Usman Alkali Baba: Abubuwa 6 da ya kamata ku sani game da sabon Babban Sufetan 'Yan Sanda

Usman Alkali Baba: Abubuwa 6 da ya kamata ku sani game da sabon Babban Sufetan 'Yan Sanda

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata ya nada Usman Alkali Baba a matsayin sufeta janar na yan sanda, IGP, na rikon kwarya.

Baba ya maye gurbin Mohammed Adamu wanda aka tsawaita wa'adinsa da watanni uku a watan Fabrairun 2021.

Usman Alkali Baba: Abubuwa 6 da ya kamata ku sani game da sabon IGP
Usman Alkali Baba: Abubuwa 6 da ya kamata ku sani game da sabon IGP. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Kafin nadinsa, Baba mataimakin sufeta ne na yan sanda a rundunar yan sandan Nigeria.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kashe shugaban 'yan bindiga da ake nema ruwa a jallo a Zamfara

Ga wasu abubuwa da ya kamata ku sani game da sabon shugaban na 'yan sanda.

1. An haifi Alkali Baba a garin Giedam, jihar Yobe a ranar 1 ga watan Maris na shekarar 1963

2. Ya yi karatun digiri na BA(ED) a fannin kimiyyar siyasa a Jami'ar Bayero da ke Kano

3. Ya yi karatun digiri na biyu MPA a fannin ilimin aiwatar da ayyukan gwamnati da mulki daga Jami'ar Maiduguri a shekarar 1997.

4. Ya halarci Kwallejin Tsaro ta Kasa kuma mamba ne na Kungiyar Shugabannin Yan sanda na kasa da kasa.

KU KARANTA: Kabir: Ɗan Nigeria da bai taɓa karatun Boko ba ya ƙera babura a Katsina

5. Baba ya rike mukamai masu muhimmanci a baya da suka hada da mataimakin sufetan yan sanda mai kula da zone 5 a Benin, Zone 4 a Makurdi, Zone 7 a Abuja da kwamishinan yan sanda a Abuja da Delta.

6. Ya kuma taba rike mukamin sakatare na rundunar yan sandan.

A wani rahoton daban, Fadar Shugaban Kasa a ranar Lahadi ta ce kalaman Bishop din Katolika na Jihar Sokoto, Mathew Kukah, basu yi kama da na malamin addini ba a sakon sa na bikin Easter inda ya soki shugaban kasa, Muhammadu Buhari da gwamnatinsa.

Babban mai taimakawa shugaban kasa bangaren yada labarai, Garba Shehu, shine ya bayyana haka a wata sanarwa mai taken "kalaman Kukah kan Buhari rashin adalci ne," The Punch ta ruwaito.

Shehu ya ce tunda dai Kukah ya ce shi malami ne, bai kamata ya dauki bangaranci wajen yin adalci da fadar gaskiya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164