Mai Neman Sanatan APC a Kebbi Ya Yi Watsi da Sulhu, Zai Fafata da Tsohon Gwamna

Mai Neman Sanatan APC a Kebbi Ya Yi Watsi da Sulhu, Zai Fafata da Tsohon Gwamna

  • Kabiru Sani Giant da ke neman takarar kujerar sanata karkashin inuwar jam'iyyar APC ya yi watsi da batun yin sulhu wajen fitar da dan takara
  • Tsohon mai taimakawa gwamnan Kebbi, ya bayyana cewa ba zai janyewa Sanata Adamu Aliero a neman takarar kujerar Kebbi ta Tsakiya
  • Kabiru Sani Giant ya bayyana cewa shirye yake domin a gudanar da zaben fidda gwani wanda zai samar da dan takarar da ya dace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kebbi - Wani mai neman takarar kujerar sanatan Kebbi ta Tsakiya karkashin inuwar APC, Kabiru Sani Giant, ya bayyana matsayarsa kan janyewa daga takara.

Kabiru Sani Giant ya ayyana cewa ba zai janye daga takarar ba domin ba wa sanata mai ci, Adamu Aliero, wuri gabanin zaɓen fidda gwani na APC.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Kwankwaso ya musanta fitowa takarar shugaban kasa a inuwar ADC

Kabiru Sani Giant zai fafata da Adamu Aliero
Sanata Adamu Aliero da Kabiru Sani Giant Hoto: Abdulrauf Shehu, Yanusa Saidu Aliero
Source: Facebook

Tashar Channels tv ta kawo rahoton cewa Kabiru Sani Giant ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai.

Kabiru Sani Giant zai fafata da Adamu Aliero

Ya zanta da manema labaran ne bayan miƙa fom ɗinsa na na-gani ina so da na tsayawa takara don zaɓen fidda gwani da aka tsara gudanarwa ranar 18 ga watan Mayu, 2026.

Kabiru Sani Giant ya yi watsi da duk wani yunkuri na tsarin maslaha, inda ya dage kan cewa lallai sai an fafata a fili, sannan ya ƙalubalanci sanata mai ci da su haɗu a wurin zaɓe.

“Maganar ita ce me suka yi wa mutane. Idan suna da abin nuna wa, su gabatar wa mutane mana. Mutane ne za su yanke shawara."

- Kabiru Sani Giant

Giant ya ce ana son canji

Kabiru Sani Giant ya jaddada cewa masu zaɓe a yankin Kebbi ta Tsakiya a shirye suke don samun canji, inda ya ƙara da cewa ya jajirce wajen shiga tsarin zaɓen fidda gwani na gaskiya.

Kara karanta wannan

Fahad Dankabo: Matashi zai kara da ɗan majalisa mai ci a Kano, ya kai takarda APC

“Muna nan a shirye. Ba mu son maslaha. Ta hanyar zaɓen fidda gwani na kato bayan kato, mutane ne za su zaɓi wanda suke so. Na shirya fuskantar kowane ƙalubale."

- Kabiru Sani Giant

Haka kuma ya yi tambaya kan dalilin ɗaukar zaɓin maslaha, inda ya jaddada cewa magoya bayansa suna sa ran zai ci gaba da kasancewa a takarar domin barin wakilai ko masu zaɓe su yanke shawara ta ƙarshe.

Kabiru Sani Giant na son yin takara a zaben 2026
Kabiru Sani Giant tare da fom dinsa na neman takarar sanata a karkashin APC Hoto: Abdulrauf Shehu
Source: Facebook

Giant, wanda tsohon mashawarci ne na musamman kan fannin Lantarki ga Gwamna Nasir Idris, ana tunanin cewa yana samun goyon bayan ƙungiyoyin da ke adawa da Sanata Adamu Aliero.

Ana ganin cewa kuma suke tare da Ministan kasafi da tsare-tsaren tattalin arziƙi, Atiku Bagudu, wanda suke da daɗaɗɗiyar adawar siyasa da Sanata Adamu Aliero.

Wannan ci gaba na zuwa ne a daidai lokacin da harkokin siyasa ke ƙaruwa gabanin babban zaɓen 2027, yayin da jam’iyyu ke tsananta shirye-shiryen zaɓen fidda gwaninsu.

APC ta fitar da dan takara a Oyo

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugabannin jam'iyyar APC a jihar Oyo sun tsayar da dan takarar gwamna domin zaben 2027.

Kara karanta wannan

Sanata ya yi wa gwamna kara, zai ajiye kujerarsa a majalisa domin ba shi wuri

Shugabannin na jam’iyyar APC a Oyo sun amince da Sanata Sharafadeen Alli a matsayin ɗan takarar gwamna a zaɓen 2027.

An tabbatar da haka ne a wani babban taron da aka gudanar a Ibadan, inda jiga-jigan jam’iyyar daga sassa daban-daban na jihar suka hallara domin tattauna dabarun zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng