Zaben gwamnan Osun: Abubuwa 7 masu muhimmanci game da dan takarar da ya kawo karshen APC

Zaben gwamnan Osun: Abubuwa 7 masu muhimmanci game da dan takarar da ya kawo karshen APC

Zaben gwamnan jihar Osun ya kammala a jiya, tuni aka sanar da wanda ya lashe zaben bayan da aka dauki lokaci ana aikin jefawa, tattarawa, kirge da kuma fitar da sakamakon zaben.

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ademola Adeleke na jam'iyyar PDP ne ya lashe zaben kamar yadda rahotanni suka bayyana da sanyin safiyar yau Lahad 17 ga watan Yulin 2022.

To amma, meye kuka sani game da wannan dan takara na gwamna ya lashe zaben, kuma ya kawo karshen mulkin jam'iyyar APC mai ci?

A rahoton da muka tattaro, mun kawo muku wasu muhimman abubuwa da ya kamata ku sani game da Ademola Adeleke.

Abubuwa 7 game da wanda ya lashe zaben gwamnan Osun
Zaben Osun: Abubuwa 7 da ya kamata ku sani game da dan takarar da ya kawo karshen APC | Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

1. Suna da nasabarsa, rayuwar

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Cikakken sunansa Ademola Nurudeen Jackson Adeleke, kuma an haife shi ne a gidan shahararren gidan Adeleke a Ede ta jihar Osun, a ranar 13 ga Mayu 1960.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP ya lashe zaben gwamnan jihar Osun

2. Mahaifinsa musulmi ne mai suna Raji Ayoola Adeleke yayin da mahaifiyarsa kuwa 'yar kabilar Igbo ce kuma kirista mai suna Nnena Esther Adeleke, rahoton Pulse.ng.

Shi ne dan auta a cikin yara 3 na iyayensa, manyan yan uwansa su ne Dr Adedeji Adeleke da marigayi Mr Isiaka Adeleke.

3. Abubuwan da sa a gaba

Ademola Nurudeen Jackson Adeleke dan siyasa ne kuma dan kasuwa, Sanata ne mai wakiltar mazabar Osun ta yamma tsakanin 2017 zuwa 2019.

Ya tsaya takarar gwamnan jihar Osun a 2022 inda ya samu kuri’u 403, 371 a kan gwamna mai ci Adegboyega Isiaka Oyetola wanda ya samu kuri’u 375,027.

4. Matakin karatunsa

Gwagwarmayarsa ta ilimi ta fara ne a Makarantar Firamare ta Methodist da ke Surulere a jihar Legas, Najeriya. Sannan ya koma Nawarudeen Primary School da ke a Ikire a tsohuwar jihar Oyo.

Ya yi makarantar sakandare ta Seventh Days Adventist da kuma Ede Muslim Grammar School a Ede, nan ma dai a tsohuwar jihar Oyo.

Kara karanta wannan

Zaben Osun: Dan takarar PDP ya lashe kananan hukumomi 17 cikin 30

Ya karanta ilimin shari'ar manyan laifuka da kimiyyar siyasa a Jami'ar Jiha ta Jacksonville da ke Alabama a kasar Amurka.

5. Sai dai hanzari ba gudu ba, an sha samun cece-kuce da yawa kan takardunsa na karatu wanda ya sa ya ci gaba da karatunsa a kwalejin jihar Atlanta Metropolitan a Amurka kuma a 2021 ya kammala digiri a fannin shari’a a can din.

Gwagwarmayar rayuwa

6. Kasuwa

Gwagwarmayarsa ta aiki ta fara ne a Kamfanin Quicksilver Courier a Atlanta jihar Jojiya ta Amurka daga 1985 zuwa 1989, inji rahoton NewsWireNGR.

A tsakanin 1992 zuwa 1999, ya yi aiki a matsayin babban darakta na kamfanin Guinness Nigeria plc kuma daga 2001 zuwa 2016 ya yi aiki a matsayin babban darakta a kamfanin dan uwansa da aka sani da Pacific Holdings Limited.

Ya kuma yi aiki a kamfanin sarrafa dandano da kamshi a Atlanta ta jihar Jojiya a Amurka a matsayin mataimakin shugaban kamfani daga 1990 zuwa 1994.

Kara karanta wannan

Zaben Osun: APC ta ji kunya, Gwamna ya rasa akwatin gidan Gwamnati a hannun PDP

7. Siyasa

A siyasa kuwa, ya fara ne a 2001 tare da dan uwansa Marigayi Sanata Isiaka Adeleke. Bayan rasuwar dan uwansa a 2017, ya tsaya takara a zaben fidda gwani na Osun ta yamma a 2017 din kuma ya yi nasara.

Ya kuma tsaya takarar kujerar Gwamna a ranar 23 ga Yuli, 2018, kuma ya yi nasara a zaben fidda gwan kana ya fito a matsayin dan takarar gwamna na PDP a jihar Osun.

Ya fito a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Osun a ranar 22 ga watan Satumba 2018, amma hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana cewa zaben bai kammala ba saboda wasu dalilai, Sahara Reporters.

Jihar ta sake zaben ranar 27 ga Satumba 2018 da kuma ranar 5 ga Yuli 2019 amma kotun koli ta bayyana Gboyega Oyetola a matsayin wanda ya lashe zaben.

Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP ya lashe zaben gwamnan jihar Osun

Kara karanta wannan

Dan takarar gwamna PDP a jihar Osun ya bayyana dalilin da yasa yayi tsallaken layi

A wani labarin, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana Dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP),Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Osun.

Baturen zabe a jihar, Toyin Ogundipe, ne ya sanar da sakamakon zaben a safiyar ranar Lahadi, 17 ga watan Yuli, jaridar The Cable ta rahoto.

Adeleke ya samu kuri’u 403, 371 wajen lallasa babban abokin hamayyarsa Gboyega Oyetola na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), wanda ya samu kuri’u 375,027.

Asali: Legit.ng

Online view pixel