Obi: NDC Ta Rufe Sayar da Fam, Ta Samar da 'Dan Takarar Shugaban Kasa 1 gabanin 2027

Obi: NDC Ta Rufe Sayar da Fam, Ta Samar da 'Dan Takarar Shugaban Kasa 1 gabanin 2027

  • Jam’iyyar hamayya a Najeriya ta NDC ta rufe sayar da fam na neman takarar shugaban ƙasa na babban zaben 2027 da ke tafi
  • Rahotanni sun nuna cewa Peter Obi ne kaɗai ya sayi fam ɗin takarar shugaban ƙasar, wanda ke nufi shi ne zai fafata da Bola Tinubu
  • Jam’iyyar ta ƙara wa’adin sauran kujeru kamar gwamnoni da majalisu da mako guda yayin da harkokin siyasa suka kankama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Jam’iyyar adawa ta NDC ta sanar da rufe sayar da fam ɗin nuna sha’awa da neman takarar shugaban ƙasa na zaɓen 2027.

Bayanai daga jam'iyyar sun tabbatar da cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Mista Peter Obi, ne kaɗai ya sayi fam ɗin

Kara karanta wannan

Yan Kwankwasiyya, Obidents sun shirya tara miliyoyi saboda takarar Obi, Kwankwaso

NDC ta rufe sayar da fam na takarar shugaban kasa
Peter Obi da ya sayi fam din takarar shugaban kasa tare da manyan NDC Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Tashar Channels TV ta wallafa cewa har zuwa lokacin da aka rufe sayar da fam ɗin, babu wani ɗan siyasa da ya sayi fam na shugaban ƙasa baya ga Obi.

NDC ta kara wa'adin sayar da fam

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa sai dai jam’iyyar ta ce ta ƙara wa’adin karɓar fam ɗin nuna sha’awa na sauran muƙamai da mako guda.

Sababbin wa’adin sun shafi masu neman kujerun gwamnoni, majalisar dattawa, majalisar wakilai da kuma majalisun dokokin jihohi.

NDC ta kara wa'adin sayar da fam na wasu kujerun
Alamar jam'iyyar NDC mai tashe a Najeriya Hoto: Nigeria Democratic Congress, Kano Branch
Source: Facebook

Sakataren jam’iyyar na ƙasa, Mista Ikenna Morgan Enekweizu, ya bayyana cewa wa’adin da aka sanya tun farko na ƙarfe 6.00 na yammacin Lahadi 17 ga Mayu, 2026, an tsawaita shi zuwa 12.00 na dare na Lahadi 24 ga Mayu, 2026.

Sai dai ya jaddada cewa wannan ƙarin lokaci bai shafi masu neman takarar shugaban ƙasa ba, domin an riga an rufe karɓar fam ɗin wannan kujera.

NDC ta fitar da jadawalin tantance ’yan takara

Kara karanta wannan

Rigima ta barke a Kaduna, zaben fitar da gwani ya jefa shugaban APC a matsala

Jam’iyyar ta bayyana cewa za a fara tantance masu neman takara daga ranar Talata 19 ga Mayu zuwa Talata 26 ga watan Mayun 2026.

Haka kuma, ta ce waɗanda suka tsallake tantancewa ne kawai za su samu damar karɓa da mayar da fam ɗin tsayawa takara tsakanin 20 zuwa 26 ga Mayu.

NDC ta yi gargaɗin cewa ba za ta sake ƙara wa’adin ba bayan wannan karo, don haka ta buƙaci masu neman takara su bi duk ƙa’idoji da jadawalin da aka tsara.

"Shekara 4 zan yi a mulki": Peter Obi

A baya, mun kawo labarin cewa tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi ya nanata alkawarin da ya yi na yin zangon mulki daya idan aka zabe shi a shekarar 2027 mai zuwa.

Obi, wanda ya koma NDC kwanan nan, ya ce ba zai kara awa guda a kan shekaru hudu ba ko da kuwa an sanya masa bindiga a kansa yayin da ya ke neman 'yan Najeriya su zabe shi.

Wannan dai ba shi ne karon farko da tsohon gwamnan ke fadar hakan ba, ko a baya da ya ke neman kujerar shugaban kasa, Peter Obi ya sha nanata cewa ba shi da niyyar dawwama a mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng