2027: APC Ta Fitar da Sabon Wa'adin Sayar da Fom da Tantance Masu Son Takara

2027: APC Ta Fitar da Sabon Wa'adin Sayar da Fom da Tantance Masu Son Takara

  • Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya APC tsawaita wa'adin sayar da fom din takara da sauya ranakun tantance masu son takara a zaben 2027
  • Lamarin ya biyo bayan wa'adin da jam'iyyar ta sanya na cewa za a dakatar da sayar da fom a daren Litinin, 4 ga watan Mayun shekarar 2026
  • Sakataren yada labaran jam'iyyar APC na kasa, Felix Morka ya yi karin bayani game da sabon wa'adin da suka sanya a kan sayar da fom din takara

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jam’iyyar APC ta sanar da tsawaita wa’adin sayar da fom din takara tare da mika takardun nuna sha’awar takara ga masu son neman mukamai gabanin zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

APC ta fitar da dan takarar gwamna a Oyo, ta juyawa ministan Tinubu baya

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da samun sabani a jihohi kan yadda gwamnoni ke ayyana wadanda suke so su gaje su a zaben 2027.

Shugaban APC na kasa, Nentawe Yilwatda
Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda a ofis. Hoto: All Progressive Congress
Source: Facebook

Jam'iyyar APC ta kara wa'adin sayar da fom

A cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na kasa na APC, Felix Morka, ya fitar a X a yau Litinin, jam’iyyar ta kuma sauya jadawalin tantance ‘yan takara domin dacewa da sabon tsarin da ta fitar.

A cewar APC:

“An tsawaita sayar da fom din zuwa karfe 12:00 na dare na ranar Laraba, 6 ga Mayu, 2026, yayin da mika fom din da aka cika zai kare da karfe 12:00 na dare na ranar Alhamis, 7 ga Mayu, 2026.”

Jam’iyyar ta kara da cewa:

“Za a gudanar da tantance ‘yan takara daga ranar Juma’a, 8 ga Mayu zuwa Talata, 12 ga Mayu, 2026, yayin da za a fitar da jerin wadanda aka tantance a ranar Laraba, 13 ga Mayu, 2026.”

Kudin sayar da fom din APC

Kara karanta wannan

Ganduje, manyan APC sun saya wa Abba fam, an tara N50bn don takarar Tinubu a 2027

Jaridar Punch ta ruwaito cewa jam’iyyar mai mulki ta sanya farashin fom din takarar shugaban kasa Naira miliyan 100, yayin da na gwamna yake Naira miliyan 50.

Ta kara da cewa masu neman takarar majalisar jiha za su biya Naira miliyan 6, masu neman kujerar Majalisar Wakilai Naira miliyan 10, yayin da masu neman kujerar Majalisar Dattawa za su biya Naira miliyan 20.

Yadda Sanata Alkali ya saye fom din APC
Lokacin da tsohon ministan sufuri ya saye fom din APC. Hoto: Sai'idu Ahmed Alkali
Source: Facebook

Jam’iyyar APC mai mulki ta fara sayar da fom din son takara ga masu shirin neman mukamai daban-daban a makon da ya gabata , a ranar Talata, domin shirin babban zaɓen 2027.

Yusuf Buhari zai yi takara a APC

A wani labarin, mun kawo muku cewa dan tsohon shugaban kasa, Yusuf Muhammadu Buhari ya karb fom din tsayawa takarar majalisar wakilai a jihar Katsina.

Gwamna Dikko Umaru Radda ne ya mika wa Yusuf Buhari fom din a wani taro da ya hada manyan 'yan jam'iyyar APC a fadar gwamnatin jihar Katsina.

Yusuf Buhari ya bayyana cewa zai tsayar da adalci idan mutane da ya ke son wakilta a kananan hukumomin Katsina uku suka ba shi hadin kai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng