Yanzu Yanzu: An Zabi Gwamna Uzodimma a Matsayin Shugaban Kungiyar Gwamnonin APC

Yanzu Yanzu: An Zabi Gwamna Uzodimma a Matsayin Shugaban Kungiyar Gwamnonin APC

  • Kungiyar gwamnonin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta zabi gwamnan jihar Imo Hope Uzodimma a matsayin shugabanta
  • An sanar da Gwamna Uzodimma a matsayin shugaban gwamnonin APC bayan ya yi nasara a zaben da aka gudanar a Abuja
  • Gwamnan na jihar Imo ya karbi ragamar kula da harkokin kungiyar daga hannun tsohon gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu

Abuja - An zabi Gwamna Hope Uzodimma na jihar Imo a matsayin shugaban kungiyar gwamnonin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) wanda aka fi sani da 'Progressives Governors' Forum (PGF)', jaridar The Nation ta rahoto.

An fitar da sanarwar ne a babban birnin tarayya Abuja a ranar Laraba, 31 ga watan Mayu bayan an gudanar da zabe

Gwamna Hope Uzodimma
Yanzu Yanzu: An Zabi Gwamna Uzodimma a Matsayin Shugaban Kungiyar Gwamnonin APC Hoto: Governor Hope Uzodimma
Asali: Facebook

Da wannan ci gaban, daga yanzu Gwamna Uzodimma ne zai zama shugaban dukkanin gwamnonin da aka zaba karkashin inuwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Kungiyar PGF yana aiki ne a matsayin wani dandalin na hadin kai, aiwatar da manufofin ci gaba da kuma koyar da makaman sanin aiki a tsakanin mambobinta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Zamowar Gwamna Uzodimma a matsayin Shugaban PGF wata shaida ce da ke nuna kwarewarsa ta bangaren shugabanci da kuma yadda ya samu goyon baya daga sauran gwamnoni ’yan uwansa.

Nauyin da ya rataya a wuyan Uzodimma a matsayin shugaban PGF

A matsayin shugaban kungiyar, Gwamna Uzodimma zai taka muhimmiyar rawar gani wajen jagorantar ayyukan kungiyar, tabbatar da hadin kai tsakanin gwamnonin da kuma jan ragamar ajandar APC a fadin jihohin, rahoton Vanguard.

Da wannan sabon ci gaban, Gwamna Uzodimma zai samu damar bayar da gudunmawa wajen tsara manufofi da dabarun jam’iyyar APC.

Zai kasance a gaba-gaba wajen tattaunawa da yanke hukunci da zai amfani jam'iyyar da ci gaban kasar.

Shugabancinsa zai kasance mai muhimmanci wajen samar da ingantacciyar gwamnati, karfafa hadin gwiwa tsakanin jihohi, da kuma tabbatar da aiwatar da manufofin ci gaban APC.

Tinubu baya shirin rage alawus din yan bautar kasa

A wani labari na daban, wani bincike da aka gudanar ya gano cewa babu gaskiya a rade-radin da ke yawo cewa sabon shugaban kasa Bola Tinubu na shirin rage alawus din yan bautar kasa.

Wasu hotuna na ta yawo a manhajar WhatsApp cewa Shugaba Tinubu na shirin rage alwus din yan NYSC daga N33,000 zuwa N25,000.

Asali: Legit.ng

Online view pixel