Kiristoci Sun Koka kan Nuna Masu Wariya a Zaben Fitar da Gwanin APC a Niger

Kiristoci Sun Koka kan Nuna Masu Wariya a Zaben Fitar da Gwanin APC a Niger

  • Wata Kungiyar Kiristoci ta yi magana kan zaben fitar da gwanin jam'iyyar APC da aka yi inda ta zargi an nuna wariya karara ga mabiya Kiristanci
  • Kungiyar ta yi zargin cewa an hana Kiristoci shiga zabukan fitar da gwani da aka gudanarwa a fadin jihar yanzu
  • Shugaban kungiyar Habila Diko ya bukaci Gwamna Mohammed Umar Bago ya dakatar da abin da ya kira wariya da danniyar Kiristoci a siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Minna, Niger - Hadakar kungiyoyin Kiristoci a Niger sun yi Allah wadai da yadda aka gudanar da zaben fitar da gwanin APC a jihar.

Kungiyar mai suna 'Niger State Christian Voice in Politics and Governance' ta zargi jam’iyyar APC da hana Kiristoci shiga zabukan fitar da gwani da ake gudanarwa a jihar.

Kara karanta wannan

'Jirgi marar matuki zan nada': Sowore kan wanda zai ba ministan tsaro idan ya ci mulki

Kiristoci sun caccaki tsarin zaben fitar da gwanin APC a Niger
Gwamna Mohammed Umaru Bago na jihar Niger. Hoto: Mohammed Umaru Bago.
Source: Twitter

Ana zargin an hana Kiristoci takara a Niger

Rahoton Punch ya ruwaito kungiyar na cewa wannan na hana Kiristoci samun damar tsayawa takara a zaben 2027 mai zuwa.

Kungiyar ta kuma yi zargin cewa ana matsa wa ‘yan takarar Kirista lamba su janye daga neman kujerun Sanata, Majalisar Wakilai da Majalisar Dokokin jihar.

Sun bayyana cewa tsarin da ake amfani da shi na maslaha da rabon mukamai yana cutar da Kiristoci.

Kiristoci sun zargi APC a Niger da hana su takara
Taswirar jihar Niger da Kiristoci suka yi korafi kan zaben fitar da gwanin APC. Hoto: Legit.
Source: Original

Kirisitoci sun tura bukata ga Gwamna Bago

Shugaban kungiyar, Habila Diko, ya bukaci gwamna Mohammed Umaru Bago da shugabannin APC su dakatar da abin da ya kira tsari na wariya ga Kiristoci.

Ya ce a halin yanzu manyan mukaman gwamnati a jihar duk Musulmai ne ke rike da su, kamar yadda Daily Post ta ce.

Ya ce:

“Da farko, muna yaba wa Gwamna, Mohammed Umaru Bago, bisa kokarinsa na kafa tsarin rabon mulki domin tabbatar da cewa mulki yana zagayawa tsakanin dukkan kananan hukumomi 25.

Kara karanta wannan

Gombe: Pantami ya fitar da wasikar da ya turawa APC kafin shiga PDP

“Amma muna son jan hankalin gwamna da shugabannin APC kan rashin adalcin da ake yi wa ‘yan takarar Kiristoci masu neman kujerun takara daban-daban.
“Mun lura da matukar damuwa kan yadda ake ware ‘yan takarar Kiristoci da gangan ta hanyar amfani da tsarin maslaha da rabon mukamai, wanda ya sa Kiristoci ba su da wakilci wajen neman kujerun Majalisar Tarayya.
“‘Yan takarar Kiristoci masu neman kujerun Majalisar Dokokin jiha ana matsa musu su janye ko su hakura da takara."

Kungiyar ta hada da Catholic Social Forum, Nupe Christian Forum, Niger Christian Youth Forum, Christian Advocacy Youth Group, reshen matasan CPFN/PFN da kuma Christian Council of Nigeria Youth Wing.

Har ila yau akwai Coalition of APC Christian Youth Groups, National APC Christian Leaders Forum of Nigeria da Journalists for Christ.

'Yar Tinubu ta soki zaben fitar da gwanin APC

A baya, mun ba ku labarin cewa ‘yar shugaban kasa Bola Tinubu ta nuna damuwa kan yadda aka gudanar da zaben fitar da gwani a jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

Jerin gwamnoni 7 da suka samu tikitin takarar sanata na jam'iyyar APC a zaben 2027

Mrs Folashade Tinubu-Ojo ta zargi cewa an samu kura-kurai a sakamakon zaben fitar da gwani na mazabu da dama a jihar Lagos.

Yar shugaban kasar ta bukaci shugabannin APC na jiha da na kasa su binciki zaben kafin amincewa da sakamakon, tana gargadin cewa rikici na iya tashi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.