‘Watakila Allah bai Son Ka Shiga Wuta ne’: Malami Ya Shawarci Farfesa Pantami
- Malamin Musulunci a jihar Kaduna ya ba da shawara ga Farfesa Isa Ali Pantami bayan hana shi tikitin takarar gwamnan APC a Gombe
- Alkali Abubakar Salihu Zaria ya ce lamarin jarabawa ne wanda kwata-kwata babu dadi musamman idan aka dandana dadin mulki
- Sheikh Alkali ya roki Pantami ya yi hakuri da wadanda suka hana shi takara, yana cewa watakila Allah ya fi son shi shiga wuta ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Sanannen malamin Musulunci daga Kaduna, Sheikh Alkali Salihu Zaria ya yi magana bayan hana Farfesa Isa Ali Pantami takara.
Malamin ya ba Pantami hakuri duba da irin yadda ake zargin an yi masa rashin adalci a zaben fitar da gwani na takarar gwamna a Gombe.

Source: Facebook
Hakan na cikin wani faifan bidiyo da Legit Hausa ta leko daga shafin Sarki Abdullahi Fulani wanda aka wallafa a Facebook.
Alkali Zariya ya san dadin mulki
Sheikh Alkali ya yi magana kan yadda dadin mulki ke yaudarar jama'a inda ya ce ya sani rasa mulki idan ka dandana shi ya fi komai zafi.
Ya ce shi da kansa da ya rasa limanci sai da ya kusa mutuwa ball a ce ka saka rai za ka juya jiha gaba daya.
Ya ce:
"Ina rokon dan uwa, Malam Isa Ali Pantami ka bar masu, ka da ka ja kyale su, ta yiwu Allah bai son ka shiga wuta ne.
"Na sani ba dadi, jarabawa ce, wallahi na san ba dadi, saboda ka dandana ka ji, na rantse ba za ka san mulki na da dadi ba sai ranar da aka sauke ka."

Source: Twitter
Yadda malamin ya tausaya Farfesa Pantami
Malamin ya ce tabbas Malam Pantami abin tausayi ne kuma ya cancanci a tausaya masa saboda dacin da ke cikin rasa mulki.
Shehin malamin ya ce ko shi da ya rasa mukamin limanci da babu albashi ko alawus sai da ya ji kamar ya mutu tsabar bakin ciki.

Kara karanta wannan
"Shirun da muka yi ba tsoro ba ne," Gwamna Abba ya tura zazzafan sako ga Kwankwaso
"Aramma ka ga dai babu albashi da alawus a limanci ko, wallahi da aka sauke ni sai da na kusa mutuwa bare ka saka rai zaka juya jiha an ce a'a.
"Jama'a ku tsausaya wa Malam Isa wallahi, ban taba ganin yana masifa yana tsare ido ba sai wannan karo ya ce 'za ku ga abin da ba a taba gani ba'.
"Yi hakuri Malam Isa, ka san ni masoyinka ne, Allah ya fi sonka ne a Annur ba a Gombe ya ke son ganinka ba."
- Alkali Abubakar Salihu Zaria
'Takarar gwamna na nan': Yaron Pantami
Kun ji cewa dan tsohon ministan sadarwa a Najeriya, AbdulRahman Isa Pantami ya yi karin haske a rahotannin da ke cewa mahaifinsa ya hakura da neman takara.
An yi ta yada cewa Farfesa Ali Pantami ya hakura da batun neman takarar gwamna a Gombe wanda aka ce ba haka ba ne.
A karin bayanin da ya fitar, AbdulRahman Isa Pantami ya yi karin haske game da batun, inda ya bayyana cewa maganar neman takarar gwamna na nan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
