Tinubu Ya Yi Gargadi Mai Zafi kan Zargin Shirin Amfani da Addini a Zaben 2027
- Fadar Shugaban ƙasa ta yi gargadi cewa wasu ‘yan siyasa na amfani da addini a siyasa game da zaben 2027 da ke tafe
- Ta ce ana amfani da bidiyoyi na bogi da bayanan ƙarya domin tada rikici tsakanin Musulmi da Kiristoci a kafafen sada zumunta
- Gwamnati ta ce za a binciko masu yaɗa ƙarya tare da gurfanar da su bisa doka saboda barazana ga zaman lafiya da haɗin kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Fadar Shugaban Ƙasa ta yi gargadi mai zafi game da zaben shekarar 2027 inda ta zargi wasu da shirin kawo fitina.
Gwamnatin Bola Tinubu ta zargi wasu ‘yan siyasa da ba a bayyana sunayensu ba da yunƙurin amfani da addini wajen harkokin siyasa kafin zaɓen 2027.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa daga Ofishin Sadarwar Zamani da Dabarun Gwamnati da Arise News ta samu a jiya Alhams 28 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan
'Jirgi marar matuki zan nada': Sowore kan wanda zai ba ministan tsaro idan ya ci mulki
Gargadin Tinubu kan zaben 2027 da ke tafe
Fadar shugaban ƙasa ta yi gargadi kan yaɗa labaran ƙarya da ka iya tayar da rikici a ƙasa gabannin zaben 2027.
Ta ce za a gano waɗannan ‘yan siyasa tare da kai su ga hukumomin da suka dace domin gudanar da bincike da ɗaukar mataki.
Sanarwar ta ce gwamnati ta lura da ƙoƙarin amfani da addini wajen yaɗa siyasa ta kafafen sada zumunta daban-daban.
Ta ƙara da cewa an riga an ga bidiyo na bogi da sauti na ƙarya da ake amfani da su wajen bata sunan Shugaba Bola Tinubu.
A cewarta, ana ƙirƙirar labaran ƙarya ne domin tada rikici tsakanin Musulmi da Kiristoci ta hanyar amfani da kafafen sada zumunta.

Source: Facebook
Yadda Tinubu ya rike Musulunci hannu biyu
Fadar ta ce Shugaba Tinubu ba ya ɓoye addininsa, Musulmi ne kuma yana da mata wacce Kirista ce, yana shugabantar ƙasa mai addinai daban-daban.
Ta ce Najeriya ta ginu ne bisa zaman lafiya, ‘yancin bauta da mutunta juna tsakanin mabiya addinai daban-daban.

Kara karanta wannan
Ayyukan da Tinubu ya saka a gaba bayan gwamnatinsa ta shekara 3 a mulkin Najeriya
Fadar ta ce addinai biyu, Musulunci da Kiristanci suna koyar da soyayya, zaman lafiya, adalci da tausayi ga ɗan Adam.
Ta kuma roƙi ‘yan Najeriya su daina yaɗa labaran da ka iya raba kan al’umma, su tabbatar da gaskiya kafin rarrabawa, cewar rahoton Punch.
Har ila yau, ta ce duk wanda aka kama da irin wannan laifi zai fuskanci bincike da hukunci bisa dokar Najeriya ta kafofin sadarwa domin girbar abin da ya shuka.
Tinubu ya fadi kokarinsa a shekaru 3
Mun ba ku labarin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan gwamnatinsa inda ya ce ta ɗauki matakai masu wahala domin ceto tattalin arzikin Najeriya.
Tinubu ya bayyana cewa an samu ci gaba a fannoni kamar hanyoyi, ilimi, noma, gidaje da makamashi cikin shekaru uku da ya yi a karagar mulkin kasar nan.
Shugaban ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa sadaukarwar da suka yi ba ta tafi a banza ba domin ƙasar na dawowa cikin hayyacinta.
Asali: Legit.ng