Hadimin Gwamna Abba Ya Yi Zargi kan Kwankwaso dangane da Zaben 2027

Hadimin Gwamna Abba Ya Yi Zargi kan Kwankwaso dangane da Zaben 2027

  • Mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature D/Tofa, ya yi tsokaci kan wasu abubuwan da suka faru a siyasar Kano
  • Sanusi Bature ya bayyana cewa da amincewar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso suka tuntubi Shugaba Bola Tinubu don komawa jam'iyyar APC
  • Hadimin na gwamnan Kano ya kuma zargi madugun na Kwankwasiyya da yi wa Shugaba Tinubu aiki don zaben shekarar 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature, ya yi zargi kan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Sanusi Bature ya yi zargin cewa Rabiu Kwankwaso, yana yi wa Shugaba Bola Tinubu aiki a fakaice gabannin babban zaɓen 2027.

Hadimin Gwamna Abba ya ce Kwankwaso na yi wa Tinubu aiki
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Twitter

Sanusi Bature ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar Arise News a ranar Laraba, 20 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan

"Dama sharrin shaidan ne": Abba ya kawo ƙarshen rikicin Rurum da Kawu Sumaila a Kano

Hadimin Abba Kabir ya ce NNPP ta mutu

Mai magana da yawun gwamnan na Kano ya jaddada cewa shirin ƙawancen siyasa da aka tsara tsakanin Kwankwaso da Peter Obi na ɗan lokaci ne kawai kuma ba zai dore ba.

Sanusi Bature ya yi ikirarin cewa jam’iyyar NNPP ba ta da sauran tagomashi a matsayin dandalin siyasa na zaɓubbukan 2027.

Hadimin gwamnan na Kano ya bayyana cewa tattaunawar cikin gida ta riga ta samar da matsaya ɗaya kan zaɓubbukan siyasa na daban da suka haɗa da jam’iyya mai mulki ta APC.

“NNPP ba ta da sauran ƙarfin da za ta iya zama dandamali mai ƙarfi na 2027. An samu yarjejeniya tsakanin manyan masu ruwa da tsaki, har da Rabiu Kwankwaso, domin lalubo mafita mai dorewa gabannin 2027 saboda NNPP ba za ta kai labari ba.”

- Sanusi Bature

Kwankwaso ya san da batun komawa APC

Sanusi ya ƙara da cewa an yi tattaunawa tsakanin manyan ’yan siyasa a Kano game da yiwuwar sake fasalin ƙawance.

Kara karanta wannan

2027: Martanin Kwankwaso ga zargin yana yi wa Tinubu aiki a NDC

“Tare da amincewar Kwankwaso, mun tuntuɓi Tinubu da APC a matsayin zaɓinmu na farko domin bincikar yiwuwar shiga jam’iyyar."

- Sanusi Bature

Sanusi Bature ya yi zargi kan Kwankwaso
Madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Hon Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Ya ƙara da cewa Kwankwaso da kansa da fari ya nuna sha’awar tattaunawa kai-tsaye da Shugaba Tinubu kan shawarwarin siyasa, amma daga baya ya yi fatali da batun.

“Kwankwaso ya jaddada cewa dole ne ya tattauna da Shugaba Tinubu kafin kowace yiwuwar sauya sheka. Sai dai kuma, bayan an sanya rana, ya soke ganawar, inda ya ce yana da tafiya ƙasar China, kuma bai sake sanya wata ranar ba.”

- Sanusi Bature

Abba ya sulhunta Rurum da Kawu Sumaila

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sulhunta Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila da Kabiru Alhassan Rurum.

Gwamna Abba ya shiga tsakani domin kawo karshen takaddamar da ta shiga tsakanin Honarabul Kabiru Alhassan Rurum da Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila.

Bangarorin biyu sun sanar da cewa sun yafe wa juna tare da warware duk wani sabani da ya shiga tsakaninsu, inda suka nuna cewa sharrin shaidan ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng