‘Kwankwaso Hatsari ne’: Tsohon Dan Majalisar Amurka kan Takarar Jagora da Obi

‘Kwankwaso Hatsari ne’: Tsohon Dan Majalisar Amurka kan Takarar Jagora da Obi

  • Wani tsohon dan majalisar Amurka mai suna Mike Arnold ya bayyana adawarsa ga duk wani tikitin takara da Rabiu Kwankwaso da Peter Obi
  • Arnold ya zargi Sanata Kwankwaso da kasancewa kusa da fadar Sarkin Musulmi tare da sauya jam’iyyu ba tare da tunani ba
  • Tsohon dan majalisar ya bukaci Peter Obi ya zabi abokin takara daban, yana cewa zai yi aiki tukuru wajen adawa da tikitin Kwankwaso

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Tsohon dan majalisar Amurka, Mike Arnold, ya bayyana adawarsa karara ga tikitin Rabiu Kwankwaso da Peter Obi.

Arnorld ya tabbatar da cewa zai yi adawa da duk wani tikitin shugaban kasa da Rabiu Kwankwaso yake ciki.

An fara adawa da tikitin takarar Kwankwaso da Obi
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso.
Source: Twitter

Hakan na cikin wani rubutu da Legit Hausa wanda tsohon dan majalisar ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

'Mutumina ne': Peter Obi ya yi magana da ake zargin yana gujewa Atiku

Arnold ya bayyana hakan ne bayan Peter Obi da Kwankwaso sun fice daga jam’iyyar ADC zuwa jam’iyyar NDC domin neman tikitin shugaban kasa a 2027.

Musabbabin Arnorld na adawa da tikitin Kwankwaso-Obi

A cewarsa, yana adawa da hadin Obi da Kwankwaso saboda tsohon gwamnan Kano na cikin na kusa da fadar Muhammadu Sa’ad Abubakar III.

Arnold ya kuma soki yadda Kwankwaso ke yawan sauya jam’iyyun siyasa, yana cewa bai taba rabuwa da biyayya ga masarautar Sokoto ba.

Ya yi ikirarin cewa Kwankwaso na rike da mukamin ministan tsaro lokacin wasu muhimman abubuwan tsaro da suka faru a Najeriya bayan shekarar 2001.

Arnold ya ce bayan dawowar Sarkin Musulmi daga wani aiki a kasashen Musulmi, wasu manyan hafsoshin soja masu neman gyara suka mutu a hatsarin jirgin sama.

Ya kuma yi zargin cewa bayan mutuwar tsohon Sarkin Musulmi da wasu ‘yan uwansa a hatsarin jirgi, an nada Sa’ad Abubakar cikin gaggawa a matsayin sabon sarki.

Tsohon dan majalisar ya kara da cewa daga baya kungiyoyin ta’addanci daga wasu kasashe suka fara bayyana a Najeriya suna haddasa hare-hare da kashe-kashe.

Kara karanta wannan

"Ba a taba maganar sauya sheka tsakanin Kwankwaso da APC ba": Kwankwasiyya

Arnold ya tuno cewa Kwankwaso ya ayyana dokar Shari’a a Kano tare da kafa Hukumar Hisbah lokacin da yake gwamna a shekarar 2000.

Tsohon dan majalisar Amurka a soki takarar Kwankwaso
Tsohon dan takarar shugaban kasa a NNPP, Rabiu Kwankwaso. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Sai dai gwamnoni da-dama sun dabbaka tsarin shari'ar addinin Musulunci a wancan lokaci.

Haka zalika baya ga Kwankwaso, akwai 'yan siyasa da-dama irinsu Atiku Abubakar da shi kan shi Peter Obi da suka yi suna wajen sauye-sauyen sheka.

An bayyana zargin da ake yi wa Kwankwaso

Ya kuma zargi jagora a tafiyar Kwankwasiyya da batutuwan almundahanar kudin fansho da wasu kwangiloli, yana cewa EFCC ta taba bincikarsa kan lamarin.

A karshe, Arnold ya bayyana cewa zai ci gaba da adawa da duk wata tikitin takara da Kwankwaso ke ciki ko da wa yake jagoranta.

Ya bukaci Peter Obi ya zabi wani mataimaki daban wanda ba zai kasance karkashin tasirin fadar Sarkin Musulmi ba.

Hadimin Ganduje ya koma tafiyar Kwankwaso

Mun ba ku labarin cewa Hon. Mustapha Dawaki, tsohon shugaban ma'aikata na shugaban APC na kasa ya sauya sheka daga jam'iyya mai mulki zuwa NDC.

Kara karanta wannan

Tikitin Tinubu da Kashim: Malami ya gano abin da zai kawo karshen APC

Jagoran tafiyar Kwankwasiyya kuma jigo a NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ne ya tarbe shi a gidansa da ke kan hanyar Miller Road a jihar Kano.

'Dan siyasar ya bar APC ne bayan rasa tikicin komawa Majalisar tarayya sakamakon tsarin sulhun da aka yi amfani da shi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.