"Da Izinin Kwankwaso," Wata Sabuwa Ta Bullo kan Yadda Gwamna Abba Ya Koma APC

"Da Izinin Kwankwaso," Wata Sabuwa Ta Bullo kan Yadda Gwamna Abba Ya Koma APC

  • Mai magana da yawun gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sake tabo batun sauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa APC
  • Sanusi Bature ya yi ikirarin cewa Gwamna Abba bai amsa gayyatar Shugaba Bola Tinubu ba sai da tsohon ubangidansa, Rabiu Kwankwaso ya amince
  • Wannan kalamai na zuwa ne yayin da siyasar Kano ke kara daukar zafi tsakanin mabiyan Kwankwaso da 'yan jam'iyyar APC mai mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Darakta Janar na Yada Labarai da Hulɗa da Jama’a na Gidan Gwamnatin Kano, Sunusi Bature D-Tofa, ya sake tabo batun sauya shekar Gwanna Abba Kabir Yusuf zuwa APC.

Sanusi Bature ya yi ikirarin cewa Gwamna Abba ya tattauna da Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan yiwuwar komawa APC da amincewar tsohon ubangidansa, Rabiu Musa Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Hadimin Gwamna Abba ya yi zargi kan Kwankwaso dangane da zaben 2027

Sanusi Bature.
Mai magana da yawun gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: UGC

Bature ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Arise TV a shirin Morning Show, yayin da ake ci gaba da hasashen siyasar Kano gabanin zaɓen 2027.

Kwankwaso ya amince da shiga APC?

Mai magana da yawun gwamnatin Kano ya yi zargin cewa tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, shi ma yana goyon bayan wannan yunƙuri.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafin Facebook, Sanusi Bature ya ce:

"Gwamna Abba ya fara yunkurin komawa jam'iyyar APC da izinin Sanata Kwankwaso, shi ma mataimakin gwamna na wancan lokaci, AbdulSalam Gwarzo ya amince da matakin."

Siyasar Kano na kara daukar zafi

Wannan na zuwa ke yayin da siyasar Kano ke kara daukar zafi tsakanin jam'iyya mai mulki APC da 'yan Kwankwssiyya karkashin jagorancin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

A yan makonnin da suka shude, Kwankwaso ya hada kai da tsohon dan takarar shugaban kasa na LP, Peter Obi, inda suka fice daga ADC zuwa jam'iyyar NDC.

Kara karanta wannan

"Shirun da muka yi ba tsoro ba ne," Gwamna Abba ya tura zazzafan sako ga Kwankwaso

Sanusi Bature ya kuma yi zargin cewa Kwankwaso na yi wa Shugaba Tinubu aiki ne a boye ta hanyar wasu dabarun siyasa.

Abba da Kwankwaso.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf tare da tsohon ubangidansa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Obi zai samu goyon baya a Kano?

Jami’in gwamnatin Kano ya yi watsi da yiwuwar Peter Obi, ya samu gagarumin goyon baya a Kano, yana mai cewa tsarin siyasar jihar ba zai bar tsohon gwamnan Anambra ya tabuka wani abu ba a zaben 2027.

Sanusi Bature ya kuma ce bambancin akida tsakanin manyan jagororin adawa a Najeriya na iya hana samar da ƙaƙƙarfar haɗaka da za ta iya kalubalantar APC a zaɓen 2027 da ke tafe.

Ana zargin Kwankwaso na yi wa Tinubu aiki

A wani labarin, kun ji cewa mai magana da yawun gwamnatin Kano, Sanusi Bature D/Tofa ya yi zargin cewa Rabiu Kwankwaso na yi wa Tinubu aiki ne a fakaice.

Sanusi Bature ya jaddada cewa shirin ƙawancen siyasa da aka tsara tsakanin Kwankwaso da Peter Obi na ɗan lokaci ne kawai kuma ba zai dore ba.

Bugu da kari, Sanusi ya yi ikirarin cewa an yi tattaunawa tsakanin manyan ’yan siyasa a Kano game da yiwuwar sake fasalin ƙawance.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262