sahihin dan takarar da zai magance matsalolin kasa
  • NNPP ta ce za ta tantance ‘yan takarar da sauran jam’iyyu suka fitar kafin yanke hukuncin jam’iyyar da za ta kulla kawance da ita don tunkarar 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Jam’iyyar NNPP ta sanar da cewa ba za ta fitar da dan takarar shugaban kasa a babban zaben shekarar 2027 ba.

Maimakon haka, jam’iyyar ta ce za ta mayar da hankali wajen nazarin yiwuwar kulla kawance da wasu jam’iyyun siyasa domin tallafa wa dan takarar da ta ga ya cancanta.

Kara karanta wannan

2027: Mace ta zama yar takarar shugabar kasa a YPP, za ta kara da su Tinubu, Obi

NNPP ta ce ba za ta tsayar da dan takarar shugaban kasa a 2027 ba
Shugaban NNPP na kasa,Bala Mohammed yana jawabi a taron jam'iyyar a Abuja. Hoto: @MayorOfNasarawa
Source: Twitter

Dalilin kin tsayar da dan takara a NNPP

Shugaban NNPP na kasa, Bala Mohammed, ne ya bayyana hakan yayin taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) karo na 11 da aka gudanar a Abuja ranar Asabar, in ji rahoton Tribune.

A cewarsa, halin da Najeriya ke ciki a yanzu na bukatar jam’iyyun siyasa su hada kai wajen mara wa sahihin dan takara baya maimakon tsayar da ‘yan takara saboda kawai cika ka’ida.

“Ba dole ba ne sai jam’iyya ta tsayar da dan takarar shugaban kasa a kowane zabe ba. Ya kamata mu duba wadanda sauran jam’iyyu suka fitar domin tabbatar da ko suna da kwarewa, cancanta da kuma hangen nesa na jagorantar Najeriya,” in ji Bala Mohammed.

Bala Mohammed ya bayyana cewa an kira taron NEC ne domin amincewa da ‘yan takarar da aka zaba ta hanyar yarjejeniya bisa tanadin dokar zabe ta shekarar 2026.

Ya kuma ce taron zai tabbatar da nadin shugaban jam’iyyar na rikon kwarya bayan murabus din tsohon shugaban jam’iyyar wanda ya sauya sheka zuwa ADC.

Kara karanta wannan

Peter Obi ko Kwankwaso: NDC ta shirya tsaida 'dan takarar shugaban kasa a zaben 2027

NNPP za ta tantance sauran ‘yan takara

Shugaban jam’iyyar ya jaddada cewa NNPP za ta fara duba wadanda sauran jam’iyyu suka tsayar a matsayin ‘yan takarar shugaban kasa kafin ta yanke shawarar wanda za ta iya hada kai da shi.

Ya ce jam’iyyar za ta yi la’akari da kundin tsarin mulki, manufofi da kuma cancantar dan takarar kafin daukar matsaya, in ji rahoton Punch.

Bala ya ce:

“Za mu duba jam’iyyun siyasa da ‘yan takararsu domin ganin wanda ya dace da manufofinmu da hangen nesanmu na gina Najeriya."
Jam'iyyar NNPP ta ce za ta marawa wata jam'iyya baya a 2027
Takardar dangwala zabe da kuma tambarin jam'iyyar NNP. to: UGC
Source: Facebook

Martani kan rade-radin hadaka da NDC

Da yake magana kan rade-radin cewa NNPP na shirin hade kai da jam’iyyar NDC, Bala Mohammed ya ce har yanzu ba a dauki wani mataki a hukumance ba.

Ya ce duk da cewa tsohon dan takarar shugaban kasa na NNPP a zaben 2023 ya koma NDC, hakan ba yana nufin jam’iyyar ta riga ta yanke shawarar shiga kawance da ita ba.

Kara karanta wannan

Esther Okereke: Fitacciyar jarumar fim a Najeriya ta samu tikitin takarar shugaban kasa a 2027

Bala Mohammed ya tunatar da cewa dan takarar shugaban kasa da NNPP ta fitar a 2023 shi ne mafi cancanta a lokacin.

Sai dai ya ce bayan ficewarsa daga jam’iyyar zuwa NDC, NNPP ba ta da wani mutum da take ganin yana da irin wannan karbuwa da cancanta a yanzu.

NNPP ta kunnowa Kwankwaso wuta

A wani labari, mun ruwaito cewa, Tsagin NNPP ya nesanta kansa daga zargin da wasu 'yan majalisar Amurka ke yi wa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

NNPP ta bayyana cewa ba ta ji dadin mu'amalarta da Kwankwaso ba kafin daga bisani ta dauki matakin korarsa daga jam'iyyar.

Jam'iyyar ta bukaci hukumar DSS da sauran hukumomin tsaro da su yi wasa da zargin da Amurka ke yi wa Kwankwaso.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com