Yayin da Ake Rigima kan Magajin Gwamna, an Dakatar da Zaben Fitar da Gwanin APC

Yayin da Ake Rigima kan Magajin Gwamna, an Dakatar da Zaben Fitar da Gwanin APC

  • Jam’iyyar APC a Kwara ta dakatar da zaɓen fitar da gwani na gwamna da aka shirya yi a yau Alhamis 21 ga watan Mayun 2026
  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa hakan ya biyo bayan rikici da ruɗani sun dabaibaye jam’iyyar yayin da aka fara kaɗa ƙuri’a
  • Shugabannin APC sun ce umarnin dage zaɓen ya fito daga hedikwatar jam’iyyar ta ƙasa, yayin da ruɗani ya ci gaba tsakanin magoya baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ilorin, Kwara - Rikici ya sake ɓarkewa a APC reshen jihar Kwara bayan jam’iyyar ta sanar da dage zaɓen fitar da gwani.

An shirya gudanar da zaben fitar da gwani na gwamna a ranar Alhamis 21 ga watan Mayun 2026 yayin da ake shirin fitar da yan takara.

An dage zaben fitar da gwanin gwamna a Kwara
Gwamna Abdul Rahman Abdul Razak na jihar Kwara. Hoto: Bayo Onanuga, Kwara State Government.
Source: Facebook

An dage zaben fitar da gwani a Kwara

Kara karanta wannan

Babu imani: Wani ɗan masu kuɗi ya caccaka wa mahaifinsa wuka har lahira a Abuja

An sanar da dage zaɓen ne yayin da tuni mambobin jam’iyyar suka fara taruwa a rumfunan zaɓe domin gudanar da aikin kaɗa ƙuri’a, cewar Punch.

Wannan mataki ya biyo bayan sauya matsayar jam’iyyar kan ‘yan takarar majalisar dokokin jihar da aka fara bayyana cewa ba su cancanta ba.

Rahotanni sun nuna cewa sama da mutum 100 daga cikin masu neman takara an fara cire su daga jerin waɗanda aka tantance, cewar Leadership.

Sai dai daga baya APC ta sake fitar da sabon jerin sunaye inda ta amince da dukkan mutum 159 da suka nemi tikitin takara.

Rikici ya sake barkewa a APC kan zaben fitar da gwani
Taswirar jihar Kwara da ke APC ke mulki. Hoto: Legit.
Source: Original

Yaushe za a sake yin zaben?

Mai magana da yawun APC a Kwara, Abdulwaheed Olawale Babatunde, ya bayyana cewa an dage zaɓen zuwa ranar Juma’a 22 ga Mayu, 2026.

Shugaban APC na Kwara, Prince Sunday Fagbemi, ya ce shugabannin jam’iyyar na ƙasa ne suka bayar da umarnin dage zaɓen fitar da gwanin.

An kuma ruwaito cewa wasu ‘yan takara sun janye domin marawa Ambasada Yahaya Seriki baya a matsayin wanda gwamnati ke so.

Duk da sanarwar dage zaɓen, an ga dimbin magoya bayan APC sun fito a wasu gundumomi domin nuna goyon baya ga jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Sanata zai rikita APC, ya yi watsi da sakamakon zaɓen fitar da gwani a Cross River

Wasu daga cikin magoya bayan sun nuna damuwa kan rashin ganin jami’an INEC a wuraren zaɓe kafin sanarwar dage aikin ta bayyana.

INEC ta bayyana cewa aikinta kawai shi ne sanya ido domin tabbatar da zaman lafiya, ba shiga cikin gudanar da zaɓen ba.

A wasu yankuna na Kwara ta Kudu ma an samu ruɗani bayan wasu mambobi sun ce jami’an zaɓe ba su iso ba kafin dakatarwar.

Gwamnoni 3 ba su halarci tantancewar APC ba

A baya, an ji cewa jam'iyyar APC ta tabbatar da cewa gwamnoni uku ba su samu halartar tantancewar shirin tunkarar babban zaben 2027.

Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentwe Yilwatda ya ce gwamnonin sun bada uzuri kuma za a tantance su a duk lokacin da suka shirya.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da takwaransa na jihar Katsina, Malam Dikkko Radda na cikin wadanda aka tantance zuwa yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.