Wasa Farin Girki: Minista Ya Cike Takardar Takarar Tinubu a 2027
- Ministan ayyuka, David Umahi ya bayyana cewa akwai nasara ga Najeriya idan shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake 'dare wa karagar mulki
- Ya bayyana cewa cike fam na takarar Bola Tinubu karo na biyu mataki ne da zai kara karfafa ayyukan ci gaba da bunkasa Najeriya
- David Umahi ya bayyana haka ne bayan shugaban kasa ya bayyanar da aniyarsa na sake tsaya wa takara a babban zabe mai zuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Ministan ayyuka, David Umahi, ya sanya hannu kan fam ɗin tsayawa takara na shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, domin neman wa’adin mulki na biyu.
Ya bayyana cewa wannan mataki a matsayin nasara da za ta tabbatar da dorewar ayyukan gwamnati da romon dimokuradiyya a Najeriya.

Source: Twitter
Jaridar Punch ta wallafa cewa wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Francis Nwaze, ya fitar a ranar Talata,5 ga watan Mayu, 2026.
Dave Umahi ya goyi bayan takarar Bola Tinubu
Jaridar PM ta wallafa cewa Umahi ya ce wannan goyon baya na nuna ƙudurin ci gaba da tabbatar da manufofi tare da ƙarfafa nasarorin da gwamnatin ke samu.
Ya bayyana cewa fam ɗin takarar wata muhimmiyar alama ce a tafiyar ci gaban Najeriya, yana mai cewa hakan yana nuna haɗin kan jama’a wajen tabbatar da dorewa, kwanciyar hankali da kuma gina kan nasarorin da aka samu a ƙarƙashin gwamnatin yanzu.
Umahi ya jaddada cewa jagorancin Tinubu ya haifar da manyan sauye-sauye a ɓangaren ababen more rayuwa, musamman a gina da gyaran hanyoyi, waɗanda ya ce suna taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin arziki.

Source: Twitter
Ministan ya ce ayyukan da ake gudanarwa a sassa daban-daban na ƙasar na nuna ƙudurin gwamnati na samar da sakamako a aikace.
Umahi ya jaddada manufar shugaba Tinubu
Ya ƙara da cewa shugaban ƙasar na da cikakken ƙwarewa da matsayi da zai ba shi damar kammala ayyukan da ake yi tare da ƙara zurfafa ci gaba a fannoni daban-daban.
A wani ɓangare na ci gaba da shirye-shiryen siyasa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Ikeja, James Faleke, ya karɓo fam ɗin nuna sha’awa da na tsayawa takara na jam’iyyar APC a madadin shugaban ƙasa.
Faleke, wanda shi ne wanda ya kafa ƙungiyar magoya bayan Tinubu, ya karɓi fom ɗin ne a Abuja bayan da sakataren shirye-shiryen jam’iyyar na ƙasa, Suleiman Argungu, ya sanar da fara sayar da fom ɗin.
Rahotanni sun nuna cewa sayen fom ɗin, wanda kudinsa ya kai Naira miliyan 100, ya zama wata alama ta fara neman sake tsayawa takarar shugaban ƙasa gabanin zaɓen 2027.
Hukumar INEC ta tsara gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na majalisun dokoki na ƙasa a ranar 16 ga Janairu, 2027, yayin da zaɓen gwamnoni da na majalisun jihohi za su gudana a ranar 6 ga Fabrairu, 2027.

Kara karanta wannan
Masarautar Ilorin ta gano amfanin Tinubu a ofis, ta goyi bayan ya zarce zuwa 2031
Yadda za a zabi dan takara a ADC
A wani labarin, mun wallafa cewa jam’iyyar ADC ta bayyana cewa za ta zaɓi ɗan takarar shugaban kasa ta hanyar amfani da tsarin maslaha domin zaben 2027 a shirin tunkarar APC a filin zabe.
Sakataren yada labaran ADC na kasa, Bolaji Abdullahi, ya bayyana wannan shirin ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi ranar Litinin, 4 ga watan Mayun 2027, inda ya soki yadda wasu suka sauya sheka.
Ya bayyana cewa Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso da suka sauya sheka zuwa NDC, sun yi haka ne domin su nemi tikitin takarar shugaban kasa maimakon su tsaya a fafata da su a ADC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

