2027: Atiku Ya Gurfana gaban Kwamitin Tantancewa, Ya Gabatar da Muhimman Manufofinsa
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya gurfana gaban kwamitin tantance masu neman takara na jam'iyyar ADC
- Yayin tantance shi, Atiku ya gabatar da manufofin da ya bayyana a matsayin na ceto tattalin arziki da tabbatar da tsaro a Najeriya
- Wannan na zuwa ne yayin da jam'iyyar adawa ta ADC ke ci gaba da shirye-shiryen tunkarar babban zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana a gaban kwamitin tantance ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC ranar Laraba.
Atiku ya gurfana gaban kwamitin ne domin tantance takardunsa da kuma gabatar da tsare-tsarensa na farfado da tattalin arziki da tsaro gabanin babban zaben 2027.

Source: UGC
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Phrank Shaibu, ya fitar yau Laraba, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Ya ce ganawar ba wai tantancewa kadai ba ce, illa wata dama ce ta gabatar da hanyoyin ceto Najeriya daga matsin tattalin arziki, rashin aikin yi, tabarbarewar tsaro.
Atiku ya gabatar da tsarin ceto Najeriya
Atiku ya ce Najeriya ba za ta iya ci gaba da tafiya a wannan hali ba inda iyalai ke fama da matsin rayuwa, kamfanoni ke durkushewa saboda rashin tabbas a manufofi, yayin da masu zuba jari ke rasa kwarin gwiwa.
Ya bayyana cewa tsarinsa na tattalin arziki ya ta’allaka ne kan samar da ayyukan yi, bunkasa bangaren masu zaman kansu, da kuma daidaita harkokin kashe kudade.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce yana da kudurin dawo da Najeriya cikin kasashen da masu zuba jari ke son zuwa domin ci gaba mai dorewa.
Ya nuna damuwa kan matsalar tsaro
Dangane da batun tsaro, Atiku ya bayyana damuwarsa kan yadda ake ci gaba da zubar da jinin jama’a a sassa daban-daban na kasar nan.
Ya ce babu gwamnatin kirki da za ta zuba ido ana kashe mutane a garuruwansu ko kuma ana sace su a hanyoyi, gonaki da gidajensu, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan
"Ban nemi zama mataimakin Atiku ba": An fusata Rotimi Ameachi da tambayar tikitin ADC

Source: Facebook
Tsarin Atiku na samar da tsaro a Najeriya
A cewarsa, tsarin tsaronsa zai mayar da hankali kan tattara bayanan sirri, hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, da kuma samar da tsari mai karfi a matakin jihohi da yankuna.
"A wannan lokaci mai mahimmanci, Najeriya ba ta buƙatar gwaje-gwaje, abin da take bukata shi ne jagoranci mai inganci, hangen nesa, da kuma kwarin gwiwar daukar matakai masu wahala don amfanin ƙasa," in ji Atiku.
Atiku ya sake tabbatar da kudurinsa na gina Najeriya mai tsaro, hadin kai da wadata, inda kowane dan kasa zai rayu cikin zaman lafiya tare da samun damar cimma burinsa cikin mutunci.
Da gaske Atiku ke neman takara?
A wani labarin, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya jaddada aniyarsa ta neman takarar shugaban kasa a zaben 2027.
Mai ba Atiku shawara kan harkokin yada labarai, Paul Ibe, ne ya tabbatar da cewa ubangidansa da gaske yaken neman kujera lamba daya a Najeriya.
Ibe ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani ga wata tambaya da lauya mai kare hakkin bil’adama kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Inibehe Effiong, ya yi.
Asali: Legit.ng
