Siyasar Kano: Gwamna Abba Ya Kwantar da Kai, Ya Mika Bukata ga Kwankwaso

Siyasar Kano: Gwamna Abba Ya Kwantar da Kai, Ya Mika Bukata ga Kwankwaso

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya roki tsohon ubangidansa, Sanata Rabiu Kwankwaso ya hada kai da gwamnatinsa domin gina sabuwar Kano
  • Abba Gida-Gida ya nuna damuwa kan yadda Kwankwaso ya ware kansa daga sauran manyan kusoshin siyasar jihar, yana mai kafa hujja da wani taro
  • Gwamnan ya bukaci Kwankwaso ya jingine duk wani sabani da rashin fahimta, ya taho a hada kai domin ciyar da Kano zuwa gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bukaci jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da ya jingine duk wani sabani, ya taho a hada kai domin ci da Kano gaba.

Abba Gida Gida ya roki Kwankwaso ya goyi bayan gwamnatinsa domin tabbatar da zaman lafiya, hadin kai da ci gaban jihar Kano karkashin manufar “Sabuwar Kano”.

Kara karanta wannan

"Kai ma yaro na ne," Ganduje ya dauko tarihi yayin maida martani ga kalaman Kwankwaso

Abba.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf a taron Majalisar zartarwa Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Gwamna Abba ya halarci hawan Nassarawa

Gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Juma’a, 29 ga watan Mayu, 2026 a wurin bikin Hawan Nassarawa na shekara-shekara, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Abba ya jaddada cewa kishin Kano da muradanta su ya kamata a fi bai wa muhimmanci, ba burikan kashin kai ba

A cewarsa, gwamnatinsa ta kuduri aniyar gina Kano mai zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaba domin amfanin al’ummar jihar baki daya.

Abba ya aika sako ga Kwankwaso

“Ina kira gare shi da ya dubi Kano ba bukatun kansa ba, sannan ya zo mu hada kai domin tabbatar da zaman lafiya da gina sabuwar Kano mai dorewa da ci gaba,” in ji gwamnan.

Abba Kabir ya bayyana cewa kwanakin baya kusan dukkan manyan ‘yan siyasar Kano sun halarcobwani taron masu ruwa da tsaki da aka shirya, amma ban da Sanata Kwankwaso.

Ya ce har wasu gwamnoni da suka taba samun sabani da mataimakansu sun sasanta a wannan rana, kamar yadda jaridar Punch ta kawo.

Kara karanta wannan

"Ka cika hakuri": Sanusi II ya shawarci Gwamna Abba kan mulkin Kano

Abba Kabir ya bukaci hadin kan jiga-jigan Kano

Gwamna Abba ya kara da cewa:

“Lokacin da muka yi wani babban taro kwanakin baya, na lura kusan kowa yana wurin sai Kwankwaso kadai. Hatta gwamnoni da suka samu matsala da mataimakansu sun sasanta a ranar. Burinmu shi ne hadin kan jihar Kano."

Gwamnan ya ce babban burin gwamnatinsa shi ne hada kan jama’ar Kano tare da dawo da martabar jihar kamar yadda take a baya.

Ya bayyana cewa shugabanci bai kamata ya kasance kan bambancin siyasa ba, sai dai a mayar da hankali kan muradun al’umma da ci gaban jihar.

Kwankwaso.
Jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yana magana da mahoya bayansa da suka kai masa ziyara Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Ganduje ya maida martani ga Kwankwaso

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya maida martani ga kalaman jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wan da ya kira da yaronsa.

Ya ce tun a farkon siyasarsa, ya taimaki Kwankwaso musamman a lokacin zaben majalisar dokoki ta kasa da ya kai shi matsayin mataimakin kakakin majalisar wakilai.

Ganduje ya kuma tuna da zaben fidda gwani na gwamna a Kano a shekarar 1998, inda ya ce mutane da dama sun yi imanin cewa shi ne ya lashe zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262