ADC Ta Saki Jadawalin Zaben Fidda Gwani, Ta Fitar da Kudin Sayen Fom don Takara

ADC Ta Saki Jadawalin Zaben Fidda Gwani, Ta Fitar da Kudin Sayen Fom don Takara

  • Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta shirya gudanar da zaben fidda gwani domin tunkarar zaben shekarar 2027
  • ADC ta fitar da jadawalin gudanar da zaben fidda gwani a kujerun takarar shugaban kasa, gwamnoni, sanatoci 'yan majalisar wakilai da na jihohi
  • Hakazalika, ADC ta bayyana kudaden da dukkanin masu neman takara za su biya domin mallakar fom din jam'iyyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jam’iyyar ADC ta fitar da jadawalin gudanar da zaɓen fidda gwani na shekarar 2026, yayin da ake tunkarar babban zaben 2027.

Jam'iyyar ADC ta sanya ranar 25 ga Mayu, 2026, don zaɓen fidda gwani na ɗan takarar shugaban ƙasa, sannan ta sanya farashin fom ɗin tsayawa takara a kan Naira miliyan 100.

ADC ta sanya kudin fom don takara
Kakakin ADC na kasa, Bolaji Abdullahi da tambarin jam'iyyar Hoto: @BolajiADC
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin jam'iyyar na kasa, Bolaji Abdullahi, ya fitar a shafinsa na X a ranar Lahadi, 3 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan

'Ba sulhu a Nasarawa' Tsohon IGP ya rusa shirin APC, ya turje kan takarar gwamna

ADC ta shirya gudanar da zaben fidda gwani

ADC ta ce jadawalin ya tsara ƙa’idoji da buƙatun tsayar da ’yan takara gabanin babban zaɓen 2027, inda ta jaddada ƙudurinta na tabbatar da dimokuradiyya a cikin gida, tsari, da kuma bin dokar zaɓe.

Bisa ga tsarin, tuni aka fara gudanar da ayyukan, inda aka fara bayar da fom ɗin neman tsayawa takara daga ranar 1 ga Afrilu zuwa 4 ga Mayu, 2026.

An tsara sayar da fom ɗin tsayawa takara daga ranar 5 ga Mayu zuwa 10 ga Mayu, yayin da miƙa cikakkun fom ɗin zai gudana tsakanin 11 zuwa 13 ga Mayu, 2026.

Jam’iyyar ta ce za a gudanar da tantance masu neman takara daga ranar 14 zuwa 15 ga Mayu, sannan a biyo baya da wallafa sakamakon tantancewar ranar 17 ga Mayu.

Za a saurari ƙorafe-ƙorafe da suka taso daga tantancewar tsakanin 18 da 19 ga Mayu, yayin da ake sa ran fitar da jerin sunayen ƙarshe na waɗanda aka tantance ranar 20 ga Mayun 2026.

Kara karanta wannan

APC ta fitar da dan takarar gwamna a Oyo, ta juyawa ministan Tinubu baya

Yaushe ADC za ta yi zaben fidda gwani?

An tsara gudanar da zaɓen fidda gwani na majalisun dokoki na jihohi, majalisar wakilai, da kujerun Sanata lokaci guda a matakin gundumomi a ranar 21 ga Mayu, 2026.

Zaɓen fidda gwani na gwamna zai biyo baya ranar 22 ga Mayu, yayin da aka sanya zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa ranar 25 ga Mayun 2026.

Jadawalin ya kuma tanadi taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) na jam’iyyar ranar 26 ga Mayu, 2026, da kuma babban taron ƙasa na musamman ranar 27 ga Mayu, inda za a yi amincewa ta ƙarshe kan ’yan takara.

ADC za ta gudanar da zaben fidda gwani
Kakakin jam'iyyar ADC na kasa, Bolaji Abdullahi Hoto: @BolajiADC
Source: Facebook

Nawa ne kudin sayen fom na ADC?

Game da kuɗin shiga takara, ADC ta amince da tsarin farashin fom ɗin tsayawa takara ga dukkan kujerun da za a nema.

Yayin da fom ɗin shugaban ƙasa yake kan Naira miliyan 100, fom ɗin gwamna zai ci Naira miliyan 50, Sanata Naira miliyan 20, Majalisar wakilai Naira miliyan 10, sannan Majalisar dokoki ta jiha Naira miliyan 3.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban ƴan sanda ya ƙi yarda da sulhu, ya sayi fom ɗin takarar gwamna

Jam’iyyar ta sanar da rangwamen kashi 50 cikin 100 ga matasa, da kuma ragin kashi 25 cikin 100 ga mata da kuma masu buƙata ta musamman (PWDs).

Kwankwaso da Obi za su fice ADC

A wani labarin kuma, kun ji tsofaffin 'yan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi, za su fice daga jam'iyyar ADC.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi sun shirya sauya sheka zuwa sabuwar jam'iyyar adawa ta NDC.

Mai magana da yawun kungiyar Kwankwasiyya, Habibu Mohammed, ya shaida cewa sun yanke wannan shawara ne bayan amincewar baki daya daga masu ruwa da tsaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng