Gaskiya Ta Fito kan Zargin Shekarau Ya Ce Kwankwaso na Yi wa Tinubu Aiki

Gaskiya Ta Fito kan Zargin Shekarau Ya Ce Kwankwaso na Yi wa Tinubu Aiki

  • Kungiyar Kwankwsiyya ta ragargaji Malam Ibrahim Shekarau kan zargin cewa ya ce Rabiu Musa Kwankwaso na yi wa Bola Tinubu aiki a boye
  • An yada jita-jitar ne bayan Kwankwaso ya koma jam'iyyar NDC tare da hada kai da tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi da ke son takara a 2027
  • Hadimin Malam Ibrahim Shekarau ya fito ya yi karin bayani game da kalaman da ake cewa mai gidan shi ya fada a kan Rabiu Musa Kwankwaso

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Ƙungiyar Kwankwasiyya Movement ta caccaki tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau kan zargin cewa ya ce Rabiu Kwankwaso na aiki a ɓoye domin sake zaɓen Bola Tinubu.

An rawaito cewa Shekarau ya ce shi da Kwankwaso duk suna aiki domin Tinubu ya sake cin zaɓe, sai dai Kwankwaso yana yin hakan ne a ɓoye.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya fito da korafe korafe kan Buhari game da taimaka masa a 2015

Rabiu Musa Kwankwaso da Ibrahim Shekarau
Lokacin da Rabiu Musa Kwankwaso ya ziyarci Ibrahim Shekarau a Kano. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Malam Shekarau ya nesanta kansa daga maganar, yana mai danganta ta da masu yaɗa labaran ƙarya.

Martanin Kwankwasiyya ga Shekarau

Kakakin Kwankwasiyya, Habibu Saleh Mailemo ya bayyana zargin kalaman da aka danganta wa Shekarau a matsayin marasa tushe da kuma yunƙurin neman suna a siyasa.

Mailemo ya ce ya kamata mutum mai matsayin Shekarau ya riƙa auna kalamansa kafin ya yi magana a bainar jama’a, yana mai gargadin cewa irin waɗannan zarge-zarge na iya rage darajarsa.

Ya jaddada cewa an san Kwankwaso da faɗin gaskiya a harkokin siyasa:

“Kowa ya san ubangidana mutum ne mai magana kai tsaye. Idan yana tare da kai, yana tare da kai. Ba ya wasa da siyasa,”

Mailemo ya bayyana ƙwarin gwiwarsa cewa gaskiya za ta bayyana yayin da zaɓen 2027 ke gabatowa, yana mai cewa Kwankwaso na nan daram kan matsayarsa.

Rabiu Musa Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso na bayani a wani taron siyasa a Kano. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Martanin Malam Ibrahim Shekarau

Kara karanta wannan

Duk da yana NDC, Kwankwaso ya tabo batun aiki tare da Atiku, ADC a 2027

Kakakin Shekarau, Sule Ya’u Sule ya musanta kalaman da aka danganta wa ubangidansa, yana mai cewa masu yaɗa labaran ƙarya ne suka ƙirƙiro su.

Rahotanni sun nuna cewa Ya'u Sule ya ce labarin bai bayyana waje ko lokacin da Shekarau ya yi irin wannan magana ba.

“Asalin labarin ya fito ne daga wani mai rubutun yanar gizo ɗan kabilar Igbo, wanda daga baya ya bayar da haƙuri kuma ya yi alƙawarin cire shi.
A gaskiya ma, Shekarau ba ya Kano; yana Abuja lokacin da ake cewa ya yi kalaman, saboda haka ba daga gare shi suka fito ba. Masu yaɗa ƙarya ne suka ƙirƙire shi,”

In ji shi

Korafin Kwankwaso kan Buhari

A wani labarin, mun kawo muku cewa tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya yi korafi game da mulkin Muhammadu Buhari.

Kwankwaso ya bayyana cewa ya samarwa gwamnatin Buhari kuri'u kusan miliyan 2 a zaben 2015 amma shi da mutanensa ba su samu komai ba.

Ya bayyana haka ne yayin da ya ke martani game da korafe-korafen da jama'a ke yi kan sauya shekar da ya yi daga ADC zuwa jam'iyyar NDC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng