Pantami Ya Fadi Dalilin Neman Tikitin Takarar Gwamnan Gombe a PDP

Pantami Ya Fadi Dalilin Neman Tikitin Takarar Gwamnan Gombe a PDP

  • Tsohon ministan sadarwa, Isa Ali Pantami, ya zama dan takarar gwamnan jam’iyyar PDP a Gombe domin zaben 2027
  • Pantami ya samu dubban kuri’u daga dukkan manyan mazabu uku na Gombe yayin tsarin tabbatar da dan takarar jam’iyyar PDP
  • Tsohon ministan ya ce manufarsa ita ce yaki da talauci ta hanyar ilimi, noma na zamani da jawo jarin kasashen waje zuwa Gombe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Pantami, Gombe - Tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Pantami, ya zama dan takarar gwamnan jam’iyyar PDP.

Rahotanni sun tabbatar da cewa tsohon minista Pantami ya samu tikitin takarar a Gombe domin zaben shekarar 2027.

Pantami ya samu tikitin takarar PDP a Gombe
Tsohon ministan sadarwa a Najeriya, Farfesa Isa Ali Pantami. Hoto: Professor Isa Ali Pantami.
Source: Facebook

Pantami ya fito ne a matsayin dan takara guda daya tilo yayin tsarin tabbatar da ‘yan takarar jam’iyyar da aka gudanar ranar Talata a jihar, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Pantami ya fice daga jam'iyyar APC, ya samu tikitin takarar gwamna a jihar Gombe

PDP ta tabbatar da nasarar Pantami

Shugaban kwamitin zaben PDP na Gombe, Gregory Yenlong, ya sanar da cewa Pantami ya samu kuri’u 52,955 daga dukkan mazabun majalisar dattawa uku.

A cewarsa, Pantami ya samu kuri’u 16,781 a Gombe ta Arewa da 12,752 a Gombe ta Tsakiya tare da 23,422 a Gombe ta Kudu.

Bayan tabbatar da shi, Pantami ya bayyana cewa kudirinsa ba neman mulki don anfani da kai ba ne, illa yi wa al’umma hidima.

Ya ce manufarsa ita ce hada kan jama’ar Gombe tare da tabbatar da cewa bambance-bambancen da ke tsakaninsu ya zama karfi ba rauni ba.

Pantami ya fadi dalilin tsayawa takara a Gombe karkashin PDP
Tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Sheikh Isa Ali Pantami a wurin taron tabbatar masa da takara a APC Hoto: Abba Sani Pantami.
Source: Facebook

Yadda talauci ya yi kamari a Gombe

Pantami ya bayyana cewa Gombe ce ta uku cikin jihohin Najeriya mafi fama da talauci inda kaso 74.5 na jama’a ke rayuwa cikin matsanancin hali.

Ya ce:

“Wannan ba batun neman mulki ba ne, illa hidimtawa bil’adama. Ba batun Isa ba ne, batun Gombe ne. Babu wariya a tare da mu. Muna son bambance-bambancenmu su zama karfinmu ba raunimu ba.

Kara karanta wannan

Zaben fitar da gwani: Atiku ya samu gagarumar nasara kan Amaechi a Gombe

“Gombe ita ce jiha ta uku mafi fama da talauci a Najeriya, inda alkaluman talauci suka kai kusan kashi 74.5 cikin dari. Wannan na nufin jama’armu na rayuwa cikin matsanancin talauci."

Ya ce shirinsa shi ne fitar da jama’a daga kangin talauci musamman ta hanyar bunkasa ilimi da noma na zamani mai amfani da fasaha, cewar The Guardian.

Tsohon ministan ya kara da cewa yana da niyyar bunkasa masana’antu tare da jawo jarin kasashen waje domin samar da ci gaba ga jama’ar jihar Gombe.

Yan takarar PDP sun kalubalanci Pantami

Mun ba ku labarin cewa yan takarar gwamna huɗu na PDP a Gombe sun ce sun ƙi yunkurin shigar da Farfesa Isa Ali Pantami cikin neman zaɓen fitar da gwani.

Dukkanin yan takarar sun ce doka ba ta yarda ɗan takara ya sauya jam’iyya bayan ya shiga zaɓen fitar da gwani a wata jam’iyya daban ba.

Wani na kusa da tsohon minista Isa Ali Pantami ya tabbatar da cewa tsohon mai neman takarar gwamna a APC na shirin komawa PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.