Jam'iyya Ta 'Kori' Shahararren Dan Takarar Shugaban Kasarta Gabanin Zaben Shekarar 2023

Jam'iyya Ta 'Kori' Shahararren Dan Takarar Shugaban Kasarta Gabanin Zaben Shekarar 2023

  • Rikicin jam'iyyar African Action Congress, AAC, ya dau sabon salo a yayin da ta nesanta kanta da dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore
  • Dr Leonard Nzenwa, shugaban jam'iyyar na kasa ya ce ana kokarin tabattar da cire Sowore a matsayin dan takarar shugaban kasa a hukumance
  • Shugaban na AAC ya yi ikirarin cewa Sowore yana yaudarar mutane yana karbar kudade daga hannun mutane da wasu zargin

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Jam'iyyar African Action Congress, AAC, ta nesanta kanta daga dan gwagwarmayar kare hakkin bil adama, Omoyele Sowore a matsayin dan takarar shugaban kasarta gabanin zaben 2023.

Dr Leonard Nzenwa, shugaban jam'iyyar na kasa ne ya bayyana hakan a Abuja cikin sanarwar da ya raba wa manema labarai a ranar Laraba, 7 ga watan Satumba, Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Abin Da Yasa Na Ki Shiga APC Da PDP, Dan Takarar Shugaban Kasa Na AP

Omoyele Sowore
Jam'iyya Ta Raba Jiha Da Fitaccen Dan Takarar Shugaban Kasarta Gabanin 2023. Hoto: Omoyele Sowore.
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya kuma yi ikirarin cewa Sowore yana yaudarar mutane yana karbar kudade daga hannun wasu da ba su san dawon garin ba.

Ya zargi dan gwagwarmayar kare hakkin bil adaman da aiki tare da wasu daga cikin jam'iyyar da waje da nufin kawo rabuwar kai.

Shugaban na AAC ya yi ikirarin cewa an kori dan takarar shugaban kasar, ya kara da cewa babu wanda zai so ya yi harka da shi.

Nzenwa ya ce jam'iyyar ta tabbatar cewa hukuncin kotun da Sowore ya yi ikirarin cewa ta bashi nasara "babban karya ne."

Ana kokarin tabbatar da tsige Sowore a matsayin dan takarar shugaban kasa a hukumance - Nzenwa

Nzenwa ya ce AAC a halin yanzu tana kotu don tabbatar da cewa an cire Sowore a matsayin dan takarar shugaban kasarta na zaben 2023.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shugaban 'yan sanda ya magantu kan yiwuwar yin zabe a shekara mai zuwa

Kalamansa:

"Abu na biyu da muka yi shine shigar da kara a kotu kuma don soke halascinsa, kuma a yanzu suna neman tsira ne!
"Bayan hakan yanzu muna kokarin tabbatar da cewa mun cire sunansa a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyarmu, munyi nasara a wannan.
"Matakin na gaba shine tabbata da cewa an cire sunansa a matsayin shugaba mu na kasa sannan mu sanar da dukkan yan takarar mu da suka ci yi nasara a zaben cikin gida. Ba za mu yi kasa a gwiwa ba."

Abin Da Muka Tattauna Da Obasanjo, Dan Takarar Shugaban Kasa Na AP

A bangare guda, dan takarar shugaban kasa na Accord Party, AP, Farfesa Christopher Imumolen ya bayyana abin da suka tattauna da tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

Vanguard ta rahoto cewa ba wannan bane karo na farko da mai fatan zama shugaban kasar ya ziyarci tsohon shugaban kasar.

Kara karanta wannan

Machina Ya Magantu Kan Wasikar Dake Yawo Mai Cewa Ya Janyewa Ahmad Lawan Takarar Sanata

Yayin ziyarar, hotuna sun nuna farfesan ya rusuna kan gwiwansa yayin da Obasanjo ke masa addu'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel